JAGORAN AHLUSSUNNAH

65 1 1
                                    

*JAGORAN AHLUSSUNNAH*
 
📚 Wallafar
Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto

*Fitowa ta 7*

*Ka’ida ta Biyar:*
*Ba a Zubar da Kimar Malami Domin Ya yi Kuskure, Sai Dai Idan ya Bi Son Zuciya*

Mutum duk dan tara ne. Babu wanda ya cika goma sai Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam. Shi kadai ne ma’asumi wanda babu kuskure a cikin karantarwarsa. Don haka ne ma Allah Ta’ala ya kafa mana hujja da shi yana cewa:
فَإِنْ تَنَازَعْتُمْ فِي شَيْءٍ فَرُدُّوهُ إِلَى اللَّهِ وَالرَّسُولِ إِنْ كُنْتُمْ تُؤْمِنُونَ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ
“To, idan kun yi jayayya a wani abu sai ku mayar da shi zuwa ga Allah da Manzo in har kun kasance kuna yin imani da Allah da ranar lahira”. Suratun Nisa’: 59
In da kuwa hukuncin Manzo na iya zama kuskure, da Allah bai sanya shi ya zama hujja ba. Haka kuma da akwai wani wanda ba ya kuskure a cikin hukuncinsa ban da shi, da Allah ya shigar da shi a cikin masu warware jayayya.
Bisa ga haka, babu wani malami wanda zancensa yake abin karba ne dukansa, ko kuma hukuncinsa yake abin sallamawa gaba dayansa sai Manzon Allah. Haka babu wata mazhaba wadda duk hukuncin da ta yanke babu gyara a cikin sa. Maganar kowa dole ne sai an auna ta ga sikelin maganar Manzon Allah. Idan ta yi daidai shikenan. Idan ba ta yi daidai ba a ajiye ta a dauki ta Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam.
Tutiya da mazhaba don kauce ma Sunnah, dadaddiyar magana ce. Imam Ad-Dhahabi ya ce, mun ji wani mutum yana cewa: “Shugaban Mazhaba kamar Manzon Allah ne ga wanda ya lazimci mazhabarsa. Ba ya halalta a saba masa”. Shaihin Malamin ya ce, sai na ce:
Wannan zance ne kawai. Kuma an gina shi ba bisa ga ilimi ba. Ina! Kwarai ya halalta mutum ya bar shugaban mazhabarsa ya koma ga wani matukar ya ga hujjar wannan ta fi karfi a wata mas’ala. Kai, ba wannan kadai ba fa. Bin Nassi shi ne wajibi a duk inda aka san shi. Amma ba muna nufin yadda wasu mutane suke yi ba, wadanda suke tsittsintar kawai abinda suke jin dadin sa da sha’awarsa a duk mazhabar da suka same shi. Duk wanda ya bibiyi sassaucin wasu malamai kawai don ya more, ya rika tsintar kurakuran masana to, addininsa zai sassafce. Kamar yadda Imam Al-Auza’i ya ce: Wanda ya bi mazhabar wasu mutanen Makka a kan halasta auren mut’ah, ya hada da mazhabar wasu na Kufa a kan halasta shan tsimen alkama (Burkutu), tare kuma da mazhabar wasu ‘yan Madina masu halasta kade kade, sannan ya goyu bayan wasu mutanen Sham masu cewa, sarakunan Musulunci ma’asumai ne.. to, wannan ya hada hancin sharri wuri daya. Irin wannan ne kuma za ka same shi yana bin ‘yan dabaru wajen halasta kudi da ruwa. Idan kuma aka zo wajen aure da saki da sauran su sai ya zabi mazhabi mafi sassafci. Duk wanda yake yin haka addininsa ya gama lalacewa.[i]
Bisa ga wannan ka’ida, Malamai sun bayyana cewa, komai darajar Malami akwai bukatar a rika auna maganarsa da ta Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam, kuma duk in da ta saba ya zama wajibi a bar ta, ba tare da yin suka ga shi wanda ya fade ta ba. Kamar yadda suka yi ittifaki a bar fatawar sayyidina Abu Dalha Al-Ansary radhiyallahu anhu wanda ya yi fatawar cewa hadiye kankara ba ya karye azumi, saboda ba abinci ba ce, ba kuma abin sha ba, a fahimtarsa.[ii] Da fatawar babban Malamin Makka Ada’u bn Rabah cewa, matafiyi zai fara kasaru tun daga gidansa idan ya yi niyyar tafiya.[iii] Da ire iren wadannan.
Wannan kuwa ba suka ce ga malamin da ya yi kuskure aka bar shi da kuskurensa ba. Shaihun Musulunci yana cewa:
“Da an kaddara wani malami mai fatawowi da yawa ya yi kuskure dari daya bai zama aibi ba”.[iv]
Shamsuddin Az-Zahabi rahimahullah yana cewa:
Da ace duk wanda ya yi kuskure a Ijtihadinsa tare da ingancin imaninsa da kokarin biyar sa ga gaskiya, sai mu yi watsi da shi saboda kuskurensa, da babu wani shugaba ko jagora a addini da zai yi saura a tare da mu. Allah dai ya jikan su baki daya don baiwarsa da karimcinsa.[v]
Shaihin Musulunci shi ma yana cewa:
Da yawa daga cikin mujtahidai na Salaf da na bayansu sun fadi wata magana ko sun aikata wani aiki wanda a hakikaninsa bidi’a ne, amma ba su san cewa bidi’ar ne ba. Ko dai saboda wasu hadisai masu rauni da suka zaci cewa ingantattu ne, ko kuma saboda wasu ayoyi da suka fahimce su ba a yadda suke ba, ko kuma don wani ra’ayi da suka bi alhalin akwai nassin da ya saba masa wanda su ba su gan shi ba. To, - a irin wannan hali - idan har mutum ya ji tsoron Ubangijinsa gwargwadon iko, lallai zai shiga cikin wadanda Allah subhanahu ya ce: “Ya Ubangiji kada ka kama mu idan muka yi mantuwa ko muka yi kuskure” Suratul Bakara: 286. Kuma a ingantanccen hadisi Allah ya ce, na karbi wannan addu’a.[vi]
Makasudin abinda ya kamata a sani shine, ba a ture malami saboda ya yi kuskure ko kurakurai sai idan ya saki tafarkin Sunnah ga baki daya ya kama wani tafarki na daban. Maimakon haka, sai ayi masa uzuri a roka masa gafarar Allah. Amma idan malami ya saki tafarkin ya kama son zuciyarsa, ya yi fatali da ayoyin Allah ko hadisan Manzon Allah, a nan kam za a kyamace shi, kuma a tsoratar da mutane daga bin sawunsa. Allah ya shiryar da mu zuwa ga tafarki mikakke.
 
Manazarta:
[i] Siyar A’lam An-Nubala’ na Dhahabi(8/90).

[ii] Duba: Littafin da ya gabata (2/27).

[iii]  Al-Mugni, na Ibnu Kudama (2/97).

[iv]  Majmu’ Al-Fatawa, na Ibnu Taimiyyah (6/25).

[v]  Siyar A’lam An-Nubala’, na Zahabi (14/376).

[vi]  Majmu’ Al-Fatawa (19/191).

MATSALOLIN MA AURATADonde viven las historias. Descúbrelo ahora