A gajiye A'isha take juya steering wheel din motarta, ta gaji sosae saboda tun safe ta fita zuwa office gashi yanzu har biyar na yamma, sosae take jinta exhausted saboda yadda ta wuni tana aiki a office ga meeting har biyu da tayi attending da kyar ta samu ta kurbi lemo shima ba da yawa. A hankali ta shawo kwanar layin gidansu, babu abinda take bukata Irin tayi wanka ta ci abinci ta kwanta Tunda ba sallah zatayi ba, thanks to Allah Muhammad ba a dakinta yake ba yana gurin Rufaida da yanxu zai zo ya isheta, murmushi ta saki tuna yadda tayi Kwana bakwai ba tareda shi ba, Wanda ya zame mata tamkar shekaru bakwai kullum tazo bacci se tayi kuka har tadan Fara sabawa. Ranar da ya dawo dakinta Kai abin ba'a magana sun tabbatar wa junansu farin cikinsu yana tare dasu ne.A bakin gate tayi honk inda gateman dinsu ya leko don tabbatar da hajiyance, wangale mata gate din yayi itama bbu wani wasa ta danna motar ciki, seda suka gaisa kafin ta karasa parking space tayi parking gefen na Muhammad wanda ya tabbatar mata ya dawo kenan, ta dan jima ciki tana wasu abubuwan kafin ta bude murfin motar ta fito hannunta rikeda handbag da Leda se jakar system dinta, a gajiye take tafiya har ta tura kofar parlour wanda babu kowa ciki se kamshi da sanyi da ya gauraye ko ina, inhaling iskar tayi sannan ta zura kafafunta bakinta dauke da sallama, har ta kai tsakiyan parlourn taji fitowar Muhammad daga part din Rufaida, kamar an hankado shi haka ya fito Sanye da Ash jallabiya wadda Bata Kai idanun sawunshi ba, ganin A'isha yasa shi yin turus, itama kallonshi take tare da mamakin wannan yanayin da yake ciki,
Menene na ganka a haka?
A'isha ta fada tana sake karantar mood ensa, kansa ya girgixa yace
Kin dawo, ya office?
Langwabar da Kai tayi tace
Tiring Wallahi, ina Rufaida take
Gabanshi yaji ya fadi saboda abinda yake gudu kenan, muryarshi na stammering yace
Ba....bacci take
Kawai se taji bata yadda ba saboda idonsa na karyata bakinsa,
Ko bata da lapiya ne, bacci at this hour
Ta fada Tana kallon wrist watch dinta dake daure hannunta shida saura
Eh
Kawai ya fada, ai kuwa A'isha ta aje kayan hannunta tace
Subhannalllah, lemme see her
Haka ya bi bayanta kamar munafuki, gabanshi faduwa kawai yake, dakinta straight A'isha ta bude, cikin sa'a tana kwance kan gadon da ya hargitse kamar Wanda akai wrestling akai, bedsheet din ya tattare yayi exposing bare katifar yayinda Rufaida ke takure a gefe, da sauri A'isha ta karasa kanta tana fadin
Rufaida me ya sameki
Itakam Rufaida na jin muryar A'isha ta bude idonta da sukai ja, ga fuskarta tayi ja alamar tayi kuka, Dakyar ta zauna ta riko hannun A'isha ta saki kuka, jini A'isha ta hango saman bedsheet din wanda ya bata clue din Abinda ya faru, ko second bai cika ba taji wani abu ya tokare mata kirji, zuciyarta zafi ta shiga Yi a hankali ta zame hannunta Daga na Rufaida ta nufi Bandaki bakinta dauke da hasbunnallahu wa ni'imal wakil a hankali taji saukin abin haka ta hada mata ruwa me zafi sannan ta fito ta dubi inda Muhammad Ke tsaye yayi shiru tace
Ka sakata tayi wanka, ni xanje na dora abinci
Ba ta jira amsarshi ba ta juya da niyyar tafiya amma taji Rufaida da dusashiyar muryarta tana fadin
Nidai Anty Karki barni dashi, ki jira nayi wankan bana sonshi
A'isha samin kanta tayi da jin haushin Rufaida saboda tace bata son Muhammad, dawowa tayi tace
Karna kara jin kin fadi haka, mijinki ne so dole ki soshi, kinga ni na gaji wanka zanyi yau banci abinci ba ina gamawa zan dawo
Murmushin karfin Hali ta sakar mata itama ta Mayar mata tana jin son A'isha cikin zuciyarta, ficewa tayi ta kwashe kayan da ta aje a parlor ta haura sama jikinta a sanyaye, kayanta ta cire ta fada bayi ta saki shower tana zuba jikinta kawai taji ta saki kuka, seda tayi ya isheta sannnan tayi wankan ta fito, shiryawa tayi cikin pencil skirt maroon tasa milk top da hula ta shiga kitchen bakinta bai daena ambaton Allah ba, ita kanta tasan tana da tsananin kishi akan komai Balle kuma Muhammad subhannalllah abin ba'a cewa komai, ita kanta yau taga kokarinta amna ya zatayi haka ne fate dinta.
YOU ARE READING
GIDAJEN MU
General FictionGIDAJEN MU novel ne dazai yi duba akan problems din da muke fuskanta a gidajen mu cikin society dinmu, akan aure, cuttutuka and zamantakewar mu ta yau da kullum. Shatuuu♥️