📚 Wallafar
Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto*Fitowa ta 2*
*Ma’anar Sunnah*
A larabce, Sunnah tana nufin hanya, tafarki, ko kuma wani tsari wanda ake bi, mai kyau ne ko maras kyau.[Mujmal Al-Lugah, na Ibnu Faris, tahakikin Zuhair Abdulmuhsin Sultan, bugun farko, na Mu'assasat Ar-Risala, Beirut, Lebanon, 1404H, (2/455) da kuma Lisan Al-Arab na Ifriqi (13/225)]. Amma idan ka je wurin Malaman addini, to a ko wane fanni akwai abin da suke ce ma Sunnah. Duk da yake asalin ma’anar bai saba ba.
A wurin malaman Hadisi, Sunnah ita ce, “Duk abin da aka jingina shi ga Annabi _sallallahu alaihi wasallam_ na zance, ko aiki, ko tabbatarwa, ko kuma wata siffa ta jiki ko ta halitta”. Duk irin wadannan idan aka jingina su ga Annabi _sallallahu alaihi wasallam_ malaman Hadisi na kiran su Sunnah, ko da kuwa hakan ya kasance kafin lokacin da aka ba shi manzanci ne. A yayin da malaman Usulul Fiqhi sukan kira Sunnah “Duk hukuncin da aka samo daga Annabi _sallallahu alaihi wasallam_ in dai ba a cikin Alqur’ani yake ba”. Malaman Fiqihu su kuma, abinda suke ce ma Sunnah shi ne: “Duk abin da Shari’a ta ce ayi shi amma ba ta wajabta ko ta tilasta ba”. Irin wadannan abubuwan ne ake cewa, yin su na da lada, amma barin su ba shi da zunubi.[As-Sunnah wa makanatuha fi At-Tashree' Al-Islami, na Dr. Mustafa As-Siba'ee, bugu na biyu ma Al-Maktab Al-Islami, Beirut, Lebanon, 1396H, shafi na 47-48 da Qawa'id At-Tahdeeth, na Jamal Ad-din Al-Qasimi, shafi na 64 da kuma Al-Hadith wa Al-Muhaddithun, na Sheikh Abu Zuhra, shafi na 9]
Wadannan fassarori duka an yi su ne bayan an girka wadannan ilmoman har sun tsayu da kafafunsu. Amma idan muka koma baya da nisa, za mu ga magabatan al’umma wato Salaf suna cewa,“Abin da duk ya dace da littafin Allah da koyarwar Manzon Allah _sallallahu alaihi wasallam_ shi ne Sunnah”. Abin da ya saba ma dayan su shi ne Bidi’a.[Al-Muwafaqat fi Usul As-Shari'ah, nq Abu Ishaq As-Shatibi, sharhin Abdallah Darraz, watsawar Dar Al-Ma'rifa, Beirut, Lebanon, (4/3-6)]. Daga nan ne za ka ji sun ce, wane yana a kan Sunnah, ma’ana yana tafiya bisa tafarkin Qur’ani da Hadisi, wane kuma yana kan Bidi’a, ma’ana ya bi wani sabon tafarki ba na Qur’ani da Hadisi ba. Wani lokaci ma sukan ce mutum yana kan Sunnah idan ya bi tafarkin Sahabban Annabi _sallallahu alaihi wasallam_ wajen akidarsa da kuma wajen ibadarsa, domin tafarkinsu shi ne Qur’ani da Hadisi. Amma sun fi wasafta mutum da cewa yana a kan Sunnah idan akidarsa ta dace da ta Sahabban Manzon Allah _sallallahu alaihi wasallam_ musamman a lokacin da wasu akidoji suka bayyana wadanda suke baki ne a cikin Musulunci.[Wasatiyyat Ahl As-Sunnah bain Al-Firaq, na Dr. Muhammad Ba Karim Muhammad Ba Abdallah, bugun Maktabat Al-Ulum wa Al-Hikam, Madina, Saudi Arabia, shafi na 26-29].
KAMU SEDANG MEMBACA
MATSALOLIN MA AURATA
SpiritualKi samu sassaken biyayya ki hada da saiwar shagwaba da ganyen gaskiya da bawan San dangin sa da jijiyar Kula da mahaifiyar sa ki hada su a turmin nan mai suna hakuri ki samu tabaryarnan Mai Suna Iya Magana ki daka su insha Allah Zaki mallaki mijin k...