ISMAT 24.

96 2 0
                                    

❄❄🏵🏵
❄ *ISMAT* ❄
🏵 🎍 🏵
❄❄🏵🏵❄❄

*Written* ✍
*By*
*Nusaiba i Usman Z.S*

*IDON MIKIYA WRITER'S ASSO*🦅

Dedicate This Page to
*Little Princess 👸*

*24.*

Ammi ta dafe k'irji tace"niiii in bar gida yaro gadon gida alaliga rago kowa ya bar gida, gida ya barshi"Saleem Ahmad yayi dariya ya ce ai nasani Ammi baza ki bini ba nan suka ci gaba da hiran yaushe gamo basu ankara ba ji sukayi an bankad'o k'ofar ɗakin saura kaɗan a buge Ammi da zafin nama Saleem Ahmad ya tare ƙofar ba kowa bace tayi wannan aikin sai Hajiya Zaliya tana ta huci, tijara tafara yi wa Hajiya Samina kamar yadda ta saba ashariyya ta uwa ta uba haka ta ɗinga surfa ma Hajiya Samina Saleem Ahmad bai san sanda ya damƙo wuyar ta ba ya haɗa ta da bangon ya shaƙe ta sai kakari take.
Ammi sai kuka take tazo ta kama dukan sa tana cewa "ka sake ta tunda ka shaƙe ta nima zaka iya shaƙeni ka sake ta ko nayi maka baki kabi diniya" Saleem Ahmad baisan sanda ya sake ta ba ya durƙushe gaban Ammin sa yana mai zub da hawaye ya ce "Ammi sabo da wannan abun zakiyimin bak....'bai ƙarasa ba sabo da marin da yaji an ɗaukeshi da shi ɗaga kan da zaiyi sai yaga Ammi ce ta mare sa mamaki da al'ajabi ya kama sa na canjin da Ammi tayi bai gama mamaki ba sai da ya tsinkayo muryar ammi na ba Hajiya Zaliya haƙuri ta zuba gwiywowin ta a ƙasa tana mai bata haƙuri kamar wata uwar ta.

Sabo da takaici ta shi yayi zai fita Ammi ta tsaida shi taima sa nuni da inda take taimai alama da yayi abun da tayi wani malolon baƙin ciki ne ya zo ya tokare masa maƙogaro bashi da zaɓi hakan nan yazo yayi ya bata haƙuri sannan ya tashi zai fita Hajiya zaliya ta dakatar da shi ta ce "motar waye a ƙofar gida"?ya juyo da jajayen idon sa da suka koma kamar garwashi ya ce"nawa ne"tace "miƙomin makullin da ƙuɗaɗen da suke jikin ka"wani kallo da ya willa mata ba shiri ta kalli Hajiya Samina ta ce"to ke sai ki gaya masa tun da ni ban isa da shi ba" Ammi ta buɗe baki zatai magana kenan ya ciro duk abun da ya ke jikin sa ya wulla mata ya ce"in kika ƙarɓa masu mota kikaji sammaci ke kika ja wo ba abun da ya dameni"ya fice Hajiya Zaliya da ta tsani hukuma ta gwalalo ido ta ce"ɗauki abunka na fasa waɗannan ƙudin ai suma suna da yawa zasu kashemin wata kafar" ta tattara ta ce ma Hajiya Samina ki kwasomin kayana ki kawomin ɗaki ki ɗaura mani girkin dare ta fice jiki na ɓari kamar mazari.

Saleem Ahmad takaici ya rufe shi kamar zaiyi kuka dan takaici ya fara jefo wa kansa tambayoyi
wai yaushe Ammi ta koma haka ne?
irin wannan rawar jikin kamar maharfiyar ta tai mata magana?
to ko aikin da take yi kamar inji ne shiyasa ta koma haka?
duk ta lalace anya da lahiya kuwa.

Haka rayuwa ta ci gaba da tahiya ba ɗaɗi ga Saleem Ahmad yau da ɗan ɗaɗi gobe sai a hankali komai ya shigo da shi gidan sai dai Ammi ta kai wa Hajiya Zaliya sai abun da ta ɗauko ta bata ahaka sai da Hajiya Zaliya ta sa Ammi ta ƙarbe komai na hannun sa motar ne ka ɗai ta kasa ɗauka sabo da taji zancen hukuma.

