JAGORAN AHLUSSUNNAH

52 0 0
                                    

*JAGORAN AHLUSSUNNAH*
 
📚 Wallafar
Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto

*Fitowa ta 8*

*Ka’ida ta Shida:*
Addinin Allah Tsararre Ne; Alkur’ani da Sunnah. Kamar Yadda Wani Bai Iya Canja Alkur’ani Haka Sunnah Wani ba Zai Iya Gurbata ta ba.

Allah madaukakin Sarki ya yi alkawarin tsare addininsa da ya yi wahayin sa zuwa ga Annabi daga gurbata da canjawa.
Kada wani ya dauka cewa, Alkur’ani ne kadai Allah ya yi alkawarin tsarewa. Domin Madaukakin Sarki cewa ya yi: “Lallai, mu ne muka saukar da Zikiri, kuma lallai, mu ne masu kiyaye shi” Suratul Hijri: 9. Ka ga a nan, Zikirin da Allah ya saukar shi ya ce zai ba shi kariya. Masu ilimi kuwa duk sun sani idan aka ce haka, ba Alkur’ani kadai ake nufi ba. Domin ba shi kadai ne Allah ya saukar ba, har da Hikima; Hadisi kenan kamar yadda bayani ya gabata a ka’ida ta uku. Ba ka ga Allah subhanahu yana cewa ba:
وَأَنْزَلَ اللَّهُ عَلَيْكَ الْكِتَابَ وَالْحِكْمَةَ
  “Kuma Allah ya saukar maka da littafin (Alkur’ani) da Hikima (Sunnah)”. Suratun Nisa’: 113
Kuma Allah ya ce:
وَاذْكُرْنَ مَا يُتْلَى فِي بُيُوتِكُنَّ مِنْ آيَاتِ اللَّهِ وَالْحِكْمَةِ
“Kuma ku tuna abinda ake karantawa a cikin dakunanku na ayoyin Allah (Alkur’ani) da Hikima (Sunnah)” Suratul Ahzab: 34

Lallai kam an yi Annabawan karya masu da’awar an yi masu wahayi amma Allah ya tona asirinsu. Haka ne kuma aka samu zindikai masu fesa karya su jingina ta ga Annabi amma kuma sai Allah ya halicci zakakuran Malamai masana wadanda suke tona asirinsu, su bayyana karyarsu, su tankade su tace Sunnar Manzon Allahsallallahu alaihi wasallam. Ka yi tunani mana, idan Allah ya kiyaye Alkur’ani daga tozarta amma bai kiyaye Sunnah daga bacewa da gurbacewa ba, mene ne makomar Alkur’anin? A ina za a samu bayaninsa? Wa zai yi sharhi a kan sa? Ai shi ma sai samuwarsa da bacewarsa su zamo duk guda daya.[i]

Fitaccen malamin nan Ibnu Rajab rahimahullah yana cewa:
Haka ne Allah subhanahu ya tayar da wasu irin mutane wadanda suka tsayu a kan kariyar Sunnah, suka rarrabe gaskiya daga karya da kuskure da shirme, suka tantance ta iyakar tantancewa, suka kiyaye ta iyakar kiyayewa.[ii]

