JAGORAN AHLUSSUNNAH

31 1 0
                                    

*JAGORAN AHLUSSUNNAH*
 
📚 Wallafar
Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto

*Fitowa ta 13*

Ka’ida ta Goma:
Idan Hadisi ya Inganta ba a Watsi da Shi, Domin Maruwaitansa Masu Gaskiya ne. Mai Gaskiya Kuwa ba a Karyata Shi.
Hadisi ingantacce shi ne wanda ya cika duk sharudan da Malamai suka gindaya domin karbar sa. Sharudan kuwa sun hada da: Gaskiyar maruwaitansa gaba dayansu, da samun tabbacin iya kiyayewar kowanen su ga Hadisin ta hanyar rubuta shi ko hardace shi, da kuma samun tabbacin kowannen su a wurin Malaminsa ya jiyo shi kai tsaye, ba tare da an samu wata tangarda ko saba ma juna a riwayarsu ba. Hadisi kuwa kafin ya cika wadannan sharuda dole ne sai Malamai sun tantance komai da ya danganci wadanda suka karbo shi, da yanayin da suka karbo shi, da ma yanayin da suka isar da shi ga almajiransu har zuwa lokacin da aka rubuta shi ya tabbata a cikin littafai. Haka kuma kafin su yanke masa hukunci sai sun tattara hanyoyin da ya zo cikin su a garuruwa daban daban da lafazin da kowane mai ruwaya ya yi amfani da shi. Idan aka samu sabani a tsakanin su sai a rinjayar da wanda alamomi suka nuna ya fi inganci don yawan wadanda suka ruwaito shi ko karfin amincin da ake da shi a gare su.
A dalilin tantance Hadisi kwaya daya rak, don tabbata ya tsallake wadannan sharudan, Malamai sun sha yin tafiyayya zuwa garuruwa masu nisa don ji da kunnuwansu, musamman idan aka samu wani dan shakku. Al-Khadib Al-Baghdadi ya wallafa littafi na musamman a kan haka, wanda ya kawo labarai masu yawa na malaman da suka yi irin wannan tattakin, cikin su har da ta babban malamin birnin Basra Shu’uba bn Al-Hajjaj wanda ya yi tafiya ta watanni da dama don ya tantance Hadisin Ukbatu bn Amir wanda ya riwaito akan falalar alwala.[i] A cikin littafin, malamin ya jero sunaye da labarin Malaman da suka tafi aikin Hajji don kawai su hadu da Malamai su tantance Hadisai. Ya kuma kulla babi na musamman a kan wadanda suka dukufa don cim ma irin wannan manufa har ajalinsu ya cim ma su kafin su samu biyan bukatarsu.[ii]
Duk wanda ya bibiya irin tsauraran matakan da Malaman Hadisi suka rika dauka kafin yanke ma Hadisi hukunci kafin a karbe shi ko a ki karbar shi, ba zai yi shakka ba cewa, wannan hikima ce ta Allah da ya samar da ita don kariyar karantarwar Manzonsa. Haka kuma ba zai yi shakku game da Hadisin da suka ce a karba lallai ya kamata a karbe shi ba. Kai, ya ma zama wajibi a karbe shi din. Domin idan ba a karbi Hadisan da suka inganta ba, babu wata hujja ko wani hanzari da za a iya gabatarwa.
Bisa ga haka, duk wanda yake iya karfin halin da zai karyata Hadisi ingantacce, ba za ayi mamaki ba in da ya ji shi da kunnensa daga Manzon Allahsallallahu alaihi wasallam ya ki karbar sa. Yin haka kuwa sanannen tafarki ne a gurin ‘yan Bidi’a masu bin son zuciya. Suna adawa da Hadisai ingantattu saboda su, suna shimfida ra’ayoyinsu ne da soye soyen zukatansu, malaman Sunnah kuma suna yi masu raddi da ingantattun Hadisan. Kamar yadda Amru bn Ubaid – daya daga cikin jigajigan Mu’utazila – ya fada lokacin da aka ruwaito masa Hadisin Imam Al-A’mash wanda ya ruwaito daga Zaid bn Wahab, shi kuma daga Abdullahi bn Mas’ud radhiyallahu anhudaga Annabi sallallahu alaihi wasallam mai gaskiya abin gaskatawa, cewa: “Lallai dayanku ana hada halittarsa a cikin cikin mahaifiyarsa yana a matsayin digon maniyyi kwana arba’in..” har zuwa karshen Hadisin. Wannan Hadisi kuwa a takaitacciyar fahimtar Mu’utazila ya kunshi jingina zalunci ga Allah, domin ya nuna Allah zai iya rusa aikin alherin da mutum ya yi a karshen rayuwarsa don kawai ya kaddara masa shiga wuta, sai ya tilasta shi yin aikin ‘yan wuta don ya jefa shi a cikin ta. Bisa ga haka, Amru bn Ubaid ya fusata da ya ji Hadisin. A cikin rashin ladabi ya ce, “In da na ji shi da kunnena daga A’mash da na karyata shi. Kuma da na ji shi daga Zaid bn Wahab da ba zan gaskata shi ba. Haka ma da na ji shi daga Ibnu Mas’ud ba zan karbe shi ba. Da ma na ji shi a wurin Manzon Allah zan mayar da shi. Kuma in da zan ji shi daga Allah kai tsaye zan ce masa, ba haka muka yi alkawari da kai ba”.[iii]