*BAYAN WASU SHEKARU......*

Saleem Ahmad yanzu duk ya sukurkuce yayi baki kamar ba shi ba duk da kuɗin da yake samun saƙo duk wata na gun aikin sa na Sadiya kwata kwata bai nuna yana da ƙuɗi don ya fahimci Hajiya Zaliya lashe money ce idon ta idon kuɗi ce shi yasa ya daina nunawa sai indai ta kai maƙura ya ke ɗaukan wani abun yayi amfani da shi yanzu bai da abokan hira sai abokanan sa tun na yarin ta su Salis suma in abun taimako ya zo yana taimaka masu sunsha bashi shawaran ya ɗauki mahaifiyar sa su koma Saudiya da zama ya ce masu bazai yiwu ba sabo da kullum yayi mata magana amsa ɗaya ce taga mai rabata da gidan mijin ta wani lokacin ma kuka take sakamin wai ina so in rabata da mijin ta kuji fa sai kace yana da rai.

Hajiya Zaliy tana mugun tsoron Saleem Ahmad tun randa ya dawo ya shaƙe ta, ta ke shakkar sa duk randa Saleem Ahmad bai leka Ammin sa ba ba ta jin ɗaɗi kasancewar ba gidan yake kwana ba Hajiya Zaliya ta ce baza su zauna da balagaggen jibgegen na miji da shi a gida ɗaya ba zai tanka Hajiya Samina ta dakatar da shi.

Yanzu Hajiya Zaliya tana neman kauda shi duniyar baki ɗaya ne taci shima nashi dukiyar,tasha zuba masa magani cikin abinci sa ta ce ma Ammi lallai ya ci abincin Hajiya Samina ta karɓa kamar sokuwa tana gyaɗa kai kamar wata jan kai duk kuma randa Hajiya Zaliya ta zuba wani abu cikin sai Allah ya hana Saleem Ahmad zuwa gidan ahaka suke har yanzu.

Saleem Ahmad ne zaune gaban mahaifiyar sa suna hira take ce masa"mai ya hanaka zuwa gida jiya" ya kuma sadda kai ƙasa ya ce"Ammi ciwon kai ne ya rufe ni shiya sa banzo ba amma ki gafarceni hakan bazai sake faruwa ba"nan da nan jikin ta ya kama rawa tazo tana taɓa wuyan sa tana cewa mai ya sameka kaga kai amana ne aguna mahaifinka Allah yaji ƙansa yace na kula da kai kada na bari wani abu ya cutar da kai kuma Allah ne kawai ke ƙare ka ta fashe da kuka da ƙyar na lalashe ta tayi shiru ta ce "ka da ka ƙara ƙin zuwa ganina don duk randa ban saka a ido na ba ban iya yin barci"ya ce to Ammi.
ki shirya zamu fita da ke Hajiya Samina ta dafe ƙirji ta ce"fita kuma Ahmad a'a kabar shi Hajiya ta hanani fita" "shekarun baya dana fita na shiga maƙota gaisuwar rasuwa sai da ta zane ni har ina fitsari rabona da fita tun randa ka bar ƙasar nan sai fitan da nayi ta dake ni barni ban son ganin ɓacin ran ta kaje kawai nagode"galala ya saki baki da hanci yana kallon mahai fiyar ta sa bani da halin tofawa don yanzu zamu ɓaɓe in dai na faɗi aibun Hajiya Zaliya nayi shiru amma abun na cina acen ƙarƙashin zuciya ta ƙarar waya ta ne ya fagar da ni daga tunanin da na lula na ɗaga Salis ne ke kira na mukai magana sannan nayi wa Ammi sallahma na ce na fita zuciyata a cunkushe ta ke.

Tafawa sukayi irin tasu ta samari Saleem Ahmad ya ce"to yanzu ina muka nufa"Salis ya ce"muje dandali su Usman sunacen suna jiran mu"Saleem Ahmad yace"to mu tahi kudai zaman dan dalinnan na maku ɗaɗi nikuma banga abun da ake agun ba sai musun ƙwallo ko gulman ce gulma ce nifa zama nake don banda inda zani ku kuma da Allah ya haɗa ni da ku kuna so bani da yadda zanyi saudiya ina zaku ga masu zaman banza haka na kusa baku abunyi tunda da alamu rashin abunyi ke saku zaman kashe wando" dai dai nan suka isa dan dali masu sana'a sun fara zuwa kowa na gyara gun sana'ar sa.

*CIGABAN LABARI.....*

Muna Mugun Tare🤝

Taku Har Ƙullum👱🏼‍♀

*Star Nucee36O✨💫*

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Feb 01, 2019 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

ISMATWhere stories live. Discover now