❄❄❄🏵🏵 ❄ ISMAT ❄ 🏵 🎍 🏵 ❄❄🏵🏵🏵❄❄
Written ✍ _*By
Nusaiba i Usman Z.S
®Online Hausa Writters. (O.H.W)
®Baiwa Writters Association. (B.W.A)
View
nusaibaiusmanzs.WordPress.com
O3.
**** **** **** ****
Ta fannin saleem kam sanda ya sallame sallah sa ya gyara zama abunsa yana Kallon lokacin da suka bi rubibin masu fita suka fita don dama yasan batsayawa zasuyi ba don yasan halin abokannan nasu acikin Suma dama2 salis da Usman sunfi dagewa wajen zaman masallachi tsakanin magrib da isha'i amma Ahmad sai dai yatafi in an Kira isha'in saiyadawo yabi jam'i wani lokacinma Saidai yayi a gida Shidai saleem kullum yana basu shawara akan sudunga daurewa suna zama Kodan suyi karatun Alqur'ani mai girma da Addu'oi don yasan basa samun lokacin yin hakan inba wannan lokacin ba shima dai daya gama wannan tunanin sai ya yunkura ya dauko Alqur'ani mai girma zai fara karantawa sai kawai ya tuna da wancen yarinyar dazu da ta wuce su a dandali tun da takakkiya yarinyar tai masifan bashi tausayi. Ga Yanzu gari ya lalace abu ba abuba sai Kaji ance anyi wa yara fyad'e saboda lalace wa saikaji ance dattijo mutum dan kimanin Shekara 60 yayi wa yarinya yar shekara 5 fyade wa'iya zubillah wannan Duniya abun tsoro ne,ke Duniya ina zaki damu. Yanzu ko maza ba a kyleba Suma fyade ake masu.,Akama yaro ayi luwadi dashi yanzu duk inda ka leka zancen kenan gidajen rediyoyi,Talavijin,jaridu duk dai aikin kenan Allah dai Kara kare duk bakin musulmai baki daya kabamu zaman Lfy a wannan Hamshakiyar 'kasar tamu Nageriya Amin. Yanzu kotana ina? ga dare gata diya mace? bazan iya barin ta hakaba amma kuma bansaniba ko Mahaukaciya ce?kai duk da haka Ma dai bazan iya ba sai na dubo ta ya dafe goshinsa da tafin Hannunsa wata zuciya ta ce toh wai Kai malam saleem ina ruwanka da ita sai kace wata kanwarka yadan ja wata siririyar tsaki wanda shikadai yaji abinsa ko kai/ke, ke kusa da shi baza Kaji ba wata zuciyar ta ce amma kasan duk wanda kataimaka wa Allah shima zai taimake shi Kuma, in kanwarka ce zakaji d'ad'i in haka tafaru da ita kai Ma zaka so wani ya taimaka mata Kuma kasan kaddara ce bata wuce kan kowa yaja doran numfashi wannan karan duk yan cikin masallacin sanda suka dago Kai suka kalleshi shi baima San yafito ba baimasan suna Kallon shiba amma Kuma yadau Alkawarin insha Allah komai rintsi komai wahala zaitaimaka mata Kuma yana idar da sallah zai je Nemanta duk inda take cikin darennan Alqur'anin da bai karantaba kenan. Tab'ashin da yaji anyi ne shine yayi sanadiyyar dawowar shi daga Duniyar tunanin da ya lula mai tabashinne ya ankaraddashi cewa za a tada ikama yatashi yabi sahu don gabatar da sallar isha'i ana sallamewa yayi Shafa'i da wuturi sannan ya roki Allah ya taimaka masa akan abun da yake shirin yunkura koda dai yasan halin gidan su, Kuma yasan irin halin da zasu Kuma shiga shi da mahaifiyar shi amma duk da haka Yadau Alkawari Kuma duk ya Kai kukan sa gun mai duka.
yana idar wa yatashi yafita kotakan abokanan sa bai bi ba yafita don fara neman wannan yarinyar. Allah sarki baiwar Allah.
Wannan kenan.
Muna Mugun Tare
Taku Har Kullum
Star Nucee36O✨💫