ISMAT O5.

38 1 0
                                    

❄❄❄🏵🏵 ❄ ISMAT ❄ 🏵 🎍 🏵 ❄❄🏵🏵🏵❄❄

Written ✍

🏼By

Nusaiba i Usman Z.S

O5.

**** **** **** ****

Ita ko tananan tana makyarkyatan sanyi,ga wani irin tsoro da ya saukar mata ga garin da duhu gashi dama ba kowa agun Hakanan baiwar Allah bata da zabi fache ta sami dutsi ta gyara ta zauna ta rakube ta kuma kudundune kanta a chikin guywarta ta kuma ta rakube ajikin bango,gari tachi gaba da rugunniya(chida)da iska ga walkiyan da akeyi ne yake haskota tananan chikin wannan halinne taji kamar takun Mutane sai wani irin tsoro yakuma mammaye mata zuchiya tana chikin haka sai kamar an mintsile ta kawai saita daga Kai ta daga kanta.'Daga kanta keda wuya sai taga kamar ana leken ta,ita ko takafe gun da ido👀sai taga kamar mutum,kamar Kuma ba mutum ba Cen Kuma sai Kaji ana chewa Oga gatanan tana chiki ku Kara so da sauri duk ko sukai saurin isowa gurin su na chemasa toh mushiga chiki duka suka dunguma chikin gurin Dan Duna yache Acid janyota mana aiko Acid ya janyo ta yakawo ta tsakiyar dakin ya jefata ta fadi yarap kakeji sai kache anyarda tsumman da ya Sha ruwa kanta yabugu da dutsi sai da saki Kara don azaba da taji inda ta bugu inda ta bugun ko ta gun kanta ta bugu saman gefen kunnin ta na hagu gun ya kumbura har ya tara jini dan kwalin kanta yafita daga daurin da tayi kamar an kulle nagani a tsumman aikio gashin kanta ya baiyana yayi wani, wani Buf ya dukkan su saida sukaji tsoro sukaja da baya ganin irin yawan gashin kanta saikache wata Aljana. Ebola ya jada baya ya ce Oga Anya ba Aljana muka hadu da ita Oga yache ko Aljana ce sai munga abunda "Ture wa buzu nadi"yache ma Acid dagota Acid jiki na 'bari ya dagota, amma baiga fuskanta ba Dan Duna yache chire gashinnan nata daga kan fuskanta yako yaye gashin sai ga fuskanta ya bayyana Oga ya chiro torchlight karama daga aljihun sa ya haska ta nan ma tsoro ya Kara kamasu yadda sukaga fuskan nata Oga yace da tsawa ke mutum che ko Aljana.Tanajinsu batache komai ba sai bin su da ido👀takeyi bata da bakin basu amsa tambayar su Oga ya Kuma daka mata tsawa amma duk abanza Ebola yache Oga aida ba mutum bane da tuni ta kauche kawai muyi abin da ya kawo mu,mu kauce Kafin ruwannan ya sauko Oga yace baka ganin irin wannan kyau da takeda shi ga idanu kamar na mage naga alama baku ganta da kyau ba ne kuzo kukara gannin ta kugani,dukkan su suka matso har da wanda yake rike da ita dan shima kanshi bai yi arba da kyakkyawar fuskanta ba sai a lokachin da Oga ya haska masu fuskan nata sannan suka ga fuskannata da kyau,alokachinne dukansu suka firgita suka hada baki gurin chewa Oga wannan ba mutum bache murufa wa kanmu asiri mukuma kanmu tunkafin lokachi bai kure mana ba Oga ya bushe da dariya yache ai tunda muka biyota toh sai mun aiwatar da abunda ya kawo mu BABA bansan ka da tsoro haka ba mu tsallake Ma abinda yafi wannan wuya ballan tana wannan yar karamar alhaki(niko nache baisan ko dan hakin da Katsina Shika tsokale maka ido👀ba)Dan Duna yache Oga yarinyar nan fa hankalina bai gama kwanchiya da ita ba wannan kyan nata yayi yawa. Gata fara irin farin nata ma na dabanne wanda bantaba ganin irin Saba ko a kasan turawa ga tsayin fuska gata doguwa ga hanchi kamar pencil ✏ bakinta kamar an zanashi Kuma kamar tasa masa janbaki pink👄ga manyan idanu👁👁 giranta ahade yake ga gazar2 din gashin ido👀BABA abinda yafi bani tsoro akan ta shine idanun👀ta sak na mage.

