Alhaji Ibrahim haifaffen garin kwalam ne cikin jahar jigawa, matarshi hajiya Nafisa itama yar cikin kwalam dince cousins suke kuma cikin family din sarki shu'aibu. Tun a lokacin an tsaya musu sunyi karatu sosae, a Kano ya samu aiki hakan yasa daya auri hajiya nafi suka tafi Kano.Zainab kanwar hajiya Nafisa ce a gurinta take saboda rasuwar mahaifiyarsu, Tana gama secondary kanin Alhaji Ibrahim Alkasim ya aureta, Seda tayi shekara biyu sannan ta haifi yarta Latifa , bayan ta yaye ta ta kaita gidan yaya Nafi anan ta girma tare dasu Nasir wanda yake da na uku ga hajiya Nafi. Wani dare da ya zamewa family din sarki shu'aibu Daren bakin ciki, Zainab da Alkasim suna kwance yan fashi suka hauro gidan suka kwashe duk Abinda idonsu yakai inde na kudi ne sannan suka kashesu! Innalillahi wa Inna ilahil rajiun, Latifa nada shekaru goma lokacin ta gama primary dinta. Tayi kuka dukda a lokacin bata san matsayinsu a gurin ta ba, Seda ta Kara girma sanann ta fahimci su waye iyayenta.hakan yasa rikonta ya koma gurin hajiya Nafi.
Haka ta tashi a marainiya babu uwa babu uba babu dan uwa se cousins dinta. Ta Saba da kowa cikin gidan banda yaya Nasir Don shi ba maxauni bane kuma shi kadai ne namiji cikin gidan hakan yasa Alhaji Ibrahim ya jajirce akan se yayi karatu me zurfi. UK yaje yayi Law sannan yayi Law school a Lagos. Daga nan ya fara contract Law.
Seda ya gama sannan Alhaji Ibrahim yace ya fito da mata, a take yace shi Latifa yake so kuma yana son aurenta, ranar murna a gidan baa magana haka aka tambayi Latifa itama tace tana sonshi ta amince. Cikin kwanakin suka shaku sosae, Nasir ya fito mata a romantic person dinsa Sede ko a wannan lokacin Nasir mutum ne very strict, baya wasa sosae Duk Abinda zaiyi to he's serious kuma kusan bashida leisure time ko wanne Lokaci to karatu ne bashida lokacin wasa komai is serious Yana cikin mutanen da a psychiatry masu obsessive compulsive disorder, yana daya daga cikinsu amma Abu daya kowa ya sani Nasir Yana son Latifa sosae Sede shi baya da halin expressing feeling dinsa amma zaka gani a aikace.
2006 December aka daura musu aure, dangi ana ta murna aka kai Latifa gidanta ta zama matar Nasir, watanni uku ta fara samun matsala da har yau ta gaza samun effective remedy na wannan abin. Bata taba fadawa kowa halin da take ciki, Don lokancin tsoron Nasir Din take sosae saboda tsare gidanshi kwatakwata Bata rabarsa Sede idan shi ya neme ta, ita bata san wani hira, fita da miji ba the only romantic time se idan suna kwance tare yakan tambayeta matsalarta shima bata iya sakewa, ana haka 2007 November ta haifi Amal Zainab sunan mahaifiyarta, Tana yayeta ya samo mata admission a BUK inda ta Fara Dietetics, Tana level 3 ta haifi Nafisa Nana, 2012 ta gama degree dinta sannan a 2013 taje kaduna service shima lokacin ya tafi America yin course na shekara daya, yaran aka kaisu karkasara gidan sister dinshi safiyya. Lokaci daya suka kammalla suka dawo gida baki daya har yaran, lokacin ya tuntube ta zancen ko Tana son aiki ta nuna masa bata so hakan yasa ya siya mata mota. A wannan lokacin Latifa ta Kara shekaru ta sake wayewa ga karatu tayi hakan yasa ta Fara initiating hanyoyin janyo hankalin Nasir amma Abu ya gagara kuma har lokancin bata taba fadawa kowa ba, saboda Nasir ya tsare mata duk wani bukata, abinci, sutura, kudin kashewa, mota duk shekara yake canza mata sede idan baida Hali lokacin Tunda yau da gobe tafi karfin wasa, Duk Bayan shekaru biyu suke Zuwa aikin hajji ko umara, cikin yaran Mimi ce kadai ba taje hajji ba amma Amal kusan sau hudu ana zuwa da ita.babu Abinda ta nema ta rasa Wanda Latifa take ganin gwara ta rasasu ta samu full attention din mijinta, amma hakan ya gagara. Late 2016 ta haifi Mimi, a wannan lokacin ta Fara yiwa Nasir complain din halayensa, Amma kullum sede yace bata da godiyar Allah, abinda Ke damun Latifa hatta yaran baya jansu a jiki, Mimi da take shekaru uku bata dosar inda Nasir yake saboda bata saba dashi ba.
Cikin silk material Latifa take dinkin skirt da riga blue da pink wanda yayi mata das a jikinta sannan ya fito da edges and curves dinta, fuskarta Cikeda annuri saboda very hard kaga Latifa bata murmushi, shi kanshi Nasir a yan shekarun nan ne yasan tana fushi Tunda wani sa'in idan ta masa complain akan wani abin yayi banza da ita ko kuma ya Hana yaran kallon Abinda suke so se tayi fushi.
YOU ARE READING
GIDAJEN MU
General FictionGIDAJEN MU novel ne dazai yi duba akan problems din da muke fuskanta a gidajen mu cikin society dinmu, akan aure, cuttutuka and zamantakewar mu ta yau da kullum. Shatuuu♥️