*JAGORAN AHLUSSUNNAH*

203 5 1
                                    

𶠠Wallafar
Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto

*Fitowa ta 3*

*Ka’idojin Tafarkin Sunnah*

*Ka'ida ta Farko:*
Nassi a Shari’a abu biyu ne kadai: Abinda ya fito daga wurin Allah (Alkur’ani) da wanda ya fito daga wurin Manzonsa (Hadisi). Da su ake kafa hujja a addini. Kuma da su ake warware ko wace irin jayayya.
Kalmar Nassi a larabce tana nufin abinda aka daukaka shi, ko aka bayyana shi har ya fito fili aka san shi. Idan Malaman Shari’a suka ce an samu Nassi a cikin wata magana, suna nufin zancen Allah ko na Manzonsa. Domin su ne wadanda suke zama hujja a kan bayi, kuma da su ake raba duk wata gardama ko jayayya da ta shiga a tsakanin mutane. Allah _ta’ala_ yana cewa:
 “Ya ku wadanda suka yi imani! Ku yi da’a ga Allah, kuma ku yi da’a ga Manzo, da kuma majibintan al’amarinku. To, idan kun yi jayayya a wani abu to, ku mayar da shi zuwa ga Allah da Manzo in har kun kasance kuna yin imani da Allah da ranar lahira. Wannan shi ne alheri, kuma ya fi karshe mai kyau”. Suratun Nisa’: 59
A cikin wannan aya, Allah ya yi umurni da bin sa da kuma bin Manzonsa, sannan da bin Malamai majibinta al’amari ko kuma sarakuna masu gudanarwa da zartar da lamurran al’umma. Amma idan aka samu sabani ko jayayya sai Allah ya ce, a koma ga Nassi; maganar Allah kadai da ta Manzonsa, domin su ne wadanda ba a samun kuskure a cikin su. A cikin fassarar wannan aya Ibn Kathir _rahimahullah_ yake cewa:
Wannan umurni ne daga Allah mai girma da daukaka cewa, duk wani abinda mutane suka yi jayayya a cikin sa, na tushen addini ne ko na rassa (yana nufin a Akida ne ko a Sharia da hukunce hukunce) a mayar da shi ga littafin Allah da Sunnar Manzonsa, kamar yadda Allah ya ce: “Abinda duk kuka yi sabani a cikin sa ku mayar da hukuncin sa zuwa ga Allah” Suratus Shura: 10. Saboda haka, duk abinda littafin Allah da Sunnar Manzo suka yi hukunci kuma suka ba da shaidar ingancinsa to, gaskiya ne. Daga gaskiya kuwa babu komai sai bata! Don haka ne Allah Ta’ala ya ce, “Idan kun kasance kun yi imani da Allah da ranar lahira”. Yana nufin ku mayar da duk wata husuma da rashin sani zuwa ga littafin Allah da Sunnar Manzonsa, ku nemi hukunci a cikin su ga duk abinda ya shiga a tsakanin ku in dai har kun yi imani da Allah da ranar lahira. Wannan kuwa yana nuna cewa, duk wanda bai mayar da hukunci zuwa ga littafin Allah da Sunnar Manzo ba, kuma ba ya koma masu a irin wannan hali, to bai yi imani da Allah da ranar lahira ba.[i]
A nan yana da kyau mu fahimci wasu abubuwa kamar haka:
a)  Makasudin aiko Annabawa shi ne a yi masu da’a. Madaukakin Sarki ya ce:
 “Kuma ba mu aika da kowane Manzo ba sai kawai don ayi masa biyayya da izinin Allah” Suratun Nisa’i: 64
b) Bin Annabi bin Allah ne. Allah _tabaraka wa ta'ala_ ya ce:
 “Duk wanda ya bi Manzo to hakika Allah ne ya bi, wanda kuwa ya juya to, ba mu aiko ka don ka yi tsaro a kan su ba" Suratun Nisa’i: 80
A cikin Hadisi, Manzon Allah _sallallahu alaihi wasallam_ yana cewa: “Wanda ya yi min biyayya, to lallai Allah ne ya yi ma biyayya. Wanda kuwa ya saba mini to, Allah ne ya saba ma”.[ii]
A kan haka ne malamai suke ganin abin da ya zo a Hadisi kamar ya zo ne a cikin Alkur’ani; ba ya halalta sam mumini ya tsallake shi. Abdurrahman bn Yazid – daga cikin magabata na kwarai - ya ga wani Alhaji sanye da tufafin sa bayan ya yi haramar aikin Hajji, sai ya ce masa, ka cire tufafinka, ba a Hajji a sanye da dunkakkun tufafi. Sai Alhajin ya buda baki ya ce masa: Ba ni hujja daga cikin Alkur’ani! Nan take Abdurrahman ya karanta masa wannan aya[iii]:
 “Kuma abinda Manzo ya zo muku da shi to ku rike shi. Abinda kuwa ya hana ku sai ku hanu”. Suratul Hashri: 7
Shaihun Musulunci Ibnu Taimiyyah _rahimahullah_ yana cewa: Idan mutum zai saba wa mutanen duniya gaba daya amma ya bi Manzon Allah _sallallahu alaihi wasallam_  to, Allah ba zai tambaye shi don me ya saba wa mutane ba.[iv]
 
Manazarta:
[i] Tafsir Alkur’an Al-Azim, na Ibn Kathir (2/345-346)

[ii] Sahih Al-Bukhari (2967, 7137) da Sahih Muslim (1835).

[iii] Jami’ Bayan Al-Ilm wa Fadhlihi, na Alhafiz Ibn Abd al-Barr (Nassi mai lamba 2338).

[iv]  Majmu’ Al-Fatawa na Ibn Taimiyyah (16/529).

MATSALOLIN MA AURATAWhere stories live. Discover now