Daga cikin hanyoyin da Allah subhanahu ya tsare Sunnar Annabinsa da su, akwai:
1.      Sanya ma Sahabbai kaunar Hadisan Annabi, da ba su cikakkiyar kulawa ta yadda har wani yakan wakilta wani – idan zai je kasuwa – don ya sanar da shi idan Annabi sallallahu alaihi wasallam ya fadi wata Sunnah a lokacin ba shi nan.
2.      Sai kuma aka ba su karfin basira da kaifin harda, ta yadda duk abinda suka ji ko suka gani za su iya kiyaye shi da tantance shi da isar da shi ga jama’a duk sa’adda suka bukaci haka.
3.      Daga cikin su kuma aka samu masu rubutawa, kamar sayyidina Abdullahi bn Amr, wanda Abu Huraira rahimahullah ya ce, ya cire masa hula saboda shi yana rubuta abinda ya ji. A lokacin da shi kuma Abu Huraira yake hardace duk abinda ya ji albarkacin addu’ar Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam.
4.      Allah ya tsawaita rayuwar wasu kebantattu daga cikin Sahabbai wadanda suke da himma wajen karantar da mutane a garuruwan da Allah ya zaunar da su bayan sun bar birnin Madina. Kamar Ibnu Abbas da Nana Aisha a Makka, Ibnu Umar  Madina, Ibnu Mas’ud a Kufa, Muaz bn Jabal a Yaman da sauran su.
5.      Bayan wucewar Sahabbai kuma aka samu zakakurai daga cikin tabi’ai wadanda suka rika yawo gari gari suna tattara ilimin da Sahabbai suka watsa, suna karantar da mutane shi. Kamar su Sa’id bn Musayyib da Urwa a Madina, Ada’u bn Abi Rabah da Mujahid bn Jabr a Makka, Dawus bn Kaisan da Wahb bn Munabbih a Yaman, Abu Idris Al-Khaulani da Raja bn Haiwa a Sham, Abu Abdillah As-Sunabihi da Abu Tamim Al-Jaishani a Misra, Masruk da Alkama bn Kais a Kufa, Abu Sa’id Al-Basri da Abus Sha’sa’ a Basra. Akwai kuma wadanda suka zauna a Baghdad da Wasid da Khurasan da sauransu.
6.      Sai kuma aka rubuta Hadisai a cikin littafai, tun daga tattarawar da Ibnu Shihab Az-Zuhriy da Rabi’ bn Subaih da Sa’id bn Abi Aruba suka yi, har wallafe wallafen hadisai a garuruwa da suka biyo baya. Kamar littafin da Ibnu Juraij ya rubuta a Makka, da Muwaddar Malik a Madina, da littafin Auza’i a Sham, da na Sufyan As-Thauriy a Kufa, da na Hammad bn Salamah a Basra, na Ma’mar Al-Azdiy a Yaman, na Laith bn Sa’ad a Misra, da sauransu.
7.      Daga lokacin sarautar Harun Ar-Rashid aka samu karin ci gaba in da littafai suka dauki salo iri daban daban. Aka samu masu salon Muwadda da Musannaf da Musnad da Sunan da Juz’ da Jami’ da Mustadrik da Mustakhraj da Mu’ujam da Zawa’id da Adraf da sauransu.[iii]
8.      Kafin karni na uku ya zo karshe ilimin hadisi da dukan fannoninsa ya gama girkuwa. An kuma zayyana hanyoyin tantance gaskiya daga karya a cikin littafai masu yawa masu albarka. Fitattun malamai irin su Ahmad bn Hambal da Ishak bn Rahawaihi da Ali bn Al-Madini da Yahya bn Ma’in da Bukhari da Muslim da Abu Zur’ah Ar-Razi da Abu Hatim Ar-Razi da Abdullah bn Abdirrahman Ad-Darimi da Uthman bn Sa’id Ad-Darimi da sauransu sun gama fitar da ka’idoji wadanda ake rarrabe hadisai da su.
9.      An samu littafai wadanda suka tace hadisai suka wallafa ingantattu zalla, kamar Bukhari da Muslim da Ibnu Hibban da Ibnu Khuzaima. Sauran kuma an samu malamai sun bi diddiginsu sun tantance su. Ko a wannan zamani an yi ba da himma matuka a Jami’oin Musulunci daban daban wajen tahakiki da nazarin hadissan da suka zo a cikin littafan magabata. Ga kuma gagarumar hidimar da Sheikh Muhammad Nasiruddin Al-Albani; haifaffen Albeniya, dan kasar Siriya ya yi ma da yawan wadannan littafan. Sai kuma nasa da ya wallafa kamar Silsilatul Ahadis As-Sahiha, da Silsilatul Ahadis Ad-Dha’ifa da sauransu.
10. Akwai kuma sababbin hanyoyin zamani da aka yi amfani da su na tattara Sunnah da tantance ta:
   i.            Akwai shafukan yanar gizo masu dinbin yawa wadanda ke watsa hadisai da bayyana masu inganci da masu rauni. Jigajigan malaman hadisi na zamani ne suka kula da su.
   ii.            Akwai wasu shafukan a kafofin sa da zumunta da suke irin wannan aiki.
  iii.            Ka hada da tashoshin rediyo da talabijin masu kawo shiraruwa tare da malamai masana wannan fannin.
   iv.            Akwai Applications da Programs masu amfani a kan na’urori masu kwakwalwa da wayoyin tafi da gidanka.
  v.            Ga su CD da Memory masu saukin amfani.