Wannan maganar ta Amru bn Ubaid tana kwatanta irin rashin kunyar da Malaman Sunnah suka rika fuskanta daga ma’abuta Bidi’a a tsawon zamani wajen karyata Hadisan Manzon Allah sallallahu alaihi wasallamdon kawai hankulansu sun kasa kama tasharsu. Kai, ba hadisai kadai ba, har da wasu ayoyin Alkur’ani Mu’utazila suke kushewa a kan sun saba ma hankulansu. Shi dai wancan Amr bn Ubaid da muka fadi a baya – daga cikin jigajigan Mu’utazila ai ya musanta Surar Tabbat yada..ya ce, in dai har a cikin Alkur’ani take, to Allah bai da wata hujja a kan bil adama. Yana nufin cewa, Allah shi ya kaddara ma Abu Lahabi yin kafirci kuma ya zarge shi a kan sa, ya ce zai shigar da shi wuta. Muna neman tsarin Allah daga bata da aikin Shaidan.[iv]
To, ko ya ya Ahlus Sunnah suka fahimci Hadisin wanda ya inganta babu tantama daga Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam?
Ahlus Sunnah a irin wannan Hadisi da ma dukkan Hadisai sukan kwantar da hankalinsu ne su fahimci mene ne manufar Annabi sallallahu alaihi wasallamda ya fadi wannan magana? Don gano manufarsa ta hakikani kuwa sukan bibiyi ruwayoyin Hadisin yadda ya zo da lafuzan Malamai daban daban na garuruwa daban daban. A garin binciken wannan Hadisi kuwa, sai aka samu riwayar Imam Ahmad bn Hambal a cikin Al-Musnad nasa wadda ta kawar da shubhar da su Amru suka fahimta a cikin Hadisin. Imam Ahmad ya ruwaito shi da lafazi kamar haka:
"إن أحدكم ليعمل بعمل أهل الجنة فيما يبدو للناسحتى ما يكون بينه وبينها إلا ذراع فيسبق عليه الكتاب فيعمل بعمل أهل النار فيدخلها. وإن أحدكم ليعمل بعمل أهل النار فيما يبدو للناس حتى ما يكون بينه وبينها إلا ذراع فيسبق عليه الكتاب فيعمل بعمل أهل الجنة فيدخلها"
Ma’ana:
“Hakika, dayanku yakan rika yin aiki irin na ‘yan aljanna a ganin idon mutane, har sai ya kasance babu abinda ke tsakanin sa da ita sai kamu daya. Ana haka sai littafin kaddara ya rinjaye shi, sai ya yi aikin ‘yan wuta, sai ya shige ta. Kuma hakika, dayanku yakan rika yin aiki irin na ‘yan wuta a ganin idon mutane, har sai ya kasance babu abinda ke tsakanin sa da ita sai kamu daya. Ana haka sai littafin kaddara ya rinjaye shi, sai ya yi aikin ‘yan aljanna, sai ya shige ta”.
A nan zamu lura da kalmar “a ganin idon mutane” wanda ya nuna mai aikin ‘yan aljannar riya ce yake yi ba aikin kwarai ne tun farko yake yi ba. Don haka, Allah zai hana shi cikawa a kan wannan aikin tun da ba da niyyar neman yardar Allah yake yi ba. Shi kuma mai yin aikin ‘yan wutar a ganin idon mutane ne. Amma a tsakanin sa da Allah yana da-na-sani da jin zafin abinda yake aikatawa. Don haka, sai Allah ya yi masa rahama ya karbi tubansa tun da daman da-na-sani shi ne tuba. Sai Allah ya yi masa kyakkyawan karshe ya cika da aikin kwarai ya shiga aljanna. Ya Allah! Ka yi mana rabo kyakkyawa.
Wannan kyakkyawan misali ne a kan yadda Malaman Sunnah suke natsuwa idan Hadisi ya zo da wani abu da yake girgiza tunaninsu, a cikin ladabi da tsanaki sai Allah ya ganar da su bakin zarensa. A yayin da ‘yan Bidi’a nan take suke watsi da Hadisin kafin su gama fahimtar sa, sai su wurga shi Bola. Muna neman tsarin Allah daga bin son zuciya.
 
Manazarta
[i]  Ar-Rihlah fi Dalab Al-Hadith, na Khatib Al-Baghdadhi (shafi na 138).

[ii]  Duba littafin da ya gabata (Shafi na 166).

[iii] Siyar A’lam An-Nubala’ na Dhahabi, (6/104-105).

[iv] Duba littafin da ya gabata a sama.

MATSALOLIN MA AURATAWhere stories live. Discover now