JAGORAN AHLUSSUNNAH

24 1 0
                                    

*JAGORAN AHLUSSUNNAH*
📚 Mansur Sokoto

*Majalisi na 16*

*Ka’ida ta Goma Sha Uku:*
*Maganar Allah, Annabi ne Yake Fassara ta*

Babu wata tantama cewa, Manzon Allah _sallallahu alaihi wasallam_ shi ya fi kowa sani da fahimtar sakon da Allah ya aiko shi da shi. Duk da irin sani da fahimtar da Sahabbai suke da ita game da harshen larabci amma akwai wurare da yawa da suka bukaci Annabi ya fassara masu abinda Allah yake nufi. Bugu da kari, wani lokaci magana takan zo a dunkule a cikin Alkur’ani, Manzon Allah ne yake fayyace ta[i]. Ko kuma ta zo a sake sai shi kuma ya dabaibaye ta[ii]. Ko a samu wani hukunci a Alkur’ani sai Sunnah ta yi kari a kan sa.[iii]Ko kuma ma Sunnah ta zo da wani hukunci sabo wanda babu shi sam a cikin Alkur’ani.[iv] Allah _subhanahu wa ta’ala_ yana cewa:
وَأَنْزَلْنَا إِلَيْكَ الذِّكْرَ لِتُبَيِّنَ لِلنَّاسِ مَا نُزِّلَ إِلَيْهِمْ وَلَعَلَّهُمْ يَتَفَكَّرُونَ
“Kuma mun saukar maka da Ambato ne domin ka yi ma mutane bayanin abinda aka saukar masu, ko da za su fadaka”. Suratun Nahl: 44
Kuma duk wani sabani a tsakanin jama’a shi ne Allah ya yarda ya warware shi. Buwayayyen Sarki ya ce:
وَمَا أَنْزَلْنَا عَلَيْكَ الْكِتَابَ إِلَّا لِتُبَيِّنَ لَهُمُ الَّذِي اخْتَلَفُوا فِيهِ وَهُدًى وَرَحْمَةً لِقَوْمٍ يُؤْمِنُونَ
“Kuma ba mu saukar maka da littafin ba sai domin ka yi ma su bayanin abinda suke sabani a cikin sa, kuma don ya zama shiriya da rahama ga mutane masu yin imani”. Suratun Nahl: 64
 
*Manazarta:*
[i] Kamar yadda Annabi _sallallahu alaihi wa sallam_ ya bayyana sifar Sallah da yadda ake fitar da Zakka da sifar aikin Hajji da sauran su.

[ii] Kamar yadda ya bayyana cewa, ana yanke hannun barawo ne daga wuyan hannu.  
Kuma ya bayyana wadanne watanni hudu ne Allah ya ce suna da alfarma.

[iii]  Kamar yadda ya kara cikin Muharramai (Matayen da Allah ya hana a aure su) sai ya kara a cikin su da cewa, “Ba a hada Macce da gwaggonta ko Innarta. Domin idan kuka yi haka za ku yanke zumuntarku”.

[iv]  Kamar yadda ya hana cin naman jakin gida kuma ya hana auren Mut’ah a ranar yakin Khaibar.

MATSALOLIN MA AURATAWhere stories live. Discover now