❄❄🏵🏵 ❄ ISMAT ❄ 🏵
🎍 🏵 ❄❄🏵🏵❄❄
Written ✍
By
Nusaiba i Usman Z.S
®Online Hausa Wrtters. (O.H.W)
®Baiwa Writters Association. (B.W.A)
View...
nusaibaiusmanzs.WordPress.com
I Dedicated Dis pg to my lovely sis RUQAYYA D MUHAMMAD Allah ya kara maki lahiya ya kara kareki da kariyar sa Ameen(just for fanny Sis 😆😂🤣😏)
15.
HOSPITAL
Ruqayya D Muhammad ce ta fe da sauri don yau ta makara ga shi tanada aiki tare da Dr B hankalin ta duk ya tashi saboda tasan hali don inda sabo ta saba da irin wulakancin da yake mata tunda ya gano ta fad'a malak'on kogon k'aunar sa da begen sa bata da wani buri ayanzu a rayuwa banda taga ta mallki Dr B a matsayin mijin ta wanda zata zauna k'ark'ashin inuwar sa amma abun ya faskara tayi duk wani kissa ta da ki sisina da wani kwarkwasa da kuma kyautatawa da zata janyo hankalin sa amma abun ya faskara, banda ma abunda ya biyo baya na wulak'ancin da yake mata amma duk da haka ta kasa barin ta Dr B wanda a gida ake kiran sa da *HILAL* a hospital kuma Dr B shine abuncin zuciyar ta. "Toh ya ta iya." Tana zuwa bakin office din Dr B kawai sukayi kicib'is ya fito daga office din sa sai ta k'ara sauri zata wuce shi ya daka mata wani wawan tsawa duda ni kaina saida Alk'alamina na da jota suka fad'i don razana yayi mata wani irin kallon sama da k'asa yace sai yanzu kika ga damar zuwa ko yauma tsohon wasu kika samu kikai masa rashin mutunci? Tai shiru bata tanka shiba no Responding sai ya fara takowa zuwa gurin ta,tanajin takunsa tai maza ta juyo tace masa yi hak'uri mota ta ce ta sami matsala a hanya ta tazuwa "ohoo" ai ina sha kin kurmance ne in kira Dr Alex ya dubaki, magana yake amma ita sai kallon kekkyawar bakin sa ta lula duniyar tunani tunda turaren sa mai sanyin kamshi da kwantar da hankali ya daki hancin ta sai ta sauke ajiyan zuciya ta kafeshi da dara daran idanun ta masu kamar madara ga bak'i eye ball din ta kamar an d'isa su, jitayi an jijjiga ta tai firgigit ta dawo duniyar mutane, ke amma ke kin faya shirme kinsan tun yaushe nake nan nake maki magana kuwa tunanin me kike harhaka,Ruqayya ta sauke ajiyan zuciya Hmmmm!kema kinsan wazanyi tunani in banda gogan nawa,to ay harya tafi yace in kika gama tunanin kije kisame shi a "Lab"ta ware ido tace da gaske face yap Ruqayya tace ya salam shikenan zai kuma rainani,Noor tace raini kuma eh mana Hmmmm!wai miye tsakanin ki da shine kuke irin wannan Game din Hmmmm kedai bari bara naje mayi magana anjuma bye Noor itama tace bye, da sauri2 ta bud'e office din ta ta shiga ta ije handbag din ta ta dauki rigan ta tasa da yan tarkacen aikin ta, ta fice ta kama hanyar"Lab" takai kusan 5 mint kafin ta murd'a handle din k'ofar"Lab"din ta shiga tana shiga sukai ido hudu da shi tai maza ta dake,wani irin mugun kallo yake jifanta da shi tai maza ta kama aikin dake gaban ta, shi kuma yayi maza ya dakatar da ita me kuma ya tuna Ohoo sai ya ja dogon tsaki yace tafi dama hakan take jira don duk ta tsorace a haka dai suka gama aikin kowa ya kama kansa amma Ruqayya D Muhammad tana cikin farin ciki da annushuwa kasancewar duk ranar da sukai aiki tare da muradin ta haka ta ke kasancewa ta shiga office a gajiye ta wancakalar da kayan dake hannun ta ta shiga toilet ta d'auro Alwala ta zo ta gabatar da sallah Azuhur ta mik'e k'afa akan sallaya tana hutawa tana tunanin abun begenta tana murmusawa abun ta _~Oh ni Nucee36O nace soyayya mai sa mutum ya zama k'aramin mahaukaci~_ Ji tayi an zungureta firgigit ta dawo duniyar mutane ta d'aga kai tana kallon ta a'a Noor harkin shigo kenan uh tun d'azu na shigo na k'ari surutu na nagama amma naji shiru lafiya dai ko? k'alau in ji Ruqayya hakama d'azu kikayi ma Dr B yayi magana amma hankalinki ma baya jikin ki wai ke meye hakane da kingan shi duk sai kibi ki shagala da kallon sa,Rukyns ta sauke goron numfashi Hmmmmm! kedai bari. To duk ba wannan ba zuwa nayi yau naji labarin ki don kullum kike janmini aji akai yau dai baki da uzirin da zan barki, ki subuce min yau ehe Rukyns tai dariya tace yanzu dai labarinta kike sonji, Noor tace eh Rukyns tasauke dogon numfashi Hmmmm! tace labarina3 ok yanzu ko zakiji. Yanzu aka fara.
Muna Tare
Taku Har Kullum
Star Nucee36O✨💫