JAGORAN AHLUSSUNNAH

44 0 0
                                    

*JAGORAN AHLUSSUNNAH*
 
📚 Wallafar
Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto

*Majlisi na 9*

*Ka’ida ta Bakwai:*
*Allah Kadai Ake Bauta. Tafarkin Manzonsa Kadai Ake Biya*

Wannan ka’ida ita ce fassarar kalmar shahada. Abin nufi a nan, duk abinda ya danganci bauta kamar sujada da mika wuya da zuciya da tawakkali da neman biyan bukata, da rokon gafarar zunubai da neman tsari daga wuta da samun shiga aljanna to, hakkin Allah ne shi kadai ba shi da abokin tarayya a cikin su. Ba a kuma neman komai daga cikin wadancan abubuwa a wurin wani mahaluki, Mala’ika ne ko Annabi ko Waliyyi ko Shaihi ko wani na daban. Don sanin yadda ake bauta wa Allah kuwa, babu madogara sai karantarwar Annabi _sallallahu alaihi wasallam._
Kishiyar wannan Ka'ida ita ce Shirka da Bidi'a. Ahlus Sunnah ba su Shirka saboda ba su yarda su ba wani hakken Allah ba. Sannan ba su Bidi’a saboda ba su kaga ma kansu ibada sai dai su bi wadda ta zo daga Manzon Allah. Kuma wannan shi ke tabbatar da kalmar shahada.
Allah ta’ala  yana cewa:
وَمَا أُمِرُوا إِلَّا لِيَعْبُدُوا اللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ
“Ba a umurce su da komai ba face su bauta ma Allah, suna masu tsarkake masa addini” Suratul Bayyina: 5
Tsarkake ma Allah addini na nufin kadaita shi da shi, da rashin yi masa tarayya a bauta. A wajen sanin bautar da yadda Allah yake son ta sai dai abi karantarwar Manzon Allah _sallallahu alaihi wasallam_. Kamar yadda madaukakin Sarki ya ce:
قُلْ أَطِيعُوا اللَّهَ وَأَطِيعُوا الرَّسُولَ فَإِنْ تَوَلَّوْا فَإِنَّمَا عَلَيْهِ مَا حُمِّلَ وَعَلَيْكُمْ مَا حُمِّلْتُمْ وَإِنْ تُطِيعُوهُ تَهْتَدُوا وَمَا عَلَى الرَّسُولِ إِلَّا الْبَلَاغُ الْمُبِينُ
“Ka ce: ku bi Allah, kuma ku bi Manzo, to, idan kuka juya to, kawai abinda aka dora masa ne a kan sa, kuma abinda aka dora maku ne a kan ku, kuma idan kun bi shi za ku shiriya, kuma babu abinda yake a kan Manzo sai isarwa bayyananniya”. Suratun Nur: 54

MATSALOLIN MA AURATAWhere stories live. Discover now