ISMAT 18.

27 0 0
                                    

❄❄🏵🏵 ❄ ISMAT ❄

🏵 🎍 🏵 ❄❄🏵🏵❄❄

Written ✍ _

By

Nusaiba i Usman Z. S

®Online Hausa Writters. (O.H.W)

®Baiwa Writters Association. (B.W.A)

View.....

nusaibaiusmanzs.WordPress.com

18.

Hiy Zaliya tayi a bin da tayi ta kawar ma baba da hankali ga Ammi na baya zuwa inda take in sun had'u kamar yaga dodo, baya iya kallon ta 5month kenan da suka fara haka. Hjy zaliya ce gurfane gaban bokan ta ta na masa godiya da irin aikin da yayi mata taga aiki yaci Tane masa kirari "Yakai boka uban ibilisai mai ayanu, k'ik'ifil da mitsil mi'tsil" "Mai yin yadda ya so. Ya kai u'ban shege da shegiya kaci dubu sai ceto Boka," Ya barke da wata irin mahaukaciyar dariya yayi ehuu ya ce sai ni uban shegu ya k'ara b'arkewa da dariya ya ce aimu in har za'a bamu had'in kai, mugamsu da irin ku ai shikenan duk wacce ta shiga bayan BAK'AR LABULE to buk'atar sa ta gama biya, yayi wani d'an suru kullen sa ya bigi k'asa sai ga wani hayak'i ya fito sai ga fuskan Samina ya baiya na a wannan hayak'in tana kwance tana ta gurmu susu ita k'ad'ai sai am baton Allah take sai hayakin ya kama da wuta dukkan su suka tsorata bama kamar Hjy Zaliya da tai zuru2 jikin ta sai b'ari yake, Boka ya sake buga k'asa abin yaki aiki saiyayi wani ehuuu mai k'ara gurin yana ta amsawa cen sai sukaji gudun doki da haniniya Boka ya mike ya gama gwalan gwalanniyar sa ya koma ya zauna ya kalli Hjy Zaliya ya ce mata da mat'sala Hjy Zaliya da tai zuruf ta kwalalo ido makar na owl ta ma kasa magana sai dai ta girgiza kai boka ya d'aura da cewa wannan kishiyar taki tana da kariya ta gun Allah kuma shiyake kareta sabo da yawan ambaton sa da take da yawanyin azkar da safe, rana, dare, da yawan yin addu'oi aduk inda take. Wannan ma maganin da yaci mijin ki sabo da shi akayi ma wa da ko ita ne bazai yuwu ba shimad'in sabo da a d'akin ki kina shagaltar da shine wajen soyayya har ya manta dayi addu'a da gun d'ayan Matan ne to sai ta tunsmai don dayakalli fuskanta zai tuna. AMMA BABBAN MATSALAN SHINE KISHIYARKI TANA DAUKE DA CIKI NA TSAWON WATA BIYAR. Ji kike kuuluuuluuuluuul cikin Hjy Zaliya ya murd'a sabo da tsananin tashin hankalin da ta shiga zufa kawai ke tsatsifo