❄❄🏵🏵 ❄ ISMAT ❄
🏵 🎍 🏵 ❄❄🏵🏵❄❄
Written ✍
By
Nusaiba i Usman Z. S
Online Hausa Wrtters. (O.H.W)
Baiwa Writters Association. (B.W.A)
View...
nusaibaiusmanzs.WordPress.com
19.
Shopping Mall sukai siyayyan baby da mahaifiyar sa 'yan abun buk'ata suna gama siyayya sika l nufi Hospital d'in yaje yabaiwa Nurse din ya tambaye ta mi'aka samu tace masa baby boy sak kai farinne kawai irin na mahaifiyar sa da hancin yayi dariya yayi mata godiya ta wuce ta koma ciki suka gama kimtsa ta da yaron da ita ko sai barci take aka maida ta resting room, Dr ne ya fito suka gaisa ya ce kai ne ka kawo mai haihuwa Alh ya ce eh Dr ya ce to ka biyo ni office yace to suka d'unguma zuwa office suka zauna suka kumayi musabaha, Dr ya ce Alh ya akai kuka bar wannan matan ta wahala haka don ko awo kamar ma batayi sabo da alamomi sun nuna ita da yaron duk dole sai mun d'aura su kan magani don lahiyar su in ba haka ba za'a iya samun matsala barin ma uwar Allah ne kawai ya taimaka ta iya haihuwa da kanta da ba hakaba da sai dai ayi mata aiki Allah ne kawai ya kawo mata wani k'arfi har ta haihu koni nayi mamaki saidai cikin ikon Allah ba mamaki shine kawai, don da ta k'ara wasu awoyi ba'a kawo ta Hospital ba da ta kamu da ciwon yoyon fitsari shi yasa akeso mace dataji, taga alamar nak'uda tai maza ta sanar a garzayo da ita Hospital. Don Allah yan uwa akiyaye, Alh ya ce to nagode Dr za'a kiyaye insha Allah, Dr yajawo farar takarda yayi rubutu yamik'a ma Alh ya ce gashinan wad'annan magungunan muke buk'ata ayi maza a kawo kuma zamu rik'e ku harsai bayan 1week sannan zamuyi discharging naku saboda akwai taimakon da zamu bata sabo da kar asamu wani matsala Alh ya ce to mungode ya tashi ya fita yage yasayo magungunar ya dawo yaba Dr sannan Dr yakira Nurse ta kai d'akin da Hjy Samina da baby ta Alh ya nufi dakin da aka kwantar da ita. Duk tausayin ta ya kama shi, duk ya tsani kansa shi ganin abun yake kamar a mafarki yana tambayar kansa abun da baida amsa wai yaushe Samina tai ciki banda labari? Abun da sukai shekara da shekaru suna nema amma ta samu ciki ta k'i sanar da shi? Shin ina naje har da banma ganta da ciki ba? Nidai nasan banyi tafiya ballan tana nace? Amma ko bani gari ta fad'a mani in munyi waya? Amma ai koda yaushe muna tare da Hjy Zaliya bata tab'a gayamini Samina na da ciki ba to ko itama bata da labari ne?. "To meke faruwa da nine". Ni duk ma na rikice meke shirin faruwa da nine ko ince ya ma faru ya dank'e kansa da hannu bibbiyu kansa na masa wani irin juyawa kamar zai fad'i yayi maza ya zauna a gefen gadon da Hjy Samina take ga wani irin nauyi da ciwo da kansa ke masa kamar zai tsage ba abin da yake ambato sai sunan Allah zuciyar sa tai masa bak'i ta cunkushe yarasa dalili sai, addu'a yake kwararowa "'LA'ILA HA'ILLAH ANTA SUBHANAKA INNI KUNTU MINALZALIMIM'"yanayi ya na maimai tawa ahaka harya samu sauk'i har cikin ransa. . . . . . .
5 days later.....
Baby ne keta tsala kuka wata Nurse nata jijjiga shi Dr ne ya murd'a handle d'in k'ofar ya shigo ya na tambayar Nurse d'in meke damun sa shine take gaya masa yau gaba d'aya yaki shan madaran da ake ba sa shi ne yakarb'e sa ya duba sa ya mik'a mata shi ya kuma gaya mata maganin da zata ba shi, ta fita ya k'ara sa gun Hjy Samina da har yau bata farfad'o ya dudduba ta, Alh ne ya murd'a handle d'in kofar d'akin ya shi go suka gaisa da Dr sannan ya ce ma Dr,. Dr naga har yau bata farfad'o ba ko dai da matsala ne Dr ka sanar da ni Dr yayi jim sannan ya ce ba haka bane Alh jigatuwar da tayi ne shi ne yasa har yau bata farka ba amma komai yana tafiya yadda muke ko daga yanzu zuwa gobe in bata farka ba dole mukuma yin wani abun Alh ya ce to Allah ya shige mata gaba ameen inji Dr sannan suka sallama ya kama hanya ya fita Alh na kallon Hjy Samina sai yaji hawaye na bin kumatun sa yarasa dalili tausayin ta yake ko nadama ya ke oho yarasa dalili shi tunda aka haifi baby bai d'auka shi ba ya rasa dalili sai yayi kamar zai d'auke shi sai ya kasa ko meye dalili oho . . . . .
