Ranar ta kasance juma'a, Wanda ya marking Kwana biyu da Faruwar matsalar da luba Ke ciki, har yau bayan ita babu Wanda ya sani sede jiya da yamma Bayan Baba hansai ta dawo Daga yawon da ta saba wanda ya zama kamar mandatory se tayi shi duk safiya da kuma yammaci hakan ya zame mata tamkar ibada Don idan Batayi ba Bata jin dadi, ita ba miji gareta ba Don shekaru biyu da suka wuce ya rasu, Sani shi ne autanta cikin 'yaya wajen sha uku.Luba na tsaye a tsakar gida Tana kwasar zannuwan da ta bata gudun kada Baba hansai tazo ta riske ta Don an kusa kiran maghrib kuma lokacin dawowarta yayi, saboda jiya masifa ta dinga mata tana neman ba'asi akan dalilin da yasa take wanki kullum, bawai wankin ne damuwar Baba ba a'a ruwa da kuma sabulu shi ne matsalarta.
Bayan sallar isha'i, Baba hansai na kofar dakinta inda luba ta shimfida mata tabarma, ita kuma luba na dakinta gashi Tunda akai maghrib jikinta ya jike jagab babu halin ta fito, Tana nan tana sakawa da kuncewa taji kiran Baba hansai, da sauri ta Mike ta fara neman zani Don cire na jikinta,
Bakya jin ina kiranki ko? Bazaki fito ba
Gaba daya ta duburburce hakan yasa ta fito ba tareda ta canza zanin jikinta ba, tsugunnawa tayi gaban Baba wadda ta dago da sauri jin wani mugun zarni ya daki hancinta,
Meye yake zarni haka?
Baba ta fada tana toshe hancinta, wani Irin faduwar gaba ce ta ziyarci luba, har ba tasan lokacinda taja baya ba,
Ikon Allah, tashi ki bani abinci kinzo kin sani a gaba kamar me neman gafara
Baba ta fada Don ko da wasa bata taba kawowa luba wannan uban zarnin zai fita daga jikinta ba, amma se me Tana mikewa Baba taji wani gum! ga abu yana fitowa daga jikinta yana disa akan dandanin kasa saboda hasken farin wata kasancewar watan ya kai goma Sha biyar. Take Baba hansai ta Mike Tana fadin
Menene nake gani kamar fitsari daga jikinki? Menene ni hansai nake gani yau
Hannunta ta saka a bakinta saboda kukan da yake son kufce mata, abinda take gudun kada wani ya sani se gashi ya faru a gaban wadda ko sau daya bata taba son ta san wannan halin.
Dan ubanki ba zakiyi magana ba, Meye wannan a jikinki?
Zuwa lokacin Baba ta hasala, yayinda luba ta fashe da wani Irin kuka Wanda ya sake hasala Baba, cikin daga murya Tace
Matsa ki bani guri, da girmanki Luba kike fitsari a jiki banda zarni babu Abinda kike?
Haka Baba hansai ta dinga fada har ya jawo hankulan makwabta, su wajen hudu suka shigo suna fadin
Hansai me yake faruwa ne?
Daya daga ciki ta tambaya, ko kafin Baba hansai ta bada answer se kuwa dayar ta amshe
Menene ke da yar taki, hayaniya har wajen labaran me shayi
Baba Hansai Tace
Yarinyar nan ku dubi jikinta, Ku gani wai kamar 'yar nan ace fitsari take
Daya daga cikinsu ta riko Lubabatu wadda take ta kuka kamar ranta zai fita, gaba daya ji take kamar ta dinga ihu saboda yadda Baba ta tara mata jama'a, ta shiga juya ta tana fadin
Hansai yana ji jikinta jagab da ruwa?
Baba hansai tayi caraf tace
Abinda nake fada muku kenan
Ikon Allah, kada dai kuce min wannan zarnin daga jikinta yake fitowa?
Kina tantama ne? Ki kalla mana jikinta a jike yake
Laaaa! ku kalla fitsarin dada zubowa yake daga jikinta
Baki dayansu suka saki salati wanda ya sake jawo hankulan wasu makwabtan tare da sake tunzura Lubabatu take wani kukan kamar ranta zai fita. A kalla mata kusan goma ne Ke Kan Lubabatu, kowa na fadar albarkacin bakinsa ,
YOU ARE READING
GIDAJEN MU
General FictionGIDAJEN MU novel ne dazai yi duba akan problems din da muke fuskanta a gidajen mu cikin society dinmu, akan aure, cuttutuka and zamantakewar mu ta yau da kullum. Shatuuu♥️