MSF JAHUNLuba na hango kwance saman gado da dukkan alamu bacci take, kusa da ita na matsa sosae baccinta take hankali kwance ta dan cika ta fuska tayi haske kadan daga gani ta rage damuwar dake cikin zuciyarta.
Watanni uku da suka gabata anyi aiki kuma it was successful and perfect Dama idan akai repairing wata shida mutum yake da robar fitsari a jikinshi, suna fitowa daga operation theatre aka saka mata catheter din, Tunda suka zo sani ko hansai babu wanda ya leko inda suke, dukda sani Rabin hankalinsa Yana gun ita Lubabatu din amma ya kasa Zuwa ya ganta. Gaba daya ma sunyi tunanin kwanaki zatayi amma ganin har watanni biyu sun shude yasa Baba hansai ta tursasa shi akan yayi aure kuma itama yarinyar da kadan ta dara Luba badan yaso ba haka ya amince.
Sani na Zaune bakin kofar dakinshi, yayinda Baba hansai itama tana nata kofar dakin suna lissafin kudin kayan lefe, a hankali yace
Baba wani hanzari ba gudu ba, a wanne dakin Za'a saka amaryar
Da mamaki ta dubeshi tace
Nan inda kake Zaune mana, ko ni zan fita ka sakata anan
Da sauri ya girgixa kanshi yace
Ba haka nake nufi ba, amma kayan ita Luba din fa?
Kafin Baba ta bada ansa sukaji sallamar wani karamin yaro wanda shekarunsa basufi 10 ba, babu ko gaisuwa yace
Ana kiran sani a waje
Kace Yana zuwa
Baba hansai ta bashi amsa tareda maida hankalinta Kan sani wanda ya riga ya Mike Daga dokin kofar,
Baba Bari na leka, bazan dade ba
To Tohm shikenan se ka dawo ma karashe maganar
Daga haka ya fice Zuwa kofar gidan, wani matashin saurayi ne tsaye a kofar gidan Wanda kana kallonsa Kaga Dan gayu wanda Boko ta samu zama ga kuma addini a tattare dashi , baza'a kirashi kyakyawa ba haka kuma bashida muni on scale of 10 zai iya zama 5.7 Amma gayunshi ne abin burgewa da yake sake fito dashi har yake burge mutane. Cikeda mamaki sani yake kallon Ja'afar Wanda Ke ta faman murmushi, Ja'afar Dan councillor din yan dutse ne, ya samu bayan gama primary da secondary inda tare sukai da shi sani din kuma kasancewar shi shi daya ne namiji a gurin Alhaji usman hakan yasa ya kaishi China Don yin medicine, yanzu haka ya gama har ya dawo inda zai fara internship dinsa a general din Ringim.
Bayan sun gama gaisawa suka samu wani Dan tudu daga gefen gidan suka zauna suna hirar Yaushe gamo , ana haka Ja'afar yace
Ni kuwa abokina ina matarka Amma yanzu ta haihu ko?
Take yanayin sani ya fara canjawa Don har lokancin yana son Luba kawai bazai iya zama da ita ba
Dan ya mutu dayake ta jima tana nakuda ba'a kaita Asibiti ba
Cikin jin tausayi da jimami Ja'afar yace
Allah sarki, Allah ya jikanshi yasa me ceton kune ita kuma ya bata wani
Amin
Sani ya fada batareda ya fahimci adduar ba,
Mu shiga ciki na dubata na kuma gaida Baba
Bata nan Luba Sede Baba
Cikin rashin fahimta yace
Ina taje?
Sani yasan halin Ja'afar mutum ne me tambaya da bin diddigi hakan yasa yake da kokari, cikin nitsuwa ya warware masa komai tareda fadin
Mutane da yawa sunce extra Marital affairs ne Ke kawo hakan, yanxu watanta uku da sati biyu a gidansu
YOU ARE READING
GIDAJEN MU
General FictionGIDAJEN MU novel ne dazai yi duba akan problems din da muke fuskanta a gidajen mu cikin society dinmu, akan aure, cuttutuka and zamantakewar mu ta yau da kullum. Shatuuu♥️