14

1.3K 160 0
                                    


Sani baice da Baba hansai komai ba, ya karasa shigowa cikin tsakar gidan Yana binsu da kallo, Ashe da gaske ake Baba hansai tana dukan Lubabatu kamar yadda aka sha fada masa,

Baba barka da safiya

Kamar me in ina Baba hansai tace

Lapiya, Yaushe ka dawo?

Yanxu na iso Amma a Kano na kwana

Lale sannu da zuwa

Daga haka ya shige cikin dakin Luba wanda tun asuba ta gyara shi tsaf, Baba ce tayi mata alama da ido akan ta bishi, hakan tayi jiki a sabule ta bishi ciki, yana zaune bakin gado Yana kallon kofa seda ta shigo sannan ya maida dubansa kanta, gani yayi ta rame tayi baki dukda dama can ita ba fara bace, se kuma me Tana zama Kan tabarmar dake kasan dakin Sani yaji wani wari ya ziyarci hancinsa, shi kuma duk duniya idan akwai abinda ya tsana to wari ne, yanzu zai daga masa hankali, mikewa yayi da azamarsa don tambayar Luba daga inda warin yake amma yana bude bakinsa se amai, a guje ya fito ya nufi rariya Don Yi, Luba tsoro, firgici gabaki daya suka lullube ta, haka ta biyo bayanshi kamar munafuka, Baba ma na dakinta taji amansa ta fito tana fadin

To Daga zuwa se amai, Ke Lubabatu bashi ruwa ya kuskure bakinsa

A sanyaye ta debo ruwan ta nufe shi amma Tana zuwa kusa dashi ya fara kela wani sabon aman anan ya tabbatar matarsa ke wannan doyin, hannunsa yasa Yana mata alamar ta bar gurin, Baba ce ta matso tace

Matsa mana, ba dole yayi amai ba wannan Irin wari da kike haka.

Kuka sosae Luba take kamar ta hadiyi zuciyarta, bakin ciki kuwa Don dai kawai ba'a sabo da ire iren emotional disturbances dinnan da se nace tabbas bakin ciki a sati hudun nan sun zama abokanta. Sani gama aman yayi ya wanke bakinsa sannan ya dawo kofar dakin Baba yana maida numfashi, a bakin kofar dakinta itama Luba din ta zauna Tana goge hawayen dake bin kuncinta dukda hakan tamkar sake angiza lacrimal glands dinta suke wajen producing more tears.

Baba Lubabatu ta daina wankana?

Sani ya tambaya Bayan ya gama shanye tsamiya da tagargajin da Baba ta jika masa, haka Baba hansai take son ji hakan yasa tace

To ni Sani me zance? Yanxu ai mutane basu zuwa gidannan

Ta fada Tana tabe bakinta, kuma da gaske take Tun tuni mutane sukai kaura daga Zuwa gidan saboda baki daya gidan wari yake, Tunda ta Fara magana Sani ke kallonta har ta gama, shidai yasan matarsa nada tsafta to amma bai san abinda ya hau kanta ba har take wannan warin kamar mushe

Baba ni ban fahimce kiba, Kiyi min bayani plz

Tayi maka bayani dai da bakinta auta kar tace nayi mata sharri

Cikin kosawa yace

Haba Baba Dan Allah Kiyi min bayani nasan da ita ai na tambayeki

Jin hakan yasa Baba hansai ta Fara fadin

Tunda mukaje garinsu na dakko ta, shi kenan ta Ke fitsari.....

Kamar yaya fitsari Baba?

Sani ya katse ta

Fitsari dai ne yake zuba babu tsayawa duk inda ta wuce a garinnan zancen ake, ba'a Zuwa gida na kullum ciki na a kumbure nake Kwana dashi

Baba hansai ta fada Tana kukan munafurci, shiru Sani yayi kafin can ya dubi Luba dake durkushe dokin kafarta har lokancin kuka take idanunta sunyi jajawur kamar garwashi, gashi duk wrinkles sunyi forming a gefen idonta saboda azabar kuka

Lubabatu

Sani ya kira sunanta a sanyaye, dago idonta tayi ta aje Kan Fuskarshi ba tareda ta amsa ba, shima tausayinta yaji amma gaskiya bazai iya zama da ita ba don yasan zai cutu sosae, kuma yau mamakin sanyin Baba hansai yake ko dan ya kamata tana dukan tane oho

Baba an nemi magani?

