JAGORAN AHLUSSUNNAH*

31 1 0
                                    

📚 Dr. Mansur Sokoto
🌱💐🌱

*Majalisi na 25*
*Ka'ida ta Ashirin da Daya*
*Annabi sallallahu alaihi wasallam ya Bayyana ma Al'ummarsa Komai Game da Addininsa.*

Kamar yadda Alkur'ani ya tattara komai da komai na addini a jumlace, haka Sunnar Manzon Allah sallallahu alaihi wasallamta tattara su a fayyace ta yadda babu wani abu na Addini da Musulmi yake bukata don gyara lahirarsa face an bayyana masa shi.
Abu Zarr radhiyallahu anhuya ce:
Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam ya bar mu alhalin babu wani tsuntsu da yake jujjuya fukafukansa a sama face ya sanar da mu wani abu a kan sa. Kuma Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam ya ce: "Babu wani abin da ya rage wanda zai kusantar da ku zuwa ga aljanna ko ya nisantar da ku daga wuta sai da na fada maku shi.[i]
Wannan haka yake. Domin kuwa duk Annabawa ma an aiko su ne don su isar da sakon Allah zuwa ga mutane. To, ta ya ya kuma za su kasa bayyana wani abu har sai daga baya wani ya zo ya sanar da shi?! Alhalin kuma Allah Ta'ala yana cewa:
وَمَا أَرْسَلْنَا مِنْ رَسُولٍ إِلَّا بِلِسَانِ قَوْمِهِ لِيُبَيِّنَ لَهُمْ فَيُضِلُّ اللَّهُ مَنْ يَشَاءُ وَيَهْدِي مَنْ يَشَاءُ وَهُوَ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ
"Kuma ba mu aika wani Manzo ba face da irin harshen mutanensa domin ya yi ma su bayani, sai Allah ya batar da wanda ya so, ya shiryar da wanda ya so, kuma shi ne Buwayayye, Gwani". Suratu Ibrahim: 4
A wata ayar kuma Buwayayyen Sarkin yana cewa:
يَا أَيُّهَا الرَّسُولُ بَلِّغْ مَا أُنْزِلَ إِلَيْكَ مِنْ رَبِّكَ وَإِنْ لَمْ تَفْعَلْ فَمَا بَلَّغْتَ رِسَالَتَهُ
"Ya kai wannan Manzo! Ka isar da sakon abinda aka saukar zuwa gare ka daga wurin Ubangijinka. Idan har ba ka yi haka ba, to, ba ka isar da manzancinsa ba". Suratul Ma'ida: 67
Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam bai bar duniya ba har sai da Ubangijinsa ya tabbatar masa da cewa, ya kammala masa addini da ni'imarsa:
الْيَوْمَ أَكْمَلْتُ لَكُمْ دِينَكُمْ وَأَتْمَمْتُ عَلَيْكُمْ نِعْمَتِي وَرَضِيتُ لَكُمُ الْإِسْلَامَ دِينًا
"A yau, na kammala maku addininku, kuma na cika ni'imata a gare ku, kuma na yarda da Musulunci a matsayin addini a gare ku". Suratul Ma'ida: 3
Shi ma kuma Annabi da kansa abinda ya fadi ma Sahabbansa kenan sallallahu alaihi wasallam, ya ce: "Na bar ku a kan farin tafarki, wanda darensa da ranarsa duka daya ne. Babu wanda zai karkace daga gare shi a bayana sai halakakke".[ii]
Kenan, Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam bai bar wata kafa da wani zai zo ya ce yana da abin karantar da mu game da addini ba. Annabi _sallallahu alaihi wasallam_ kuma ba zai bayyano ma wani a cikin mafarki don ya karantar da shi wani abinda ya manta bai isar da sakon sa ba. Haka kuma, babu wani abu da ya rage na addini wanda ba a fada ma musulmi shi ba, balle a bukaci sake saukowar Jibrilu alaihis salam don ya sanar da shi ga wani daga cikin mutane. Duk wanda ya raya cewa, ya samu wani sabon karatu wanda Annabi sallallahu alaihi wasallam bai karantar da Sahabbansa shi ba, to, wannan karatun Shaidan ne. Allah ya kiyashe mu daga sharrin Shaidan.

*Manazarta:*
[i] Al-Musnad na Imam Ahmad (5/153, 162) da Silsila Sahiha na Albani (1803). Akwai kuma Hadisin Ibnu Mas'ud mai kama da wannan a cikin Al-Mustadrak na Hakim (2/4) da kuma cikin Silsila Sahiha (2866).

[ii] Duba: Al-Musnad na Imam Ahmad (4/126) da As-Sunan na Ibn Majah (43) da Almustadrak, na Hakim (302). Malamai da yawa suka inganta shi. Duba: Jami' Bayan Al-Ilm wa Fadhlih na Ibn Abdil Barr (2/348).

MATSALOLIN MA AURATAWhere stories live. Discover now