BAYAN WATANNI UKUFatima na Zaune cikin sabon parlonta da yasha gyara, yayi matukar kyau dayake shekaranjiya ta tare a sabon gidan, Tasha kwaliyya cikin dankareriyar shadda ja da akayi mata aiki da zare Baki da fari yayi kyau aikin da yake ta kashe kudi, dukda kwaliyyar da tayi hakan bai hana ramar da kuma tsananin tashin hnklin da take ciki fitowa ba, Bilal dai ya zama angon Jidda duk wani bala'i na Fatima bai hana komai ba se ma kaimi da ya kara, tayi kukan tayi balain amma a banza, tsaf ya gama ganinsa me flat duplex guda biyu ko wanne bedrooms uku ne a ciki, parlour biyu da toilet kowanne daki kitchen da dining, Amma Fatima nada extra daya nasu Jawad. kowacce ita ta zabi colors din da xaayi mata amfani dashi.
A maiduguri anyi biki na gani na fada, kasan barebari da al'ada da karamma baki anyi shagali jiya aka daura auren Bilal Misalin karfe Tara na safe akan sadaki na sisin gwal ana gamawa aka dakko Amarya Jidda Zuwa katsina Se kuka take ita ta fasa auren a gurin iyah zata gama Rayuwarta. Da haka suka taho katsina Se dare suka isa Faskari yau kuma Bayan axahar suka taho, yanzu haka sun kusa.
Babu laifi 'yan uwan Fatima sunzo da yawa, dayake basu San rayuwar da take ba yasa kawai suka dukufa kawo mata kayan harka a cewarsu zamfara ma ba baya ba wajen wannan harkar. Wasu a ciki su zugata wasu kuma su Bata shawara akan ta zauna lapiya amma itakam ko sau daya bata taba sawa zuciyar ta zasui zaman lapiya ba. Tana cikin wannan tunanin aka sanar da zuwan Amarya, take gidan ya cika da guda, side din Fatima suka nufo wanda kafin su iso kamshinsu ya gama isowa, yan uwanta suka tare su suna raha tareda danne Abinda Ke zuciyar su, haka aka bada amanarta akai musu fada da nasiha sannan aka maida Jidda part dinta yayinda Tee tayi shiru ta zubawa inda bata sani ba ido tana tunanin Wanda ta kasa tantance akan me, kawai se ji sukai ta saki kuka me tsanani, a take babbar yayarta Aina'u ta Fara fadin
Kukan me zakiyi? Salon ayi mana dariya duk dauriyar da kikayi da se yanxu to Kiyi kuka kowa ya gani
Ta gama fada cikin accent dinsu na Gusau, dayar sister dinta ce ta jata Zuwa bedroom tana ta lallashinta har aka samu tayi shiru.
Bayan sallar isha'i gidan tsit babu kowa duka sun juya wajen karfe biyar, ya rage Jidda ita kadai cikin part dinta se Tee itada yaranta, Ta zabga tagumi Kamar wanda aka aikowa mutuwa. Part dinta Bilal ya fara shigowa haka kurum yake jin tausayinta, yasan kishiya ko kusa ko alama batada dadi, zama yayi gefenta tareda kamo hannunta wanda hakan yasa tayi firgigit ta kalleshi don bata san ya shigo ba, kuka ta saki wanda yake neman karya mishi zuciya, bayanta ya buga tareda hura mata iska cikin kunne yana fadin
It's ok dear, komai ya wuce Allah ya baku zaman lapiya
Wani Irin faduwar gaba taji Jin wai baku zaman lapiya sun zama su biyu kenan, tureshi tayi ta shige dakinta, Dan murmushi yayi ya aje abun hannunshi sannan ya fice Zuwa inda Tun dazu yake zumudin zuwa.
Kan royal bed take, makeke queen size me kyau, Tana cikin lafaya me kyau kalar brown me golden glitters a jiki, babu Abinda yake tashi banda kamshi wanda idan me asthma ya shiga babu abinda zai hana ya samu attack, gefenta ya zauna tareda yaye lullubin dake kanta, fuskarta ta dago wadda tayi fresh se kyalli take saboda yadda taji gyara, murmushi suka sakar ma junansu ba tareda sun samu damar fadin wani abu ba, se can Bilal ya sake matsowa ya rungumeta, itama hannunta tasa ta zagaye bayanshi hawaye nayi mata zirya, jin dumi a bayansa yasa ya dago ta, gaban shi ya fadi saboda bai taba tunanin hakn ba, yace
Jidda farin ciki ya kamata Kiyi Allah ya cika mana burinmu, ba kuka ba
Hannunta tasa ta goge hawayen se kuma murmushi wanda idan ta tuna ta auri Bilal se taji she's safe batada damuwa. Seda sukaci abinci sannan sukai sallah yayi touring dinta cikin gidan taga ko ina part dinta, komai yayi kyau kamar mafarki haka take ganin abin. Seda suka yi kallo sannan suka wuce daki inda bacci me dadi ya dauke su dama bayada niyyar yi mata komai ba saboda yasan ta gaji kuma shi yazo ya kara mata wata gajiyar inda so akwai tausayi. Fatima kuwa yadda taga rana haka taga dare, tayi kukan kawai se tana jin kamar ihun Jidda wanda yake sake tunzura zuciyar ta.
YOU ARE READING
GIDAJEN MU
General FictionGIDAJEN MU novel ne dazai yi duba akan problems din da muke fuskanta a gidajen mu cikin society dinmu, akan aure, cuttutuka and zamantakewar mu ta yau da kullum. Shatuuu♥️