Kai Baba ta kada tace

Eh naje gurin da ma'arufa gurin me magani , ta bada wani gari amma yarinyar nan fir taki sha se ma rashin mutunci data dinga yimin.

Sani dai jinta yake zai iya yadda idan ance taki shan magani  tunda shi din shaida ne don kuwa lokacinda tana da ciki idan aka karbo magani bata sha amma ace tayiwa Baba rashin kunya shi ne Abinda bazai taba yarda ba. Gyara zamanshi yayi yace

To Baba me kike gani, me cece mafita

Da murmushi Baba tace

Ina ganin mu maida ta gida suyi mata magani

Runtse idonta Luba tayi, Tana godewa Allah Don abinda take son ayi mata kenan ta koma gida.

Bai Kara cewa komai ba ya mike ya fita a gidan, Baba hansai ta saki guda tare da fadin

Allah na gode maka yau zan rabu da alakakkai, mujiya me bakin jini kije can da wannan warin ki Kai gidanku amma ba anan ba.

Wajen 30 minutes Sega Sani ya dawo, babu kowa tsakar gidan kowacce na dakinta, Baba ce ta Fara fitowa sannan Lubabatu ita seda Sani ya Kira ta sanann ta fito har ta canza kaya Amma suma kayan har sun jike in fact diga ma suke kamar an tsamo daga ruwa.

Zama tayi tana sha re hawayen dake bin kuncinta, Sani nesa dasu ya zauna yace

Za'a maida Luba gida don suyi mata magani tunda anan bazata Sha ba idan an Bata, do....

Waye zai dauketa tana Wannan warin?

Baba hansai ta katse shi

Akwai motar da ta kawo shanu daga can gasakole din, to yanxu zasu juya Don haka na basu kudi su sauke ta a gida

Hakan yayi, Maza jeki dakko kayanki yau dai mun huta da annoba

Kamar ana hankada ta haka taji saboda yadda zuciyarta Ke tafasa, ga wani bugu da take kamar kirjinta zai Balle zuciyarta ta fito waje haka taji, ko minti daya Bata cika ba ta fito da kayanta, lokacin kukanta ma ta daina, zani ta canza sannan ta fito, babu Wanda ta kalla cikinsu ta tsaya kawai

Ina fatan baki bar mana tsimma ko daya wanda zai mana zarni cikin gidannan ba?

Baba ta tambaya, Luba bata ansa taba har Sani yace ta biyo bayanshi, Tana fitowa taji yara sun taru ga motar akori kura nan tsaye bakin kofar, kawai Luba ji tayi hawaye sun sake wanke mata fuska, Sani na kallonta dukda tausayinta da yake ji saboda son da yake mata amma haka ya saka ta cikin motar Bayan ya matsa Don Kada ta taba shi, yara kuwa se ihu suke mata wanda yasa ta kara fashewa da wani kukan tana jin inama ta mutu Tunda can ma gasakole din bata san yadda za a kaya ba. Haka nan driver ya hau ya ja motar suka nufi gasakole. Kuka kawai Luba take kamar zata shide, haka take jin Rayuwarta babu amfani, ita kam babu wani abu tunda ta taso ta tsinta me dadi, quite sure iyayenta na sonta sede ita yar fari ce wanda yasa mahaifiyarta take jin kunyarta, shekarunta shida babarrta ta rasu se Inna matar babanta ta rike ta riko na amana, babanta mutum ne me son karatu haka yasa ta makarantar islamiyya da kuma ta Boko, Luba tana da kokari da hazaka a haka ta gama primary inda kakarta da ta haifi babanta ta uzzura se anyi mata aure, ganin babu miji din Luba bata kula kowa yasa ta sarara musu, a daddafe ta gama Js3 nan aka yi mata auren ba da son ranta ba se dan karfinta da akafi.

Shatuuu ♥️




GIDAJEN MU Where stories live. Discover now