JAGORAN AHLUSSUNNAH

119 3 1
                                    

*JAGORAN AHLUSSUNNAH*
 
📚 Wallafar
Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto

*Fitowa ta 5*

*Ka’ida ta Uku:*
*Alkur’ani da Sunnah Duk Daga Allah ne. Kuma Matsayinsu daya ne:*

Babu shakka cewa, Alkur’ani ta fuskar falala da matsayi, kasancewar sa maganar Allah kai tsaye, shi ke da matsayin daraja ta farko a cikin Nassoshin Shari’a. Haka ma ta fuskar duba ga hanyoyin da muka same su. Alkur’ani ya fi yawan adadin maruwaita fiye da Sunnah. Amma ta fuskar tsayar da hujja da ba da hanzari, da wajabta wani abu a kan Musulmi ko haramta shi ko fitar da kowace irin doka, Alkur’ani da Sunnah duk abu daya ne. Domin dukan su daga wajen Allah su ke. Manzon Allah – Amincin Allah ya tabbata a gare shi - babu komai nasa a ciki sai wanda aka umurce shi. Allah Ta’alaya ce:
وَمَا يَنْطِقُ عَنِ الْهَوَى * إِنْ هُوَ إِلَّا وَحْيٌ يُوحَى
*“Kuma shi (Manzo) ba ya furuci da son zuciya. Shi dai (abinda yake fadi) kawai wahayi ne da ake yi masa shi (daga wurin Ubangijinsa)”.* Suratun Najm: 3-4
Kuma Allah ya ce, ya fadi:
إِنْ أَتَّبِعُ إِلَّا مَا يُوحَى إلَيّ
*“Ni, ina bin kawai abinda aka yi mini wahayinsa ne”.* Suratul An’am: 50, Suratu Yunus: 15 da Suratul Ahkaf: 9
Allah _subhanahu_ ya kara cewa:
وَأَنْزَلَ اللَّهُ عَلَيْكَ الْكِتَابَ وَالْحِكْمَةَ وَعَلَّمَكَ مَا لَمْ تَكُنْ تَعْلَمُ وَكَانَ فَضْلُ اللَّهِ عَلَيْكَ عَظِيمًا
*"Kuma Allah ya saukar maka da littafin (Alkur’ani) da Hikima (Sunnah) kuma ya sanar da kai abinda ba ka sani ba, kuma falalar Allah a gare ka ta kasance mai girma”.*
Bisa ga haka ne, Manzo _sallallahu alaihi wasallam_ ya tsoratar daga bambanta Alkur’ani da Sunnarsa. Yake cewa: _*Hakika, an ba ni Alkur’ani, da wani irinsa a tare da shi. Nan gaba kadan za a samu wani mutum da zai ci abinci ya yi tatil, yana kishingide a kan gadonsa, ya rika ce wa mutane: “Ku rike Alkur’anin nan shi kadai ya ishe ku. Idan kun ga abu halas ne a cikin sa sai ku halasta shi. Idan kuma kun ga wani abu haram ne a cikin sa sai ku haramta shi”. To, ku saurara! Duk abinda Manzon Allah ya haramta kamar wanda Allah ya haramta ne”*_.[i]
Na’am. Alkur’ani da Sunnah abu daya ne; babu bambanci. Domin Allah _subhanahu_ ya hana a bambanta shi da Manzanninsa, in da ya ce:
إِنَّ الَّذِينَ يَكْفُرُونَ بِاللَّهِ وَرُسُلِهِ وَيُرِيدُونَ أَنْ يُفَرِّقُوا بَيْنَ اللَّهِ وَرُسُلِهِ وَيَقُولُونَ نُؤْمِنُ بِبَعْضٍ وَنَكْفُرُ بِبَعْضٍ وَيُرِيدُونَ أَنْ يَتَّخِذُوا بَيْنَ ذَلِكَ سَبِيلًا * أُولَئِكَ هُمُ الْكَافِرُونَ حَقًّا وَأَعْتَدْنَا لِلْكَافِرِينَ عَذَابًا مُهِينًا * وَالَّذِينَ آمَنُوا بِاللَّهِ وَرُسُلِهِ وَلَمْ يُفَرِّقُوا بَيْنَ أَحَدٍ مِنْهُمْ أُولَئِكَ سَوْفَ يُؤْتِيهِمْ أُجُورَهُمْ وَكَانَ اللَّهُ غَفُورًا رَحِيمًا
*“Hakika, wadanda suke kafirce ma Allah da Manzo, kuma suna son su bambanta tsakanin Allah da Manzanninsa, kuma suna cewa, mun yi imani da sashe mun kafirce ma sashe, kuma suna son su riki wata hanya a tsakanin wannan. Wadancan su ne kafirai tsantsa, kuma mun yi tanadin azaba mai wulakantarwa ga kafirai. Wadanda kuma suka yi imani da Allah da Manzanninsa, kuma ba su bambance tsakanin wani da wani a cikin su ba, wadannan da sannu za mu ba su ladarsu, kuma Allah ya kasance Mai gafara, mai jinkai”*. Suratun Nisa’: 150-152
A kan haka ne, Sheikh Muhammad bn Salih Al-Uthaimin _rahimahullah_ yake cewa: Wadanda suke musanta Sunnah suna musanta Alkur’ani ne. Domin Sunnah mai kammala Alkur’ani ce. Sai fa idan ba ta inganta ba, wannan kam wani abu ne daban. Amma idan ta inganta to, daidai take da Alkur’ani.[ii]
 
*Manazarta:*
[i] _Al-Musnad_ na Imam Ahmad (4/ 131, 132), _Sunan Abi Dawud_ (4604), _Sunan At-Tirmidhi_ (2664) da _Sunan Ibn Majah_(12).

[ii] _Sharh Sahih Al-Bukhari_ na Uthaimin(8/160).

MATSALOLIN MA AURATADonde viven las historias. Descúbrelo ahora