ISMAT 10.

39 3 0
                                    

❄❄🏵🏵 ❄ ISMAT ❄ 🏵

🎍 🏵 ❄❄🏵🏵❄❄ Written ✍

By

Nusaiba i Usman Z. S

®Online Hausa Writters. (O.H.W)

®Baiwa Writters Association. (B.W.A)

View..

nusaibaiusmanzs.WordPress.com

Copy By Salamatu Sulaiman Garba Ssg(Matass)

I Dedicate Dis Page To My lovely Aunty Salamatu(Matass)

1O.

Alh dazun dana farka zanje toilet sai naji surutu kamar ana fada dana sake kasa kunne sai naji kamar ana dukan mutum yanata ehuu, sauran mutanen sunatayi mashi magana amma ban fahimci abinda suke chewa ba, amma gaskiya alhaji wanda ake dukan yana bukatan taimako, takare maganar tana kallon alhaji da fuskan tausayi, alhaji yanisa yace, toh yanzu yakikeso ayi? Tace alhaji ataimaka masa, yace to naji2, amma ke baki tunanin ko barayine sukeyin hakan don sujawo hankalin mai karan kwana? Mutum baisan shirinsu ba yatasan masu su illatashi komasu kasheshi baki daya, kinsan yanzu irin dabarar dasuka ganeyi kenan, dama hausawa sunce mai son abinka yafika dabara, tace kumafa hakane amma inshaallahu wannan bazai kasance hakaba, nan dai ta fahimtar dashi har ya yadda zai fita yatashi masu gadinsa suje su duba sugani, ya bude durowan gefen gado(side drower) yadauko bindiga(gun) ya rike dama yanada ita ya ajetane saboda kariya(protection) a matsayinsa na babban mutin, tanada lasisinta don haka gwamnatima tasan da zamanta, alhaji yafito matarsa tana biyedashi har bakin kofar falo tayi masa adduar fatan alheri yafita ita kuma takoma chikin gidan ta Daura alwala ta kabbara sallah don rokon Allah yataimaki mai gidan nata yakuma kareshi. Yana fita yaje yashi masu gadinsa yayi masu bayanin abinda kefaruwa suka dunguma gaba dayansu suka fita kowa da fitila(touch light) a hannunsa amma alhaji yace kadasu kunna sai ya umurcesu dayin hakan, haka sukayita sanda har sukakai bayan gidan alhajine yafara lekawa sai ya hangi wasu mutane sunata dukan wani gashi kwance shame2 akasa.

**** **** **** ****

Oga wannan yacika taurin kai, mizai hana mu aikashi inda baa dawowa kawai muhuta daga baya sai muduba inda yaboye yarinyar mu cika aikinmu muwuce kowa yahuta inji Ebola, acid yace gaskiyarka Ebola kayi tinani mai kyau hakan yakamata ayi kawai, danduna yace fakat, Oga yace, hakan kuke ganin yayi? Koda yake duk wanda yashiga hurumin mu mutuwace hukuncinsa, kawai ku aikasa kukaddamar masa muwuche, gaba dayansu suka amsa angama Oga, Ebola yace abinda yafi sauki shine mufasa masa kai kawai, danduna da acid suka dauko wani katon dutse, sunzo saitin kan saleem sai sukaji karar bindiga(gun) bashiri suka saki dutsen basusaniba jikake tiiim dutsen yafada akafarsu su biyun ai da wuri2 suka saki wani irin ihu don azabar da sukaji, Ebola yace kai Oga, ai yarn sandane(police), Oga yace to kowa yayi takanshi don insuka kamamu bazamuji da dadi ba tunda dama suna nemanmu ruwa ajallo(wanted).

**** **** **** ****

bangarensu alhaji kuwa sunata lekensu daidai wannan lokachin alhaji yace kushirya dana baku izini kuhaskasu nikuma zan harba sai munufesu gadan2 sukace toh, amma alhaji kamar dutse suke daukowa inji mai gadi, alhaji yace toh muje yana gaba suna biyedashi a baya, yace ku haskasu shi kuma yaharba sama suka doshi gunsu da sauri2,. Aiko kafin kaceme Suma sun runtuma da gudu sunfuta a 360 alhaji yakuma sakin sama Suma suka bisu a 360 dasukaga sun gudu sai alhaji ya kwalawa mai gadi da yaransa Kira yace sudawo tinda sun gudu, suka dawo wurin saleem suka duddubashi sukaga yasha wuya da duka sosai ko hannunsa baya iya dagawa, gashi ko ina sai jini kefita, alhaji yace kukamashi mukaishi asibiti karya mutu don naga yanashan wahala, yacewa daya daga chikin yaransa kai yimaza jeka kadauko mota, ya amsa toh daddy yatafi dasauri yana sassarfa sukuma suka tallaboshi sukamo hanyar gidan alhaji annur suna zuwa bakin kofar gidan(gate) sai suka tarar har yafito da motar yana jiran zuwansu, suka kamashi suka sashi a bayan motar alhaji yashiga yazauna tare dashi sukama hanyar asibiti shikuma mai gadi yakoma bakin aikinsa. Suna chikin tafiya saleem yanata motsa baki yanasonyin magana yakasa saboda maganar bata fita sosai haka yadinga kokari har yafara magana da alhaji ya lura yanasonyin magana sai yakai kunnensa wajen bakinsa kozaiji abinda yake fada, aikuwa akeyi saa yanajinsa kasa2 a haka saleem yakwashe labarin komai yagayawa alhaji, nan take alhaji ya umurci faisal yajuya kan motar sukoma hayin jamaa layin masallachi gida mai zaure ba kofa, aiko haka akayi kafin kace kobo har sunkai wurin kasancewar ba nisa bane da unguwar tinda a motane suna zuwa sukayi paking suka fito alhajine a gaba yayansa na biye dashi a baya, yana shigarda kansa zauren gidan jini yafarayi masa maraba yana ganin haka sai yayi sauri yawaiga inda jinin ke tahowa sai yayi arba da yarinya kwance chikin jini dasauri yaje yataba yajikinta yayi sanyi karara sai yayi sauri ya sureta kamar jaririya kasancewar batada auki, duk abinda kefaruwa yaransa suna bakin kofa suna Kallon sa da mamaki baisantaba yakama daukanta kumazai kaita mota, yasani ko aljanace? Kallifa gashin kanta kamar ba mutinba, duk maganar nan subiyu sukeyinta kasa2 kar mahaifinsu yajisu kawai sai sukaganshi gabansu yana chewa inkun gama kuzo mutafi, gakudai maza amma kuna abu kamar mata, sukayi sauri2 suka shiga mota shima yashiga tare da yarinyar a hannunsa suka Kama hangar asibiti duk kowa yayi shiru Kuma kowa da abinda yake sakawa a zuciyarsa.

