ISMAT 22.

21 0 0
                                    

❄❄🏵🏵 ❄ ISMAT ❄ 🏵 🎍 🏵 ❄❄🏵🏵❄❄

_*Written*_ ✍

_*By*_

_*Nusaiba i Usman Z. S*_

*IDON MIKIYA WRITER'S ASSO🦅*

View...

nusaibaiusmanzs.WordPress.com

_*22.*_

Ya jingina bayan sa da jikin kujerar motor ya daga kansa sama ya jinginar da kansa saman kujeran motar ya runtse ido kamar wanda wani abun zai shiga masa idon kamar an muntsine shi ya bude ido wata katuwar motar tanka ne tayo kansu a sukwane Alh yayi k'ok'arin sa driver ya kauce amma abun ya ci tura ta ke suka had'e da motar suka kama da wuta.

.

..

...

....

.....

Sukai gefen titi motoci biyun basu daina tafiya ba kuma wuta saici yake wata k'atuwar bishiyar rimi ce tai masu burki a inda motar su Alh ta noke baza ace mota bace.

.

..

...

....

.....

Sanda motocin suka had'e Alh ya yi baya gilas d'in kusa da shi ya fashe wayar shi tai tsalle ta fita ta windon motar, kurmus sukayi sai dai aka kwashi tokar su bayan wutar ta lafa ne aka fara tunanin yadda za'a san yan ina ne su ba shaida yan sanda da suke gunne suka fara bincike daga inda motar suka had'e har zuwa gun da bishiyar tai masu burki cikin sa'a d'aya daga cikin yan sandar ya samu wayar Alh sai ruri take cikin hanzari ya kara sa gun ogan su inspicter Zaharadden ya mika masa ya ce ga wannan yanzu na ganshi cikin ciyawa ogan ya karb'a yana dubawa cen sai ga wani d'an sandan ya taho da lambar mota ya tsintoshi cen cikin sunkuru ya mik'a wa ogan na su ya duba yaga ni sannan shima ya ije sa gefe d'aya har'yanzu dai wayar sai neman agaji take daga sunan yasan matar mai wayar ne.

.

..

...

....

.....

Zaune take bisa d'aya daga cikin kujerun parlor ta, ta jingina bayan ta da kanta a majinginin kujeran wani mummunar tsinkewar gaba ne ya ziyarci zuciyar ta da yayi sanadiyar tashin ta a gigice Saleem Ahmad da ke kwance a jikin ta sai da ya tashi shima afirgice kasancewar ya fara barci ya fashe da kuka ta fara lalashin sa amma hankalin ta baya gunsa ta janyo wayar ta, ta fara kiran lambar mijinta kira take ba k'ak'k'autawa ji tayi ba abun da takeso sai jin muryar mijin ta a dai2 wannan lokacin ne kuma sai ta ji an d'aga wayar ta fara magana gaban ta ne ya tsinke ya fad'i da taji bakuwar murya salati ta fara duk ta rud'e tana tambayar ina mai gidan nata daga cen ya fara bata baki ya samu hankalinta ya kwanta sannan ya fara mata magana cikin dabara ya sanar da ita inda zata zo ahaka hankalin ta badai ya kwanta ba ne taja mayafinta ta fita ta kira gateman ya tukata suka tafi 1hour ya kaisu gun a sukwane ta fito tai gun da sukaga cincinrindon mutane d'an sandar ya dakatar da ita ta hanyar magana da yayi mata nan ya ja ta sukai gefe anan ogan su yayi mata bayanin abun da ya faru, kafin nan saida ya tambaye ta "waye shi nata"ta fad'a masa sannan yasan ta inda zai fara mata bayani, ta kenan ta fad'i sumamma.

.

..

...

....

.....