mata ji take a duniya take ko a lahira, ko dai mafarki take sai da ta mintsili kanta taji zafi sannan ta tabbatar da ba mafarki take ba sai taji duk jikin ta ya saki kamar banata ba sai kuma ta fara tunani"ni da naso in had'a ta da mijin in kashe su muci Dukiyar nasa gaba d'aya sai gashi jarababbiyar matan ta k'ara kawo mana wani bala'in. BOKA YA KATSETA DA HAURAGIYAR MURYAR SA BA'AYIN TUNANI A GUNA. in tunani zakiyi kije in kin gama sai ki dawo, ayi hak'uri boka ta ce sonake akashe su duka ita da abun da ke cikin ta akuma kashe shi ma mijin nawa. Boka ya barke da dariya ya ce duk wannan mai sauk'i ne amman wannan aikin da zan maki ba'a so mijin ki yasan tana da ciki da zaran yaji komar zai karye ta ce to, boka yayi abin da zaiyi ya bata magungunan da yadda zatai amfani da su ta tashi ta fita da baya2 tana tsallen kwad'o(frog jump) tana komawa gida taje ta barbad'a maganin a k'ofar gidan da kofar d'akin Hjy Samina, ta kuma yiwa mai gidan ta girki da d'aya daga cikin maganin da Boka ya bata mai gidan na dawowa ta kanainaye shi da kissa ta bashi abincin RASHIN SANI YAFI DARE DUHU yaci yana gama ci sai bacci ya kwashe shi tunda ga nan daya farka ya kuma jagulewa wannan karan harda dangin sa ya tsana ya daina taimakon da yake basu kuma yace kada wanda ya kuma tako masa zuwa gida inba haka ba duk abunda yayi wa mutum shiya ja sa a lokacin suka fara ganin ranar Hjy Samina yadda in suka zo take masu kamar ta goya su don murna, haka in zasu tafi tabasu abubuwan ma da basu san da su ba tai masu shatara na arziki sannan sutafi. Hakanan suke zira masa ido suna taya Hjy Samina addu'a Alh ibrahim ko gun k'ofar ta baya kallo, in kuma ya zo zaiyi addu'a ko azkar sai ya rasa miya ke hana sa sai wani abin ya d'auke masa hankali yayi gaba. Hjy Samina tana nan tana ta fama da jiki ba kuma mai zuwa gunta kasancewar ita ba Yar zaria bace bafulatanan Adamawa ce to sukan d'ad'e basu zo ba, da kyar Hjy Samina keyin aikin fannin ta ta kwana uku bata ci abinci ba sai dai ta sha "Tea"hakanan take gudanar da rayuwar ta cikin ta har yakai wata wata tara 9month ba ta tab'a zuwa Hospital da sunan yin awo ki duba lafiyar ta da na cikin jikin ta Allah ne kawai ke taimakon ta.