**** **** **** ****

A bangaren hajiya kuwa tinbayanda ta sallame nafila rakaa biyu take zaune a dadduma(carpet ) tanata adduar samun nasara da kariya ga mijinta kasancewar tana jiyo ihu da alamun ana duka, tana chikin hakane tajiyo harbin🔫 take ta mike zumbur cikinta yabada kululu sai waige2 take a daki kamar wadda akabiyo zuwa can tazabura tayi hanyar falo, komi tatuna oho sai Kuma tadawo bakin gado tazauna sai kawai taji tanaso tayi kuka amma takasa gaba daya tadabarbarce tarasa inda zatasa kanta, kanaganinta zakagane tana cikin tashin hankali da fargaba, sai tafara tunanin miyasa tamatsa mashi yafita da tsohon daren nan, shin Harbin nan dataji kodai mijinta ko yayanta aka harba kokuma mai gadi? Don tanakyautata tunanin dasu akatafi, hakadai tayita sake2n zuci, zuwa chan tasakeyin zambur ta mike kamar an mintsileta tadauko wayarta tafara nemo numbern mai gidan nata sai kawai tajiyo rurin wayar mijin nata a bayanta sai tahau salati tace shikenan ashema bai tafi da wayanba, tana ta magana ita kadai kamar zararriya, gashi Kuma cikin kuka takeyin maganganun nata, kasancewar gidan babbane idanba kana faloba bakajin abinda ke gudana a gidan shiyasa bataji lokacin da aka fitada motaba, kamar ankuma tsikarinta tatashi tafito falo tana safada marwa can dai taga hakan ba nafita bane sai tayi wurin taga(window) aguje ta yaye labule dayake akwai hasken wutar lantarki a tsakar gidan sai tahangi mai gadi da buta a hannunsa da alamu zaije bayine tanaganinshi sai tayi maza2 tabude kofar falon tafito ta tsaya, tananan tsaye sai gashi yafito yana ganinta yadoso inda take dasaurinsa yana tambarta, hajiya Lfy naganki cikin wannan daren kinfito? Tace inafa lafiya alhaji yafita tindazun haryanzu bai dawoba shiyasa nike tunanin Anya lafiya kuwa, sai yayi wani gajeren murmushi yace, hajiya alhaji lfylau, nandai yalabarta mata abinda yafaru yakara da chewa yanzu suntafi asibiti shiyasa basudawoba sabida suntafi da yaron rai hannun Allah shiyasa bai tsayayi maki bayaniba. Alhamdulillah hajiya ta furta hankalinta yadan kwanta tayiwa mai gadi sallama takoma chikin gida, tana komawa takuma dauro alwala a lokacin anata kiran sallah nafarko watau assalatu tazo tagabatar da rakaatul fijir tazauna tana lazimi tanajiran a Kira sallan asuba don ta gabatar.

**** **** **** ****

HOSPITAL

4:37am Dai2 su Alh, suka danna hanchin motar su chikin Hospital d'in ba kowa a harabar Hospital d'in sai securities da suke ta kai komo, suna shiga wani security 1 ya taso da sauri ya karaso gun motar su Alh, Alh ya fito da wuri2 yache ma security din marasa lahiya ya kawo da sauri security din ya nufi k'ofar da zata sadashi da chikin Reception din Hospital d'in bada dadewaba sai gashi sun dawo su hudu maza3 mache1, da gadon daukan marasa lahiya, suna isowa sukache ina marasa lahiyan Alh yanuna masu motar da yatsa don kidimewa yakasa ma yimasu magana chikakke, suka gungura gadon gudu doshi motan zuwan su keda wuya suka 'balle murfin kofan suka fara kichi2 fiddo su, machen suka fara fiddowa sannan suka fiddo da Saleem duk suka daura kan gadon marasa lahiyan suka gungura su da gudu sukai emergency da su.... Kuyi Sorry friends narashin yin post akai2 hakan yafarune saboda wasu dalilai dafatan uzirina ya karbu.

Ngd

Muna Mugun Tare🤝

Taku Har Kullum

Star Nucee36O✨💫

ISMATWhere stories live. Discover now