Sanda ta farka a Hospital( asibiti) ta tsinci kanta sai a hankali ta fara tuna abunda ya faru kasancewar Allurar da akayi mata jikin ba kwari sai kukan da ta keyi a kwance gateman ne a gefenta yayi maza ya fita ya kira Nurse tazo ta dubata sannan ta kuma yi mata allura, don ta samu nutsuwa nan take barci ya d'auketa bata kuma sanin inda take ba har sanda ta kwana biyu Sannan ta farka a gidan ta, ta tsinci kanta sai 'yan uwan ta da ta gansu cike da d'akin ta da d'angin mijin ta, kowa sai tausaya masu suke itama kukan mai bantausayi ta farayi mai tsuma zuciyar mai karatu duk ta dawo wata abun tausayi cen sai ga Hjy Zaliya ta shigo da kukan muna furci ta rungume ta ta ce munshiga uku Anty yanzu shikenan mundawo marayu Alh ya tafi ya barmu a gabbar da muka fi bukatar sa wayyo🙆🏻 yanzu ya zamuyi nan suka rungume juna sunata kuka sai gidan ya kara rikicewa da kuke2 'yan uwa da abokanan arziki kowa ya kalle su sai su bashi mugun tausayi sai sukuma fashewa da kuka da kyar aka rarrashe su anan suka wuni gyam sallah kawai ke tada su a haka akayi bakwai kowa ya watse da 'yan uwan Hjy Samina zasu tafi nan ma tasha kuka kamar me.

.

..

...

....

.....

Yanzu gida ya koma daga su sai 'ya'yan su ahaka suka ci gaba da zama harzuwa sukai fita takaba nan akazo maganar rabon gado Hjy Samina tace basai anraba ba kawai suci gaba da zama hakanan kamar da yadda suka saba kowa yana amfani da abunda yake da bukata Hjy Zaliya ba k'aramin d'ad'i ta ji da wannan maganar ba, don tariga da tasan tuggun da, ta ke shirya wa shiya sa ta sa bokanta ya rufe mata baki dan ginsa aka basu nasu hakkin sauran kuma aka mika masu. ko wanna ma'aikata zasu cigaba da aiki kamar yadda suka saba, file d'in aka mik'a wa Hjy Samina ta k'arb'a ta mik'a wa Hjy Zaliya ta ce ki ije a gunki, Hjy Zaliya tace ayi haka Anty kece babba ke yakama ta ki ije Hjy Samina tace sai kace ba d'aya muke ba haba Hjy Zaliya tai wani shu'umin murmushi😏 ta karb'a nan suka yi sallama da lauyan Alh ya tafi suma sukai d'aki, Hjy Zaliya na shiga d'aki ta fara rawan💃murna harda kwaso Shoki👯abunda ta d'ad'e tana bid'a yau gashi yazo hannun ta, tace Samina zaki gane kuranki na yarda dani da kikayi, kika mik'a min duk dukiyar Alh saikin dawo abun tausayi a gidan nan "duk wanda ya ci tuwo dani miya yasha" tai kwafa ta wuce kan gadon, ta kwanta tana tunanin ta inda zata fara da kud'in.

.

..

...

....

.....

Hjy Zaliya taje gun bokan ta ya kafeta ya kuma rufe mata baki bata datacewa ga duk abunda Hjy Zaliya tazo mata dashi ta dawo kamar wata baiwa a gidan.

.

..

...

....

.....

Saleem Ahmad harya kammala primary d'in sa yanzu shirye2 tafiyar sa Saudiya karatu take don tacika ma mahaifinsa burin sa, nasa d'ansa ya zama USTAZ angama komai ranar d'agawar sa kawai suke jira.

.

..

...

....

.....

Hjy Zaliya dai duk bata gane kansuba na irin wannan hidima da sukeyi ina suke samun kud'i don tasan ko yunwa zai kashesu Hjy Samina bata da bakin da zata iya tambayan ta KO da kwayan masara balle shinkafa bata gama tsinkewa ba saida tafita gari taji ana cewa Saudiya zaije karatu nan su Hjy Samina sukaga tashin hankali...........

.

..

...

....

.....

Muna Mugun Tare🤝

.

..

...

....

.....

Taku Har Kullum👱

‍ .

..

...

....

....

_*Star Nucee360✨💫*_

ISMATWhere stories live. Discover now