🏵❄❄🏵🏵 ❄ ISMAT ❄ 🏵 🎍 🏵 ❄❄🏵🏵❄❄
_*Written*_ ✍
_*By*_
_*Nusaiba i Usman Z. S*_
Online Hausa Writter's. (O.H.W)
Baiwa Writter's Association. (B.W.A)
View...
nusaibaiusmanzs.WordPress.com
5 DaYs To My Birthday🎊 🎊 🎊 🎊 🎊 🎊 🎊🎊 💃🏻💃🏿💃🏻💃🏿💃🏻💃🏿💃🏻💃🏿💃🏻💃🏿💃🏻💃🏿💃🏻💃🏿💃🏻🤷💃🏻💃🏿💃🏻💃🏿 🎉🎉🎉🎉🎉🎉🎉🎉 _SAVE THE DATE_
_*21.*_
Alh yayi dariya ya ce ai ni d'ana ustaz ne da yardan Allah karki damu kici gaba da masa Addu'a ya zaro wata farar takarda da daga aljihun sa ya mik'a mata hannu na rawa ta karb'a yaja hannun ta zuwa bakin gado ta bud'e ta duba tafara karantawa galala ta bude baki tana kallon takardar sannan ta dago kai tana kallon Alh tace yanzu duk wadannan miliyoyin kud'in a wannan makarantar kawai ya juyo ya d'an tsira mata ido yana nazartan wani abu daga gare ta sannan ya bata amsa da a'a har ya gama makaranta da kuma aiki zasu isa harma da ragowar canji sabo da halin rayuwa kinsani na sani mune ka dai muke son dan mu a gida nan wancen tarbiya da tayi wa 'ya'yan ta hudubar shedan, dadin sautin bugun gangan shedan yariga da yayi tasiri a kunnen su neman halaka ni ko ke ko shi take ido rufe, jiya na dawo masallaci nazo wucewa lungun windon ta naji tana waya da wata nan naji duk abun da suke kitsima wa da yiwuwa tana shirin yin wani abunne amma babu abinda dan Adam ko Aljan ya isa yayi maka wanda Allah bai ma ba amma akwai tsautsayi da sila don haka dole mu k'ara taka tsantsan a gidannan.
.
..
...
....
.....
Babu abunda Hjy take sai zubda hawaye ya kuma zaro wasu takardu ya ce wadannan k'ada rori nawa,duk naki ne nariga da na mai da su kin siya ne a hannu na komai na ciki keda Saleem Ahmad kamar yadda nake nuna masa gata haka nakeso kema ki nuna masa, nasa amintattu cikin ma aikata na zasu ringa kula da maki da kamfanin ki da na Saleem Ahmad in kud'in kike buk'ata akwai number da na sassaka a cikin file d'in duk wanda kika kira cikin su zasu baki ko nawa kike buk'ata tunda ke ce mai gidan su nayi hakanne saboda bbanso RIKICIN GADO ta, taso a cuce ki ke da d'anki kuma dama na d'ad'e dayin Alk'awari a zuciya ta zan mallaka maki wasu cikin kamfanina keda 'ya'yan ki don Allah ko bayan ba raina ki kulamin da kanki da yaro na don Allah Hjy Samina tayi jagab da hawaye don kallon maganganunsa take kamar wasiyya ya ke bata zatai magana yayi saurin rufe mata baki ya ce nasan me kike son cewa itama na basu na su kamfanin ita d'aya da 'ya'yan ta na fita hakkin kowa.
.
..
...
....
.....
Godiya kawai ta ke nasa tana kuka Alh zai cigaba da magana kenan tai maza ta rufe masa baki ta had'a hannun ta gu d'aya ta ce plsss ya isa haka tashi kayi wanka kaci abunci murmushi kawai yayi ya nufi bafroom yayi wanka ya fito ya ci abunci sannan suka d'unguma zuwa d'akin Saleem Ahmad har yayi barci suka gyara masa kwanciya sika mai addu'a sannan suka rufo masa d'akin suka tafi nasu d'akin. Sai ince Asuba ta gari.
.
..
...
....
.....
BAYAN WATA TAKWAS.....
.
..