05

1.8K 196 7
                                    

Cikin purple abaya take, wadda Tasha stones tundaga sama har cikinta, dogon hannu ne da abayan me rubber tayi dauri da siririn mayafi kalar white da Polk dots purple a jiki. A'isha tayi kyau karshe Sede fuskarta babu walwala tana kan kujera idonta na kan plasma TV dake aiki wanda idan ka shigo zakayi tunanin kallon take amma a zahiri hankalinta baya gidan baki daya yana gurin mijinta, tun ranar da Umman Engr tazo tayi musu diban albarka shi kenan ya tsiri fita wanda a da ba halinsa bane inde ya shigo gida Daga office to ba karamin Abu bane ke fitar dashi sede idan kuma tare zasu fita ne.

Agogon parlour ta kalla karfe goma Harda yan Mintina, cikin nitsuwa ta Mike ta isa dining ta kwashe abincin da ta jera masa ta nufi inda megadin gidan da iyalansa ke Zaune, sallama tayi, Hamida ta fito Tana fadin

Anty Kece ki shigo mana

Kai A'isha ta girgixa tace

Karbi abincinnan kuci, ki gaida Mamu

Amsa Hamida tayi tana cewa

Allah ya saka da alkhairi, se da safe

Haka ta juya ta koma cikin gida, dakinta ta wuce ta fara rage kayan jikinta Don watsa ruwa gaba daya zuciyarta babu dadi, gashi bata son abinda take tunani yayi tasiri cikin zuciyarta saboda tana jin kamar Muhammad ya tafi zance gurin wata ne, da wannan tunanin tayi wanka ta zura sleeping dress sannan ta dawo parlour Don kashe TVn data bari a kunne, Tana danna switch din Muhammad na shigowa cikin parlour bakinsa dauke da sallama, cikiciki ta amsa don shima saboda sanin muhimmancin sallamar ne amma da bazata ansa ba.

Ko kallonshi Batayi ba ta shige dakinta ta banko kofar, gado ta fada ta runtse idonta bawai Don tana da tabbacin baccin zai zo ba Sede Don ta samu damar yin tunani. Muhammad kuwa kamar munafuki haka ya shiga dakinsa ya rage kayan jikinsa Don ya san tabbas ya taro match har to 11 baya gida ai shima ya sani to amma ya zaiyi, parlour ya dawo Don cin abinci amma dining was empty, hakan yasa ya kwashi kafafunsa Zuwa kitchen Don dubawa amma labarin is same hakan yasa jiki a sanyaye ya tafi dakinta, Tana kwance tayi rub da ciki, hawaye na bin gefen kuncinta. Hannunsa ya Dora kanta yace

Baby am sorry, I didn't mean hakan please

Janye jikinta tayi ta matsa daga inda yake batareda ta ko kalli inda yake ba, matsowa yayi zai dada rikota tasa hannunta ta doke nashi cikin karaji tace

Don't touch me again, Ka koma inda kake zuwa
.dama yasan kwanan zancen hakan yasa ya Mike kawai Don yasan bazata saurare shi ba, kofarta ya jawo mata bayan ya kashe wutar dakin sannan ya nufi nashi

Kuka A'isha ta saki tana jin yadda zuciyarta Ke wani Irin bugu kamar zata balla chest wall dinta ta fito, wayarta ta janyo ta kunna qura'ani kira'ar maher mu'aqilee ta rage volume din tana saurare a haka bacci barawo ya saceta.

A gurin Muhammad abin Yafi gaban misali Dan kuwa he can't remember last time ya bata wa A'isha rai har tayi masa ihu haka, let all say sunyi fada but ya manta lokacinda ya kaisu raba daki Balle shimfida kullum suna tare da juna cikin soyayya da aminci.

Da asuba kusan Lokaci daya suka tashi, massallaci ya wuce ita kuma ta tada sallah a dakinta, Tana idarwa ta nufi kitchen da IPad dinta ta kunna qura'ani Don jin saukin Abinda take ji cikin zuciyarta, idanunta sun Dan tashi saboda kukan da tayi cikin zuciyarta tana jin kamar she shouldn't have shouted at him, amma batada yadda zatayi ta gaji, she's tired of trying saboda bata haihuwa shi ne kowa yake turning bayansa against her..... Rungumeta taji Muhammad yayi wanda ya sata sakin nannauyan ajiyar zuciya

Am sorry Aeesh , Kinsan ina sonki

Goge hawayen fuskarta tayi ta cigaba da juye abinda tayi cikin warmers, a hankali ta cire hannayensa daga waist dinta ta nufi dining shi kuma kawai ya bita da ido, Tana aje kayan ta nufi dakinta Don yin wanka, Tana shiga ta maida kofar ta rufe bayan ta jingina jikinta tare da dafe kanta, Tana jin komai ya fita a kanta itakam she's at the verge of despair, kusan minti biyar tayi tsaye kafin sluggishly ta nufi toilet.

GIDAJEN MU Where stories live. Discover now