BAYAN KWANA TAKWAS

8 days later.....

Alh ibrahim yamusa ne zaune cikin masallaci yana zaune ya rasa mai ke masa dad'i a duniya yau tunda ya tashi yarasa mai ke masa dad'i cen sai yaji wani a masallacin yana karatun Alqur'ani Alh ibrahim yamusa yaji kansa yayi masa wani irin gingirigim kamar an dauko DUTSEN KUFAINA an d'aura masa ya dik'ke kansa da k'arfi ya saki k'ara da ya razana 'yan cikin masallaci akayo kansa ana tambayar sa lahiya, bai samu amsasu ba saiya ji kamar an zare masa allura, a jiki yajishi wasai da shi sannan ya kai ya kalle mutanen da ke kansa yace masu bakomai na god'e sannan suka ce kadunga Addu'a Alh yayi murmushi ya ce nagode sannan yatashi ya fita daga nasallaci ya kama hanyar gida yana zuwa suka gaisa da mai gadi(gate man) yayi mamakin ganin ganin yau Alh ya na yin murmushi kamar an masa albishir da gidan Aljanna da kuma yadda suka gaisa da Alh koda yaushe fuska a murtuke sai fad'a da tsiya daga shi sai Amaryar sa da 'ya'yan sa kake ganin dariyar Alh, Allah mai iko annabi Mai daraja, Alh yayi nisa sai"gate man"ya tuna da dazu daya shiga cikin gidan yaji ana nishi da kuma buga k'ofa a d'akin uwar gida, sai yayi sauri2 yabi bayan Alh yana rankashi dad'e 2 Alh ya na dab da shiga falo sai yayi kira ya juyo da fara'ar sa ya amsa ma (Gata man) d'in yace Alh da ma d'azunne na shigo ciki mik'a ma Hjy aiken da tamin shine naji d'akin Hjy uwar gida ana nishi da buga k'ofa gashi Hjy Amarya bata nan sai yara shine nai tunanin Hjy uwar gida nak'uda ne ya kamata tunda su yara basu san me ake ciki ba don nai masu magana sunce umman su ta hana su shiga d'akin tunda,"Gate man"ya fara magana Alh jikin sa ya fara yimai b'ari b'ar b'ar b'ar b'ar idon Alh ya kad'a yayi ja kamar garwashin wuta"Gate man" yana ganin duk sai ya fara rud'ewa sai yafara ba Alh hak'uri yana neman gafara karya rasa aikin sa dashi yake samun na cin abinci da ci da iyalin sa da wannan aikin suka dogara bai ankara ba sai jin mutum yayi yarab ya sulale a k'asa "Gate man"ya kuma rud'ewa yayi yayi ta maza yayi sauri ya ruga bakin gate ya d'auko butar sa ya dawo ya yayyafa ma Alh ruwa cen Alh ya ja numfasa ya farka zumbur ya mik'e gate man yana sannu Alh amma ina Alh hankalin yayi gaba baya gane ma wanna yare gate man d'in yake masa ya daki k'ofar falon kamar zai b'alla k'ofar 'ya'yan sa suna falon suna kallo duk suka tsorata sukai tsuru tsuru dama gasu marasa kunga amma yau yadda sukaga Baban nasu fuska amurtuke ba mutunci sai duk suka rik'e rashin kunyar su ya gama kalle su sama da k'asa sannan yayi hanyar d'akin Hjy Samina abun da ya kuma mamaki kenan yau she rabon su da suga Baban nasu ya shiga d'akin nan sudai sunsan umman su ta ce ya sake ta tak'i ta bar gidan ta mak'ale kamar mayya shiya sa baya shiga d'akin ta sai kuma gashi kwatsam yau sunga yana k'ok'arin shiga Alh ya yaye labulen gun yaga eshe ma ankulle dakin da mukulle ne sai ya kira gata man yaban bare makullen suka shiga suna, shika sukai arba da ita kwance cikin jini bata motsi sai dai nishi da take yi kad'an2 in bama ka kai kunnen ka kusa da bakin ta ba baza kiji ba, gagun har jinin ya bubbushe Alh yayi maza ya sunkuce ta sai Hospital akai emergency da ita suka shiga bata taimakon gaggawa wata Nurse ta fito da sauri2 ta ce ana buk'atar jini Alh ya ce ad'iba nasa akaje lab aka gwada akai sa'a yayi dai dai aka samata sukai mata alluran da zai k'ara mata kuzari asamu tai nishi da d'an ko 'yar zai fito aiko suna mata da 5mint sai k'arfi ya zo mata Allah ya sauke ta lahiya ta haifo santalelen d'an ta kato Mai kama da uban sa sak ba inda ya baro sa dai ya d'auko hasken mahaifiyar sa ko dayake mahaifin nasa ba wani b'ak'i cem bane irin wad'annan mutanen ne da ake kira da chocolate color wankan tarwad'a. Nurse ce ta fito daga labor room Alh na ganin ta yayi sauri yazo gunta ya ce Nurse ta sauka ne Nurse tai murmushi ta ce eh kayan ma jinjirin na zo karba sai alokacin Alh ya tuna ma ashe ana zuwa dai wani abu wai shi kayan jarirai sabo da ya k'id'ime da rud'ewa, yace ma Nurse d'in sun manta basu zo da shiba amma bara yayi sauri ya sayo ta ce to amma kayi sauri bai amsa ta ba yayi sauri ya fice ya je gun da gate man ke tsaye ya ce masa suje Super shopping Mall zaiyi siyayya yace to har ta sauka ne ya ce eh yana ta washe hakwara kamar gonan auduga ya ja motar suka nufi Shopping Mall di'n,.

Muna Mugun Tare 🤝

Taku Har Kullum

Star Nucee360✨💫

ISMATWhere stories live. Discover now