* JAGORAN AHALUSSUNNAH *
📚 Mansur Sokoto
*Majalisi na 14*
*Ka’ida ta Goma Sha Daya:*
*Babu Bukatar sai Hadisi ya Zama Mutawatiri Sannan Ayi Aiki da Shi:*Mutawatiri shi ne Hadisin da mutane masu dinbin yawa suka ruwaito shi daga wasu masu yawa irin su, har karshensa, kuma suka ba da labarin abinda suka ji ko suka gani, ta yadda a hankalce ba zai yiwu labarinsu ya zama karya ko kuskure ba. Idan Hadisi ya cika wannan sharadi to, ya kai kololuwar inganci. Amma fa ba sharadi ne sai kowane Hadisi ya zama haka ba sannan a karbe shi, a Akida ne ko a hukunce hukuncen Shari’a. Annabin da aka aiko mana ma mutum daya ne. Kuma akasarin wadanda ya aike su zuwa birane domin su karantar da mutane Addini daidaiku ne. Idan aka ce hujjar Ubangiji ba ta tsayuwa akan mutane sai ta zo ta hanyar Tawaturi to an yi jifa da kaso mafi girma na addini.
Babu shakka, Alkur’ani ya zo ne ta irin wannan hanya ta Tawaturi, domin kuwa ba a san iyakar adadin wadanda suka dauko shi daga Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam ba. Haka su ma wadanda suka dauko shi daga almajiransa; Sahabbai. Su ma ibadoji na aikace kamar Sallah da yadda ake yin ta, mafi yawa ta irin wannan hanya aka same su. Amma sauran bayanan addini ta daidaikun malamai suka iso mana, kuma babu wani mai hankali da yake cewa, idan mutum daya mai gaskiya, amintacce ya ba da karatu kada a dauka ko kuma kada ayi aiki da shi.
Hadisin da bai kai matsayin Mutawatiri ba shi ake kira Ahad; ma’ana Hadisin daidaiku. Kuma malaman Sunnah sun hadu a kan cewa, matukar ya inganta wajibi ne ayi aiki da shi. Wannan abu ne da babu kokwanto ko sabani dangane da shi a tsakanin Malamai. Maganar Mutawatiri ita kanta magana ce da aka soma yin ta daga baya, bayan shudewar Sahabbai. Amma a zamaninsu duk amintaccen mutum idan ya fadi magana ana gaskata shi.
Misalin wannan shi ne lokacin da annoba ta faru a birnin Sham alhalin Sahabbai masu dinbin yawa suna kan hanyar zuwa can a karkashin jagorancin Sarkin Musulmi sayyidina Umar Radhiyallahu Anhu, sai ya shawarci jama’a cikin su har da Malaman Muhajiruna da Ansar amma babu wanda yake da Nassi daga Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam a kan mas’alar. Don haka sai ra’ayinsu ya bambanta; wasu suka ce aje, wasu suka ce a koma. Sayyidina Umar ya bi ra’ayin wadanda suka ce a koma. Sai wani ya ce masa, za mu yi gudun kaddarar Allah ne? Ya ce, eh, za mu guji wata kaddarar Allah ne zuwa wata. Bayan haka ne sai Abdurrahman bn Auf ya zo daga wurin wata bukatarsa ya tarar da abin da ake ciki, sai ya ce, ai kuwa ni ina da wani ilimi a cikin wannan mas’ala. Domin na ji Manzon Allahsallallahu alaihi wasallamyana cewa: “Idan kuka ji labarin faruwar annoba a wani gari kada ku shiga wannan garin. Idan kuma ta faru kuna a cikin garin kada ku fice don gudun ta”.[i]
Ka ga duk yawan Sahabban nan babu wanda ya ji wannan Hadisi amma da suka ji shi daga mutum daya amintacce sai suka gaskata shi, ba su ce sai an samu jama’a masu yawa sun ruwaito shi ya zama Mutawatiri ba.*Manazarta:*
[i] Sahih Al-Bukhari (5729) da Sahih Muslim (2219).
![](https://img.wattpad.com/cover/191725293-288-k255555.jpg)
YOU ARE READING
MATSALOLIN MA AURATA
SpiritualKi samu sassaken biyayya ki hada da saiwar shagwaba da ganyen gaskiya da bawan San dangin sa da jijiyar Kula da mahaifiyar sa ki hada su a turmin nan mai suna hakuri ki samu tabaryarnan Mai Suna Iya Magana ki daka su insha Allah Zaki mallaki mijin k...