ISMAT 23.

30 2 0
                                    

❄❄🏵🏵 ❄ ISMAT ❄ 🏵 🎍 🏵 ❄❄🏵🏵❄❄

*_Written_* ✍

_*By*_

*_Nusaiba i Usman Z.S_*

*_IDON MIKIYA WRITER'S ASSO🦅_*

View....

nusaibaiusmanzs.WordPress.com

_*23.*_

Amma duk da haka saida Saleem Ahmad ya tafi mahaifiyar sa tace"in yage kada ya waiwayo gida harsai ya kammala digiri(degree) 🎓 dinsa" yana kuka tana kuka ya tafi amintattun abokanan sa suka raka sa filin girgi Aminu kano ya tafi ✈ sai saudiya("Anan saimuce Allah bada abinda akaje nema adowo lahiya")

.

..

...

....

.....

Nan kuma Hjy Samina ta kuma shiga cikin wani uk'ubar rayuwa, Hjy Zaliya ta gaiyato Samari masu jini ajika ta biyasu suka kwashe kayan Hjy Samina suka maida mata V.Q nan ta koma da zama kwata kwata bata shiga gidan, ita da ciki sai dai ta hanga, bata, bata abunci sai dai ita ta nema ma kanta abincin da zataci gashi tunda tagane duk wata anamata aiken kud'i nan ma bokan ta yayi mata maganin suka daina kawo mata, tasa akamantar dasu ita, nan fa rayuwa ta kuma cakud'e mata ahaka tacigaba da gwagwagwa don a sati bai wuci taci abunci sau uku ko hudu ba duk tabi ta lalace tai bak'i ta fyad'e ba kowa ke iya gane ta ba. Indai 'yan uwanta sunzo Hjy Zaliya taita tarairayan ta sukuma kamar ta hadiye su don murna ganin yadda ta lalace sukace zasu tahi da ita amma afafir ta k'i binsu ta ce "sai dai mutuwa zai rabata da gidan"sukace "to maiyasa kika bar cikin gidan kika dawo nan"carab Hjy Zaliya ta cabke zancen da cewa"ai nima ba yadda banyi da ita kada tadawo nan ba amma tace in tana cikin gidan Alh take ganin kamar zai shigo shiya sa ta bar ciki ta dawo nan "Hjy samina ta ce nan d'in yafiye min ciki"su a tunanin su gaskiya ne "mace d'aya ce cikin su ta lura da irin kallon da Hjy Zaliya take ma Hjy Samina tai tunanin da jikakkiya a k'asa ta dai basar.

.

..

...

....

.....

Kwanan su d'aya suka juya garin su sunkawo mata shatara Na arziki sosan gaske _kunsan tsarabar fulani basa bada kad'an_suna tahiya Hjy Zaliya tasa 'ya'anta suka kwashe abunda suka kawo tas suka maida cikin gidan Hjy Zaliya tai mata tatass sannan ta koma cikin gida.

.

..

...

....

.....

A cikin motar ne k'anwar mahaifiyar Hjy Samina take ma 'yan uwan ta magana basu karanci wani abu ba game da abokiyar zaman Samina sukace basu ga komai ba sai k'aunar juna da suke sai taja bakinta tai shiru amma ta k'udurta azuciyarta zata dage dayi mata addu'a da saukan Alqur'ani mai girma haka kuwa tafaru tana komawa gida tasa malamai suka fara saukan da addu'oi da sadaka.

.

..

...

....

.....

Wahala kullum sai k'aruwa yake ma Hjy Samina yanzu aikin gidan komai ita keyin sa wani tijara da wulak'anci ma sai 'ya'yan Hjy Zaliya sunzo to ranar bata da sukuni ko kad'an, ita da samun sa sai idan sun bar gidan kasancewar duk sunyi aure.

.

..

...

....

.....

Akwana atashi, ranaku na koma sati, sati ya koma wata, wata yakoma shekara, rayuwa na canzawa abunda yafaru baya yakoma labari. . .. ... .... ..... BAYAN SHEKARA GOMA SHABIYAR DA SUKA SHUD'E

.

