🎶Baby, who can tell when two hearts belong so well? May be d walls will tumble and sun may refuse to shine. When I say I love you, baby you gotta know that's for all time 💖♥️♥️💖Bilal na Zaune cikin mota yana kallon gate din wani gida da dukkan alamu wani abu yake jira, yana nan cikin motar yana duba wayarshi yaji an bude motar, cikin sauri ya dago kansa take kuma ya saki murmushi tareda mikawa Yusuf hannu Wanda Ke murmushin ganin abokin nashi,
Yau de ka cika alkawari kazo
Yusuf ya fada suna musabaha
Wallahi kua, naji dadin ganinka its been long
Bilal ya fada shima Yana kallon abokin nasa
Mu shiga daga ciki kaida ka kwaso hanya,
Fitowa sukayi Bayan ya rufe motar tareda daukar wayarsa yabi bayan yusuf, bakin gate ne a gidan budewa yusuf yayi suka shiga, tsakar gidan babu laifi yana da girma Don motoci biyu zasu iya parking, Tun anan Bilal ya fara raina kansa Don kuwa neat gurin yake tamkar ka yasar da abinci kaci ne, kofar da zata shigar da kai parlour gidan yusuf ya tura bakinsa dauke da sallama, Mashaaa Allah shi ne furucin Bilal, ba tsaftar gurin ce kadai ta birgeshi ba, a'a wasu dogayen zara zaran yatsu Bilal ya hango rike da portable handryer tana tana drying wani gashi baki, dogo mai yawa Don ya rufe fuskar meshi a Zaune cikin parlour ta Mike kafafuwanta wanda suma yatsun kafar dogaye ne ga kafar ma me kyau, runtse idonshi Bilal yayi Don yadda wani haske daya taho Daga gurin wannan halittar yayi piercing zuciyarshi, Baki daya yaji jikinsa yayi masa nauyi ko kafarsa kasa dagawa yayi, meye ne Ke shirin faruwa dashi haka?
Yakake tsaye Bilal, shigo mana
Yusuf ya fada ganin yadda abokinshi ya tsaya still to the ground , firgigit Bilal yayi Yana warning zuciyarsa me yasa yake kallon ta what if she happens to be matar yusuf, da sauri yayi auzhiyya yabi bayan yusuf wanda ya tsare shi da ido yana smirking, abin mamaki har lokancin wannan halittar bata dago ba Balle ta bar gurin, seda suka zauna cikin sofa dake cikin parlour yusuf ya dubeta yace
Jidda
Se lokacin ta dago idonta ashe earpiece ne makale a kunnenta, baka ce idan nace baki I mean Baki wanda yake shining Irin na asalin barebarin maiduguri, Dara daran ido gareta farare tas se iris dinta ne deep chocolate ga wasu dogayen lashes da kuma cikakkiyar brows wadda ta yalwatu da gashi, bakinta me Dan kauri ne haka pointed nose dinta Wanda ya kayata fuskarta, gaba daya Bilal yayi observing hakan cikin nanosecond wanda ya haifar masa faduwar gaba tare da runtse idonshi
Na'am yaya, Yaushe ka dawo?
Haka daddadar muryarta ta daki kunnensu take ta sake rikitar da Bilal har baisan ya ware idonshi ba
Yanxu, kirawo Rahama
To yaya
Ta fada Tana mikewa, Tana tattare gashinta cikin wani karamin band wanda a take ya tsinke hakan yasa ta dan ja tsaki tare da barin parlour, tareda samun rakiyar idanun Bilal wanda yasan babu tantama so ne Irin at first sight kuwa,
Ko Nayi maka hanya ne, naga kamar ka yaba
Yusuf ya katse tunanin Bilal Don Tunda suka shigo yake lura da abokin nasa, da sauri ya zabura yace
Wacece ita?
Kanwar Rahama Matata
Ya bashi amsa a takaice, har Bilal zaiyi magana se gasu sun dawo tare Wannan karan kanta a cikin hula yake, se lokacin ya lura da shigar dake jikinta silk gown ce wadda tasa curves dinta da shape dinta suka fito, wani kishi yaji kamar ya mayar da ita Tasa hijab saboda yusuf dake kallonta, a bangaren Jidda itama lokacin ta lura da Bilal, cikin seconds taji ya burgeta saboda she sees everything she needs in him. To fa!
YOU ARE READING
GIDAJEN MU
General FictionGIDAJEN MU novel ne dazai yi duba akan problems din da muke fuskanta a gidajen mu cikin society dinmu, akan aure, cuttutuka and zamantakewar mu ta yau da kullum. Shatuuu♥️