A yau, babu wani hadisi da za kawo face a cikin sauki ana iya sanin matsayinsa da hukuncinsa ta hanyar maganganun malamai masanan hadisi - na da, da na yanzu - a kan sa. Ga saukin bincike, ga takaita lokaci, ga karancin kashe kudi, ga rashin wahala. A cikin aljihunka sai ka dauki littafai dubu ba tare da jin nauyinsu ko kadan ba.[iv]

Abu daya ne ya rage mu yi nuni zuwa gare shi a nan shi ne, kiyaye Sunnah ba ya nufin cewa, duk wata kalima wadda Ma’aki sallallahu alaihi wasallam ya furta sai ta iso gare mu ba. Wannan kuma ai ba zai yiwu ba. Abinda ake nufi shi ne, duk abinda ake bukatar sani game da rayuwarsa mai tsarki da ayyukansa masu albarka, tare da duk wani muhimmin abu da ya taba faruwa a lokacinsa wanda ya tofa albarkacin bakinsa a ciki, to, lallai ne al’umma ta samu labarinsu. Ba wai mutum daya shi kadai ya kewaye dukan wannan ba. Shi ma wannan ba shi yiwuwa. Amma abinda wani bai sani ba wani ya sani. Wanda ba a rubuta a wani littafi ba an rubuta a wani.
Imam As-Shafi’i rahimahullah ya ce:
"Harshen larabci yalwataccen harshe ne mai yawan kalmomi da lafuzza. Ba mu taba sanin wanda ya kewaye iliminsa kacokam ba, in dai ba shi Annabi ne ba. Amma kuma babu abinda ba a sani ba a cikinsa. Larabawa sun san shi gaba daya, kamar yadda Malamai suka san Sunnah. Ba mu san wani mutum shi kadai wanda ya kewaye sanin ta ba, ta yadda za ace babu abinda ya boyu gare shi a cikin ta. Amma idan aka tattara ilimin malamai gaba daya, babu wani Hadisin da ba za a samu ba. Amma idan aka raba, kowa zai tashi da wani kaso ne ban da wani."[v]
 
Manazarta
[i]  Don karin bayani duba: Al-Ihkam fi Usul Al-Ahkam, na Ibnu Hazm (1/95 da 115) da kuma As-Sawaik Al-Mursalah, na Ibn Al-Kayyim (2/371).

[ii]  Tafsir Ibn Rajab Al-Hambali, (1/605).

[iii] _Muwadda_: littafin
da ya tattara hadisai a tsarin baboba na fikihu kenan. Kuma ana shigar da har fatawoyin Sahabbai da tabi’ai da almajiransu a ciki, gami da wasu ruwayoyin tarihi da darajojin Sahabbai da sauransu. _Musannaf:_ Shi ma a kan jerin baboban Fikihu ake tsara shi. Ba shi da wani dogon bambanci da Muwadda. _Musnad:_ Ana jera shi a kan hadisan kowane Sahabi a babi daban ba tare da la’akari da fannin abinda suka kumsa ba. _Sunan_: Ana jera shi a kan baboban Fikihu amma ba a sanya fatawoyin Sahabbai sai nadiran. _Juz’i_ Yakan kunshi hadisan babi daya ne kacal. _Jami’_: Yakan kunshi hadisan Imani da na Fikihu da Tarihi da Tafsir da Falaloli da hadisan tashin kiyama da alamominta. Hadisan Annabi ne zalla a ciki. _Mustakhrij_: Littafi kamar na Bukhari sai wani malami ya zo ya fitar da hadisansa ta wasu hanyoyin na daban. _Mu’jam_: Akan jera hadisai a cikin san a Sahabbai daban, haka kuma na kowane malami ko kuma gari daban daban. _Zawa’id_: Sukan kunshi hadisai kari akan na wasu littafai da suka gabace su. _Adraf:_ Sukan jera farko farkon hadisai kamar yadda ake jera Kamus don saukin komwa gare su.

[iv]  Ya zama wajibi a nan mu yi nuni da cewa, tattare da alfanun wadannan hanyoyi na zamani ba kowa ne zai iya amfani da su yadda ya kamata ba. Akwai malamai na bogi, akwai shafuka na masu son zuciya, akwai wadanda ba a tantance bayanansu tsakani da Allah ba. Amma fa duk wanda yake da cancanta da kwarewa to, suna takaita masa wahala da lokaci matuka.

[v]  Ar-Risala, na Shafi’i, shafi na 42-43.

MATSALOLIN MA AURATAOnde histórias criam vida. Descubra agora