4 Hours Later
Motsa idon ta tafara k'afarta ma haka sai hannun ta da ta d'aura a kan ruwan cikin ta, ta shafa tana furta addu'ar ta shi daga barci, . "Alhamdulillahillazi ahayana ba'adama amatana wa'ilaihinnushu", . Tayi mik'a tana salati bata k'arasa ba sabo da wani azaba da ta ji, ya ratsa ta a hannun ta da k'asar ta ya sa ta saki wata yar k'ara, wanda yayi sanadiyar farkawar Alh daga gyangyad'in da ya keyi ya yo kanta da sauri yana tambayar ta ya jiki yane mata sannu, sai ta saki baki galala tana kallon sa da mugun mamaki don ita atunanin ta KO da mutuwa zatayi bazai kulata ba amma gashi yazo yane mata sannu sai alokacin sai ta kalli d'akin da take, taga ba d'akin ta bane sai taci baba da kallon d'akin ko ina da ina har tazo kan godon da aka ije mata baby ta, ta ka sheshi da ido farar d'aya taji son baby ya shiga ranta har take cewa dama baby ta ne amma kuma baby yana kama da Alh ta ce ko zaliya ce ta kuma haihuwa oho sai cen ta tuna cewa itama fa tana d'auke da ciki sai tai sauri ta shafa cikin ta ji wayam sai ta kuma yun kura zata tashi ta zauna sai taji wani irin azaba ta k'asan ta kumatayi alamar a kwai part ajikin ta to ko period nake ta kuma kallon baby ta kafeshi da ido kamar ta had'iye sa. . . . . .
Tunda ta farka da abubuwan da takeyi akan idon Dr ne don yazo wucewa yace bara ya k'ara duba ta sai yaga ta farka sai yayi tsaye yana kallon ta shima Alh bai ce mata komai ba, sai hawaye ya ke fita a idon sa da yaga ta kafe baby da kallo sai yaje bakin gadon baby ya d"auko shi ya mik'a mata, ta karb'i baby cikin zumid'i ta sakin ma Alh tattausan murmushi da shi ya manta rabon da ayi masa irin shi ya saki wani wawan ajiyan zuciya da ita kanta Hjy Samina sai da ta d'ago ta kalle sa sannan ta mai da kallon ta gun baby da keta sharar barci tana ta masa murmushi shiko baby baima san tanayi ba, Allah ya jawo kujera ya zauna kusa da ita ya kalle ta ya kalli baby duk sai suka bashi tausaya da sha'awa Dr ne yayi gyaran murya ya nufo ta da fara'a akan fuskan sa ya ce mata sannu da jiki ta gyad'a masa kai ya ce yanzu ina ke maki ciwo ta sunkuyar da kanta k'asa sai ya fahimci bazata iya sanar da shi ba sai ya kira Nurse ya ce ta tambaye ta abun da ke damun ta ya kuma cema Nurse d'in ta taimaka mata tayi wanka ta gasa jikin ta Nurse ta amsa da to sir sannan tayi gaba ta shige d'akin kasance wa a k'ofa sukai maganar ta je ta aiwatar da abin da Dr ya fad'a mata Hjy Samina ta ji d'ad'in yin wanka nan sannan Nurse ta tambaye ta mekuma ke damunta Hjy Samina ta ce bakomai dama k'asana ne amma yanzu da nai wanka naji d'ad'in gun Nurse tace dama sabo da 5days baki farfad'o ba ne shiya sa bakiyu gashi ba yadda ya kamata ba ne shiya sa jikin yayi tsami amma yanzu insha Allah KO mai ya wuce sai fatan Allah ya karo lahiya Hjy Samina tace amin Ngd sannan ta fita ta ce ki tabbatar kin bashi ya sha ta ce to in kuma bazaki iya ba in tsaya in tai maka maki kinsan haihuwar fari duk sai mun koya maku yadda akeyi Hjy tai murmushi ta ce insha Allah zan iya Nurse ta ce to sannan ta karisa fita ta taxi Hjy ta d'auki baby ta fara bashi abunci yana k'arb:a ya fara tsotsa da sauri2 sabo da dama abun da yake nema kenan ta saki Yar k'ara sabo da zafin da take ji lokacin da ya cabki kan mama. . . . . . .
Muna Mugun Tare🤝 . . . . .
Taku Har Kullum . . . . . .
Star Nucee36O✨💫