Gidan tsit tamkar Bbu kowa ciki, karar fankoki kawai da AC din gidan kawai kake ji. dauke da basket me Cikeda turaren wuta iri dabandaban Latifa ta sakko, incense burner dake jikin wani angle a parlour ta nufa ta zuba kusan Kala hudu sannan tayi switching abin take kuwa ya fara burning abin, nan cikin dakunan kasa ta aje basket din sannan ta dawo ta zauna cikin parlour tare da kurawa screen din plasma TV din data kunna yanxu.
Dayake ranar asabar ce yaran sun tafi islamiyya cikin Ibrahim Kunya har house help dinta Fa'iza, shima tun safe barrister ya fita har yanxu bai dawo ba, ta kirashi Don ko abinci baici ba amma wayar tashi a kashe take, ita babbar damuwarta bata san inda ya tafi ba saboda ce mata yyi yanxu zaeje ya dawo, wayarta ta janyo ta Fara neman layinsa cikin sa'a ta shiga Sede har ta gama ringing Nasir baiyi picking ba, a Karo na biyu ta sake Kira shima dai no answer, mikewa tayi ta kashe TV din sannan ta dakko mayafinta a sama Don Bata jin dadin zaman so take tadan Fita taga unguwa don Kwananta uku ko gate bata leka ba. Incense burner ta kashe tana lumshe idanunta Don kamshin yayi mata yadda take so, wayarta ta dauka ta kulle kofar parlour sannan ta dubi Baba megadi Bayan sun gaisa tace
Baba zan shiga makota, bazan jima ba idan yaran ko kuma babansu ya dawo Dan Allah kayi min flashing
Ta fada Tana daga masa wayarta
To to hajiya, Inshaaa Allah sekin dawo.
Da haka ta fice a gidan, ringing wayarta ya shiga yi wanda ya sata duba screen din my half taga an saka hakan yasa tayi saurin picking muryarta Cikeda damuwa tace
Daddy ina Kaje? Ba kaci abinci ba ina Kake?
Naje office ne, ya akai naga missed calls dinki muna meeting ne
Ya fada ba tareda yayi duba Zuwa tambayoyin da ta jero masa ba
Duk hankalina a tashe yake Inata kiranka wayarka a kashe
Latifa ta fada muryarta da alamun damuwar,
Ki dinga tausayawa zuciyarki, ni karamin yaro ne dazan bata? kinsan dole akwai Abinda nakeyi ko?
Damuwar da na nuna akanka Shiyasa ka fadi haka, shikenan Dama zance dakai zan shiga makwabta
Se kin dawo
Ya fada Yana kawar da Abinda Ke taso masa akanta, batareda ta amsa shi ba ta kashe wayar tana jin kamar tayi ihu, zuciyarta Ke azalzalarta akan ta koma gida amma haka ta danne zuciyarta ta nufi gidan da take shirin Zuwa, gida uku suka rabasu, a bakin gate suka gaisa da maigadin sannan ta shiga ciki Bayan ya tabbatar mata Hamida tana nan, kofar parlour ta kwankwasa Daga nan taji an bude, wata karamar Yarinya ce ta gaisheta wadda bazata wuce Saar Fa'iza ba itama aiki take mata, ciki ta shiga tana fadin
Ina Antynki?
Yarinyar tace
Bari na kirata
Ko kafin ta tafi se gasu sun fito itada Lawan mijinta kenan, kuka take tayi shikuma yayi kicinkicin da rai yana fadin
Ni na gaji da complaints dinki id... ..
Sauran maganar ta tsaya masa ganin Latifa Zaune Kan kujera, Allah ya sani yana ganin girmanta tun ranar da ya Fara zuwa ganin gida shida mamansa suka shiga gurinta sannan da aka kawo Hamida gurinta aka bada amanarta hakan yasa yake tsananin ganin girmanta, shigowa parlour yayi Hamida na bayanshi suka zauna, shi ya fara gaida Latifa wadda ta tsare shi da ido, amsawa tayi sannan ta dubi Hamida wadda ta kasa bude Bakinta saboda kukan da take yi,
Kada kuce min wata biyar dayin aure kun fara samin matsala is it not too early?
Latifa ta fada Cikeda mamaki, kasa yayi da kanshi yace
YOU ARE READING
GIDAJEN MU
General FictionGIDAJEN MU novel ne dazai yi duba akan problems din da muke fuskanta a gidajen mu cikin society dinmu, akan aure, cuttutuka and zamantakewar mu ta yau da kullum. Shatuuu♥️