..

...

....

.....

Wata had'add'iyar bakar mota mai bak'in gilas ta faka a k'ofar gidan marigayi Alh Eng Ibrahim Yamusa duk wanda yazo wucewa saiya kalla ya kuma ya kalli motar dan had'uwa ahankali yabude k'ofar motar ya zuro k'afarsa d'aya kafin ya ziro d'ayar ya fito baki daya wani kyakkyawan saurayi ne yafito cikin shigan larabawa komai nasa irin na larabawa jallabiya fara sai makawuya da babban gilas a idon sa brown tafiya yake cikin k'asaita da ganinsa kasan kud'i da hutu sun hudashi cikin gidan ya shiga ya tsaya yana kallon gidan duk gidan ya janza duk yaji jiki alamun ba'a gyara filawoyin gidan ya lalace bai samun gyara wani tsohon mutum ne ya fito daga d'akin mai gadi duk furfura yace "wani balarabe ne wannan ya shigo mana gida ba sallama" wanda aka kira da balaraben ne ya juyo ya kalle sa ya bud'e baki ya fara magana cikin hausarsa data had'e da larabci ya gaishe sa yace"ina neman Hjy Samina ce"mai gadi yace"daga ina"kai tsaye yabashi amsa "daga Yola"mai gadi ya nuna masa V.Q yace "ga sashinta nan"wannan balaraben ya nufi gunda mai gadin yanuna masa, sannu ahankali harya isa bakin k'ofar V.Q d'in yayi sallama Hjy Samina sai aikin gugan kayan da ta wanke jiya take duk kamannin ta ya canza.

.

..

...

....

.....

Gabanta ne ya yanke ya fad'i jin muryar wanda take muradin gani da ji ta dago kanta daga duk'en da take ta aza idonta kan nasa kawai sai ta fashe da kuka da sauri yaje ya rungume ta yana bata hak'uri, shima bai san sanda hawaye suka cika masa ido ba ita kuka shi kuma zabda hawaye saida ta tsagaita, kukan sannan ta d'ago kai ta kallesa tace "Saleem Ahmad ashe zan kuma ganin ka a raye bayan ancemin incire rai akanka bazan sake ganin ka ba sai dai a lahira ta kuma rushewa da kuka"Saleem Ahmad yace"Ammi waya gaya maki? ina nan gakuma shi kingan ni da rai na da lahiya na ki kwantar da hankalinki don Allah"sannan ya saketa ya karbi gugan datakeyi ya cigaba harya gama ya kashe gawawin sannan yadawo kusa da ita ya zauna yana tambayar ta ya bayan rabuwa dan inbamu mantaba yatafi ya barta cikin mawuyacin hali nan ta kwashe duk labarin abun da ya faru da ita bayan tafiyar sa, yayi kuka kamar wani k'aramin yaro saida yayi mai isar sa sannan yafara bata labarin yadda yayi karatunsa cikin d'umbin nasarori da sa'a bayan kammala karatun jami'a nane suka rikeni suka bani aiki shekarana biyar muna aiki amma hankalina na gida 9ja ina nan ina tunaninki."

.

..

...

....

.....

"Ammi rana d'aya na birkice masu na ce masu gida zan dawo sukuma sukace baza su iya yarda na saki aiki naba sai dai inje in dawo na gaya masu da kyar zan dawo sukuma sukace zasu nemoni in har bukatar hakan ya taso sun kuma barni na dawo kuma duk wata zasu na turomin da albashin wata koda bana masu aiki Ammi don nasan yadda na dawo bazaki barni na koma ba nima bazanso hakan ba in bada ke zan koma ba, don nasan ke baza ki bini mu tafi ba" "Ammi ta dafe kirji tace... "

.

..

...

....

.....

Muna Mugun Tare 🤝

.

..

...

....

.....

Taku Har Kullum👱‍

.

..

...

....

.....

*_Star Nucee36O✨💫_*

ISMATWhere stories live. Discover now