ISMAT O1.

203 5 0
                                    

🏵🏵❄❄❄🏵🏵 ❄ ISMAT ❄ 🏵 🎍 🏵 ❄❄🏵🏵🏵❄

Written✍

By

*Nusaiba Ibrahim Usman Zango*

Online Hausa Writters (O.H.W)

Baiwa Writter Association (B.W.A)

View

nusaibaiusmanzs.WordPress.com

Bismillahir Rahmanir Rahim.Ya uban giji Allah ina mai rokonka yadda na fara rubuta wannan littafi nawa mai taken ISMAT,Allah kabani ikon gamawa lahiya.

Jinjina ta musamman gareki Khadija Candy 🍬 da Irin goyan baya da kikeban.

ZAINAB Y(Queenna👸)NAFEESAT YUSUF(Feenah baby)ohhhh bazan manta da kuba da irin kwarin guywa da kukebani Allah bar zumunchi Ameen.

Ohpsss kuwu ANAM DORAYI bafa zanmanta da kaiba Godiya ta musamman gareja.

O1.

Iskane mai d'ad'i yake kad'awa ga garin yayi wasai gunin ban sha'awa duk inda ka kalla ciyawa ne kore shar,sunyi lup2 gunin ban sha'awa ga rassan itace sai rausayawa suke,kamar zasu taba kasa kasancewar iskan damuna yahad'u da iskan amma Cen daga nesa na hango wata yarinya tafe kamar ta bab'b'iya.Tafe take Tanata 'barzan Kuka kamar zata shide don kuka 'kafan baya na cimma na gaba,fuskannan yayi caba2 da hawaye da majina tana tafe tana waige2 tana cigaba da Kuka itakanta batasan inda take sa k'afantaba,ballantana tasan inda ta dosa itadai tasan tana tahiya,har ta Shigo gun Mutane. Mutanen dake hada2 agun sai kallonta suke kowa na mata Kallon Mahaukachiya bawanda ya tanka ta, Saidai suka sa mata na mujiya masu imani na tausayinta da sukayi la'akari da karanchin shekarunta don yarinyache karama. Gungun samari ne ke zaune reras abin su, kasanchewar yammachine kowa nata hidin dimunsu,masu Kuma Sana'a nata sana'ar su,gefe mai koko ce keta saida kokonta,gefe daya kuma mai kosai ce taketa suya abinta sai layi ake ana siya,daga gaba Kuma mai awara ce itama sai suya take ana saya,dayan gefen ma mai doya da kwai,kaza da kwai,kwai da kwai yaketa suyan sa ana saya. Wannan gungun samarinne keta musu akan kwallon kafa,masu shan koko da kosai nata siya suna sha,masu siyan awara doya da kwai,kaza da kwai,kwai da kwai na siya,kowa hankalinsa na kan abin da yake gabansa,Amma fa rabin hankalin su na gun samarinnan masu musu kan kwallon k'afa, wa'yancen na cewa sai Basalona wa'yannan na chewa sai Arsenal sunadai ta musun su. Daya daga cikine ya ce Ohhh Duniya ina zaki damu ne don Allah don Annabi jibi wancen yarinyar Mahaukaciya ce ko mai yarinyar ta tsare ma wanda sukamata wannan mugunta yarinya da ita amma take hauka,dayan yace a'a ammafa ba kamar ba Mahaukaciya bace ba, kamar dai atsorache take ko kuma an biyo tane ta firgita shine ta koma haka? Toh likita bokan turai inji 1 daga chikin samarin wanda tunda suka fara magana baice dasu ta tafasa ba ballan tana ta kone toh Kai waya gayamaka hakan,MAZA baka da dama saikache kamanta abinda nake karanta kenan fannin kwakwalwa,ok sai yanzu na tuna Sarkin iya magana Hhhhhhhhhhhhh! Sauran yan dandalin suka kwashe da dariya ba k'akk'autawa saida sukayi mai isar su sannan suka tsagaita,duk wannan maganganun da sukeyi, bayan wucewar yarinyar ne suke yi Wanda baicika maganan achikin sunne yache MAZA is time to pray,don lokachin anfara kiraye2 Sallah magrib yache muwuche Masallachi dukkansu suka tashi atare suka Kama hangar masallachi. *shiko wannan Saurayin suna tafene amma hankalinsa da tunanin sa duk sunagun wannan yarinyar tambayoyi yake ta zabga wa kansa wanda shi kansa bai San amsarba,toh ita Kuma wannan yarinyar daga ina tafito? ina iyayenta suke da yan uwanta?Mahaukaciyache ko mai hankalice?yana kaiwa nan ya sauke goran numfashi wanda yayi sanadiyyar jawo hankalin Abokansa atare suka juyo suna kallonsa, shi Kuma dayaga haka sai ya sake daure fuska yache dasu lahiya dukkansu suka che kai zamu tambaya lahiya Irin wannan goron numfashi da kayi dai2 nan suka karaso masallaci don haka sai suka bar maganan duk suka dauki buta don yin Alwala su gabatar da sallan magrib.

**** **** **** ****

Muje zuwa

_*Star Nucee360*_✨💫

ISMATWhere stories live. Discover now