12

1.5K 183 0
                                    







Wai wannan wanne irin zarni ne haka yake tashi kamar gishirin kunshi

Wata matashiyar Yarinya da shekarunta zasu tasar mawa sha shida ta tambaya lokacinda Luba ta karaso rijiyar kanta dauke da bokiti, mata ne sun kusa bakwai yawanci yan mata ne bakin bore hole din, kowacce na jira layinta yazo ta diba Don kaiwa gida, Tun Kwana biu da taje rijiya ta fahimci 'yan gurin sun Fara fahimtar ita ke wannan warin yasa ta daina Zuwa yau ta kudurce tuka-tuka(hand pump ko bore hole) dukda tafiya zuwa bore hole din Yafi Nisa akan zuwa rijiya amma itakam bata son kyamar da mutane Ke nuna mata, dukda har yanxu mutane basu gama fahimtar hakan ba.

Luba na nan tsaye tayi baki ita dama ba wani hasken kirki gareta ba, ga wata rama da ta kara dukda da can ma kafin ta auri Sani ba wani kiba gareta ba, Balle kuma yanxu da take cikin tsaka me wuya, kudaje ne Ke bin zanin jikinta da kuma kafafunta saboda ta sake zani kafin ta fito amma kuma rabonta da wanka Tun jiya da asuba don Baba hansai Tace ta gama bata mata ruwa, idan zatai wanka sede ta debo sabo, to ita bata son fitowa saboda yadda zance ya bazu cikin garin, Duk inda ta wuce toshe hanci ake, hakan ba karamin tayar mata da hankali yake ba, zannuwanta Duk sun baci saboda wanki ma ta hanata yi, dakinta in banda zarni, wari da Kari babu Abinda yake saboda yadda abin ya kara tsamari har tsakar gidan shima ya fara zarnin.

Ganin layi yazo kanta yasa ta matso gurin don fara diba, tana zua daidai wasu yanmata taji daya na fadin

Kaiiiii, Wannan ce Wallahi take uban zarnin nan

Dayar tace

Matsa mana, ba itace matar Sani na hansai ba?

Ita ce mana, matsa a kanmu

Tabbbbb wannan ai se ta kashe mutum

Hawaye sharr haka Luba ta fara buga ruwan se kuma taji zubar fitsarin wanda ya saka 'yan matan da suka rage na gurin fadin

Innalillahi, kunga da tsakar Safiyar nan fitsarin take

Dallah malama, sauri ki buga ki bawa mutane guri haka kurum kinzo kin saka gaba daya zarni yake

Har se ta gama? Ta sakko kawai ai ta gama diba

Haka suka ture ta daga Kan, tana ta kuka sa'a daya ma ruwan kiris ya rage ya cika, Amma da bata san Irin bala'in da Baba zatayi mata ba, haka ta dauki kodadden bokitin wanda Rana ta gama dashi, with little pressure zai iya fashewa, haka ta fara tafiya tana sake share hawayen fuskarta, ita kam ina zata saka ranta taji sanyi, Wacce Irin rayuwa take ciki, haka ta dinga kuka Tana sauri har ta daina juyo muryar ihun da matan Ke mata suna fadin me fitsarin tsaye jaka ce.

Duk wanda ya wuce ta gefenta se taga ya toshe hancinsa tare da fadin Abinda zai soya mata zuciya. Tana wucewa ta gurin wani me shayi wanda kullum Se yayi mata kashedi akan ta canza hanya saboda tana korar masa customer, to nan ce kadai hanyar idan bata wuce ta nan ba babu wata hanyar, tunda ta hangoshi a tsaye taji gabanta na faduwa, bugun zuciyarta ya dadu, tana karasowa gab dashi yasa hannu ya hankada bokitin wanda yana kaiwa kasa ya dare gida biyu, hakan kuwa ba karamin sake tayar mata da hankali yayi ba, ko kafin ta gama kallon bokitin da ruwan tuni ya sheka mata mari Yana fadin

Banace Karki kuma biyowa ta Wannan hanyar ba

Wani saurayi a gurin yace

Dake ta Wallahi Isuhu yarinyar bata jin magana

Dama tuni ta durkushe a gurin Tana kuka hakan yasa Isuhu taka kafarta wadda tasa ta saki Kara tare da sake fashewa dawani kukan, wani dattijo dake gefe yana kurbar tea ne yace

Isuhu kar ka sake dukanta baka ganin Yarinya ce kuma mace ma

Haba Liman baka jin warin da yarinyar nan take kamar Dan bunsuru

GIDAJEN MU Where stories live. Discover now