**** **** **** ****

Ita ko duk maganganun nan da sukeyi tanajin su gawani azababben chiwon kan da kanta keyi saboda azaba har wani duhu take gani duda ko darene ga hasken da ya haska daki amma bata daina ganin duhun ba ga rawar da jikin ta keyi sai rawar jikin ma ya karu,Acid daya taketa dan tsoro da ya kamasu shikam tuni ya sake ta ya koma gefe shima yana Kara,kare mata Kallo da tun dazu baisamu yayi mataba saboda riketan da yayi tananan tsaye taji wani daya daga chikin su wanda suke Kira Oga yache me kuke jira da itane ku kadda mar mata tanajin haka saita fara neman hanyar da tashigo dan ta tsira da mutun chimta, tafara tafiya ahankali yadda baza sujita ba tafara barin gurin tana tafiya har ta kai dab da bakin kofar fita sai ta taka wani abu yayi Kara Ru'kuuu'kuuuu'kuus shiya yajawo hankalin su ga duban kofar saiko suka ganta tana sauri suna ganin haka sai suka dunguma da sauri suka fara binta. Ita Kuma tana ganin haka tafara gudu iya karfinta suma suna ganin haka suka Kara wuta,gudu take iya karfinta duda bata da karfi ajikin ta amma dayake gudun cheton rantane sai Allah ya sako mata wani irin karfi da ita kanta tasan batada shi daga Allah ne, gudu kawai take ita kanta batasan inda take saka kafarta ba saitai rashin sa'a ta fadi,jikake yarab,ashe wani gini ne daya aka yi kos daya aka barshine bata lura dashiba tafadi Kuma ga duhu ba haska ko kadan ga iska da kura datake tahowa sai dai walkiya da akeyi ne shine yake taimaka mata take ganin wani gurin da take sa kafa (Allah sarki baiwar Allah)fadin datayi sai akai rashin sa'a ta kuma fadi saitin inda ya kumbura aiko gurin dama ya tara jini kawai gun yafashe saboda azaba saida ta saki wani gawur tachchen ihu jini nazuba.Ihun da tayi ne yasa masu binta suka 'Kara azama sukayo tagun da sukaji ihun da tayi dama ta bache masu. Tanajin takun gudun su saitakara azama ta mike da taimakon Allah tachi gaba da gudu tana chikin wannan halinne ta hango titi sai tai zama ta tasar ma titin gadan2 don neman taimako ko Allah zai tai maketa tahadu da wani akan titin ya tai make ta taje dab da titin sai ta rakube awani jikin gida tana leke ko zataga wani bawan Allah yazo da zai taimaka mata tana chikin hakane Cen sai ta hango masu binta gadan2 sunyo inda take ashe bata san ,sun hangotaba saboda walkiyar da akeyi tana ganin haka saita bargun ta Sha kwana da gudu tachigaba da gudu akan titin tana waige waige2 ko Allah zai hadata dawani akan hanya

**** **** **** ****

Ana sallame sallah suka tsaya sukai Shafa'i da wuturi sannan suka mike don tafiya sai suka waiga gun da abokin suya ke zaune don Su tafi ga mamakin su sai sukaga bashi agun abun ya matukar basu Mamaki don sun Saba ko sun idar sai sun jirashi amma yau yariga su,ma tafiya Kuma baima kowa sallama ba. * Suka firfito sukai chirko2 kowa da abunda zuchiyar sa ta ke kitsamai.

Wannan kenan

Happy Ramadan in advance.

Allah kasa Muna cikin 'yantattun bayi.ameen

Star Nucee360✨💫

ISMATWhere stories live. Discover now