03

2K 201 2
                                    

Cikin Asibiti na Ringim dake cikin jihar jigawa su me gari suka Kai Lubabatu, a kofar maternity suka tsaya yayinda Matar me gari ta nemi taemakon wasu mata su biyu dake zaune kofar maternity din da alama yan uwa suke dashi, taimaka mata sukai aka shiga da Lubabatu ciki wadda gaba daya a sume take, me duty din dake aikin yamma ta nuna musu gadon da zasu daura ta, a Kai suka daura ta, nan tazo itada yar uwarta don duba ta amma se me zasu gani? Lubabatu a sume, ko takan matar me gari basu bi ba suka Fara bata taemakon gaggawa yayinda dayar sister ta kira likita, cikin sa'a ya shigo reviewing patients din da akayi musu CS, tare suka karaso yana fadin

Tana eclampsia ne (jijjiga)?

Kai sister mami ta girgixa tace

Kamar obstructed labour ne naji wadda ta kawo ta tana cewa tun jiya take labour

Ta karasa fada lokacinda suka isa Kan Lubabatu, sister mero ta juyo duk tayi gumi tace

Doctor Ku tafi emergency CS saboda baby din is macerated (ya mutu a ciki)

Girgixa kansa yayi yace

Tunda ya mutu bari ayi forcep delivery, ki karbar mana data a gurin relatives din

Sister mami ta nufi gurin matar me gari yayinda sister mero ta tattaro kayan da zaayi amfani dasu, Tana karasawa suka Fara aiki itada Dr bashir cikin kwarewa.

Kunsan matsalar da zaku ja mata Kwana uku tana nakuda ko baku taba haehuwa ba karshe kenan

Sister mami ta fada lokacin da Matar me gari ta gama bata account din Abinda ta sani, ran mami ya baci sosae wannan rashin imani ne , matar me gari da duk ta tsorata da masifar sister mami tace

Yar nan wallahi uwar mijinta ta hana mu namu temako ne kawai

Tsaki sister mami tayi tace

Yarinya karama an barta a wahala ai gashi yaran ya mutu a ciki Allah yasa kar ta samu matsala, ina shi wawan mijin nata?

Hannu matar me gari ta tafa Tace

Yaje aikinsa can kudancin kasa

Drips ta rubuta da abubuwan da bazaa rasa ba ta bata akan a siyo a pharmacy ko kuma kofar Asibiti.

Acan yan dutse, su me gari na tafiya ko minti biyar baayi ba sani ya karaso, ganin mahaifiyarsa na ta masifa yasa shi saurin karasawa gurin ga mutane sun taru, Tana ganinshi tace

Maza shiga ciki Ka aje kayanka kazo muje Ringim

Tsayawa yayi confused ganin duka kowa kallonshi yake ga kuma furucin Baba ,hakan yasa yace

Lapiya Baba?

Tala unguzoma ce wannan karan tace

Kaji Daga baya

Babu musu ya wuce ciki, Yana wulla ido Don ganin matarsa Amma se me? Dakinta kacakaca ga wani zafi da hayaki da ya buge shi, tsayawa yayi Yana nazarin gurin se jin muryar Baba yayi Tana fadin

Sani me kakeyi har yanxu baka fito ba

Da sauri ya aje kayan ya fito suka nufi Tasha ana tayi musu Allah ya kiyaye, Koda suka shiga mota Baba ba tace dashi Kala ba shima bai tambayeta ba Don yaga kamar she's nervous. Da yake tsakanin Ringim da yan dutse ba wani taxara sosae Yasa suka iso cikin stipulated time, babu bata Lokaci suka nufi maternity se lokacin sani ya fahimci Abinda Ke faruwa, amma tambayarshi anan waye ya kawo luba Asibiti?

Kece uwar mijin da kika Hana a kawo ta Asibiti?

Sister mero ta tambaya, Cikeda fargaba Baba tace

Yar nan nice ina fatan yata lapiya take?

Sister mami dake rubutu cikin file din luba ta dago tace

GIDAJEN MU Donde viven las historias. Descúbrelo ahora