📚 Wallafar
Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto*Fitowa ta 4*
*Ka’ida ta Biyu:*
*Ijma’in Malamai hujja ne a Shari’a. Amma maganar daidaikun malamai ana kafa ma ta hujja ne, ba a kafa hujja da ita.*
Abinda ake nufi da Ijma’i shi ne, haduwar bakin Malaman Musulunci na duniya baki daya, a lokacin da ake iya tantance su, ma’ana lokacin Sahabbai. Idan duk Malaman al’umma suka hadu a kan wani hukunci na addini ba tare da sabani daga ko mutum daya ba, to wannan shi ake kira Ijma’i. Amma fa ba a iya samun Ijma’i a lokuta na baya baya, domin ba za a iya tantance ra’ayoyin Malamai ba bayan duniya ta fadada.
Idan aka samu Ijma’i a cikin wani hukunci, to shikenan ya zama hujja a addini. Domin wannan al’umma ba ta haduwa a kan bata gaba daya[i]. Wannan ya sa Allah ta’ala yake umurni a koma ga Nassi (Alkur’ani da Hadisi) idan aka samu sabani. A lokacin da babu sabani duk abinda Musulmi suke a kan sa daidai ne.
Ijma’i shi ne tafarkin muminai da Allah ya fadi a in da yake cewa:
وَمَنْ يُشَاقِقِ الرَّسُولَ مِنْ بَعْدِ مَا تَبَيَّنَ لَهُ الْهُدَى وَيَتَّبِعْ غَيْرَ سَبِيلِ الْمُؤْمِنِينَ نُوَلِّهِ مَا تَوَلَّى وَنُصْلِهِ جَهَنَّمَ وَسَاءَتْ مَصِيرًا
Ma’ana:
Kuma duk wanda ya saba ma Manzo bayan shiriya ta bayyana a gare shi, kuma ya bi wanin tafarkin muminai to, za mu jibinta masa abinda ya jibinta wa kansa, kuma mu kona shi da wutar Jahannama, kuma ta yi muni ta zama makoma. Suratun Nisa’: 115
Imam As-Shafi’i _rahimahullah_ ya kafa hujja da wannan aya a kan cewa, duk tafarkin da muminai suke a kai na wani hukunci ba tare da sabani a tsakanin su ba, wannan tafarki wajibi ne a bi shi.[ii]
Shaikhul Islam _rahimahullah_ yana cewa:
Isma, wadda take nufin “rashin yin kuskure” tana tabbata ne ga littafin Allah da Sunnar Manzonsa da abinda bayinsa Muminai suka hadu a kan sa. Wannan kam ba ya kasancewa sai gaskiya. Amma abin da Musulmi suka yi jayayya da sabani a cikin sa to, akan samu gaskiya a cikin sa kamar yadda ake iya samun kuskure a ciki.[iii]
Manzon Allah _sallallahu alaihi wasallam_ a hadisai masu tarin yawa ya yi umurni da lizimtar jama’a da rashin saba masu. Kamar hadisin da Bukhari da Muslim suka ruwaito in da yake cewa: “Babu wanda yake rabuwa da jama’a kuma ya mutu a haka sai ya yi mutuwar jahiliyya”.[iv] Da kuma hadisin Abu Dawud ingantacce wanda a cikin sa Annabi _sallallahu alaihi wasallam_ yake cewa: “Duk wanda ya rabu da jama’a daidai taka daya to, ya cire igiyar Musulunci daga wuyansa”.[v]
Imam Shafi’i _rahimahullah_ ya ce:
Manzon Allah _sallallahu alaihi wasallam_ ya yi umurni da lizimtar jama’ar Musulmi. Abinda ake hujja da shi kenan a kan cewa, bin ijma’in Musulmi ya zama tilas, in Allah ya so.[vi]
Babban malami Ibnu Kudama shi ma ya ce:
Wadannan hadisan an san su sarai tun zamanin Sahabbai da tabi’ai, kuma babu wani magabaci – ko dan baya - wanda ya taba ture su. Ko da kuwa ba su zama mutawatirai a daidaikunsu ba, amma a jumlace, sun amfanar da ilimi na tilas, kan cewa, Annabi _sallallahu alaihi wasallam_ ya girmama sha’anin wannan al’umma, kuma ya bayyana an tsare ta daga yin kuskure.[vii]
Wannan maganar duka tana da alaka ne da abinda Malamai cikarsu da batsewarsu suka hadu a kan sa. To, da zarar an samu sabani, maganar wani ba ta zama hujja a kan wani; sai dai a koma ga Nassi don tantance wanda ya fi kusa da gaskiya. Kamar yadda za mu yi magana a nan gaba, babu wanda maganarsa ba ta bukatar tantancewa in dai ba ma’asumi ba, wanda shi ne Annabi kadai, da Allah yake yi masa wahayin Shari’a.Manazarta
[i] Tirmidhi ya ruwaito wannan hadisi daga Ibnu Umar _radhiyallahu anhuma_. Duba: As-Sunan, na Tirmidhi (2167) kuma Sheikh Albani ya inganta shi. Haka ma Ibnu Abi Asim a cikin littafin As-Sunnah nasa daga sayyidina Anas bn Malik _radhiyallahu anhu_ daga Annabi _sallallahu alaihi wasallam_ cewa: “Hakika, Allah ya tsare al’ummata daga haduwa a kan bata”. Duba _Sahih Al-Jami’_ (1786).[ii] Duba: _Tafsir Al-Qur’an Al-Azim_, na Ibnu Kathir, (2/413). Duba kuma: _Majmu’ Al-Fatawa_ (19/177-178).
[iii] _Al-Jawab As-Sahih_ (4/333).
[iv] _Sahih Al-Bukhari_ (7143) da _Sahih Muslim_ (1849).
[v] _Sunan Abi Dawud_ (4758). Kuma Sheikh Albani ya inganta shi.
[vi] _Ar-Risalah_, na Imam Shafi’i, (1/403).
[vii] _Raudhat Al-Khatir Al-Atir Sharh Jannat An-Nazir wa Junnat Al-Munazir_, na Ibnu Qudama (1/387). Duba kuma: _Majmu’ Fatawa wa Rasa’il Al-Utahimin_,(11/63).
YOU ARE READING
MATSALOLIN MA AURATA
SpiritualKi samu sassaken biyayya ki hada da saiwar shagwaba da ganyen gaskiya da bawan San dangin sa da jijiyar Kula da mahaifiyar sa ki hada su a turmin nan mai suna hakuri ki samu tabaryarnan Mai Suna Iya Magana ki daka su insha Allah Zaki mallaki mijin k...