ISMAT 20.

34 0 0
                                    

❄❄🏵🏵 ❄ ISMAT ❄ 🏵

🎍 🏵 ❄❄🏵🏵❄❄ Written ✍

By

Nusaiba i Usman Z. S

Online Hausa Writter's. (O.H.W)

Baiwa Writter's Association. (B.W.A)

View...

nusaibaiusmanzs.WordPress.com

2O.

A haka tana cije baki tana runtse ido take shayar da shi har sai sanda ya saka don kansa sannan ta rungume shi ta ji sanyi da son baby da tausayin kan su ya kamata don batasan irin zaman da zasuyi in ta koma gida ba kawai sai ga hawaye sharr ya shiga bin kumatun ta.

. ..

...

....

.....

Hjy Zaliya.....

Tana shiga parlor taga 'ya'yan ta sunyi cirko2 ta kallesu galala tana daka masu tsawa meye haka kunwani cirko2 kamar wa'yan da akaiwa aikan mutuwa, dukkan su suka watsa mata kallon raini yar autar cikin su da bata wuce shekara 10 ba mai suna D'ahara ta wani watsa mata kallo ta ce Momy dai anji kunya kinsan baki abuba kikace mana kinyi, Zainura ta cabke to Momy Malamin ki yadai cimiki k'ud'i abanza don dai maganin ki bai ciba ehee, Raziqa ta daka tsalle tace wadda kikace Baba bashi ba ita to yau gashi yashiga d'akin ta shi da mai gadi sun dauketa cikin jini suntafi kaita Hospital Gateman sai wani rawar kai yake kindai ji kunya Momy da girmanki kin mana k'arya Hjy Zaliya da tunda suka fara magana tai suman tsaye, tafad'i yaraf ak'asa ta kasa magana Nabila da tunda suka fara magana bata tanka su ba saboda takaici daya turbune ta ta ce Momy wlh kin ban kunya da ina alfahari da ke amma yanzu kin sa nafara haufi akan ki Malama zama baiganki ba kitashi kisan abunyi don mu bama buk'atar zama da wata mai suna kishiya ehee.

.

..

...

....

.....

Hjy Zaliya da tunda taji abun da 'ya'yan ta suka gaya mata taji kamar saukan aradu gaba d'aya duniyar ta juye mata, tunanin ta ya gushe tama rasa ta inda zata fara don tunda suke da bokanta bai tab'a yi mata aiki ya wargaje kamar wannan lokacin ba dole nema taje ta ziyar ce shi. Tashi tayi daga inda ta baje ta yayimi gyalenta da jaka tai d'aki. tanar 'ya'yan ta anan sunata mitan su baza su zauna da wata a gidan ba mai suna kishiya tana, tana shiga d'aki ta zube kan gado ta wullar da jakar hannun ta ta kwanta tana tunanin yadda za'ayi taga bokanta da gaggawa don ayanzu kodama zataje gurin nisa zai mata ayadda ta zak'u ta san yadda zatai da wad'annan mutanen da suke k'ok'arin hanata rawar gaban hantsi, ta lula cikin duniyar tunani, ko mai ta tuna oho ta mik'e zumbur kamar wacce aka tsikara da allura, tai cikin drower kayan ta tafara bincike kamar wata motsatstsiya daga cen k'asa cikin wani akwati ta bude ta fiddo wata farantin silva mai kyalli har yana kashe ido mutum ya kan hangi fuskan sa ciki kamar madubi ta kuma fiddo da wata fararr takarda ta bud'e ta fara karanta rubutun da ke ciki tana gama karatun idon ta yayi haske ta d'auki farantin hasken idon ta ya daki farantin sai ga fuskan bokan ta ya bayyana nan tafara masa bayanin abun da ya ke damun ta kafun ta k'arasa ya karasa mata, inda Hjy Zaliya ta bukaci a kashe su baki d'aya, Boka ya amsa da cewa wannan mai sauk'i ne ki duba bakin k'ofar d'akin ki zakiga kullin magani ki d'auka ki sa masu a abinci kada kuma kibari a samu wata matsala tunda kinyi sake wancen aikin ya karye Hjy Zaliya tace ayi hak'uri boka wannan baza'a samu Marsala ba za ayi yadda kace kuma nawa ne kud'in da za'a buk'ata boka ya bushe da wata mahaukaciyar dariya yau nine da kaina zan ziyar ceki da dare don haka ki shirya da kyau ya k'ara wage baki yana dariya da zak'ozak'on hakwaran sa duk sun rine sunyi ja har wani dusa dusa suke yi da wani bak'i2 a tsakankanin hakwaran sa d'iff kamarfa an d'auke wuta haka farantin ya d'auke fuskan bokan.

ISMATWhere stories live. Discover now