JAGORAN AHLUSSUNNAH

100 1 1
                                    

*JAGORAN AHLUSSUNNAH*
 
 
 
📚 Wallafar
Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto

*Fitowa ta 6*

Ka’ida ta Hudu:
Ijtihadi Gaskiya ne. Taklidi ma Gaskiya ne.[i]
Mujtahidi shi ne wanda yake karanta Nassi ya fahimce shi kuma ya fitar da hukuncin Shari’a daga cikin sa. Mukallidi kuma shi ne wanda yake bin hukuncin da aka fitar ba tare da ya san Nassin da aka dauko hukuncin daga cikin sa ba. Bin Nassi ga asali shi ne wajibi a kan kowane Musulmi. Amma kuma kasancewar ba kowa ne yake iya karanta shi da fahimtar sa ba, sai ya zama lalura ta tilas a samu masu yin Ijtihadi da wadanda ba za su iya yi ba, su ne masu Takalidi. Kuma tun da Allah Ta’ala ya ce a tambayi Malamai[ii], to, bin abinda suka yi fatawa da shi daidai ne.
Shaihun Musulunci Ibnu Taimiyya _rahimahullahu_ yana cewa:
Abinda ilahirin al’umma suka tafi a kan sa shi ne: a dunkule, Ijtihadi ya halalta, Takalidi ma ya halalta. Ba su wajabta ma kowa da kowa yin Ijtihadi, su haramta yin Taklidi. Haka kuma ba su cewa, dole ne kowa ya yi Takalidi ya bar Ijtihadi idan har ya cancanta. Wanda bai kai matsayin da zai yi Ijtihadi ba shi ne ya halalta ya yi Takalidi.[iii]
Abinda ya wajaba mai bin Tafarkin Sunnah ya sani shi ne, akwai bambanci tsakanin tambayar Malami don yin aiki da fahimtarsa da kuma lizimtar ra’ayoyin wani Malami da Ijtihadinsa ta yadda zai zama a irin matsayin Manzon Allah; ba a saba ma maganarsa ko da kuwa ta yi hannun riga da Nassi. Daliban Ilimi wajibi ne a kowace mas’ala su nemi sanin dalilinta domin bauta ma Allah a cikin haske da basira. Idan gaskiya ta fito daga bakin ko wane Malami, hujjarsa ta bayyana, sai a rike ta gam; ayi aiki da ita, a kuma karantar da ita, don tana gaskiya ba don tana maganarsa ba. Don haka a kullum magana ake la’akari da ita ta fuskar karfin hujjarta da kwarin madogararta, ba mai maganar ba. Wannan shi ya sa malamai suka tabbatar ana ba Mujtahidi lada a kan ijtihadinsa. Amma ba a ba wanda ya bi shi a makance irin ta.
Ibnu Rajab Al-Hambali _rahimahullah_ yana cewa:
Sau da yawa akan samu shugaba daga cikin Malamai ya fadi maganar da an rinjaye ta (Ma’ana, ba ta da karfin hujja) amma kuma Ijtihadi ne ya yi da za a ba shi lada a kai, kuma a yafe masa kuskurensa. Wani kuma ya zo yana kariyar wannan Ijtihadin nasa amma ba zai samu wannan ladar da shi wancan ya samu ba. Domin yana kariyar maganarsa ne kawai don yana shi, ba don ya fadi gaskiya ba. In da kuwa wani ne ya fadi maganar ba shi ba, da ba zai karbe ta ba ballai kuma ya kare ta, ko ya nuna kaunar masu bin ta, da kin masu barin ta. Tare da haka, shi, a zatonsa yana taimakon gaskiya ne, alhalin ba haka ba ne. Malamin nasa ya yi iya kokarinsa ne don cim ma gaskiya da bayyana ta. Amma shi kam kokarinsa na daukaka darajar malaminsa ne da rinjayar da maganarsa a kan ta sauran malamai, da kokarin ganin ba a ce malaminsa ya yi kuskure ba. Wannan kuwa cuta ce da take hana nufin taimakon gaskiya. Ka fahimci wannan bayani don yana da amfani matuka. Allah shi ne mai shiryar da wanda ya so zuwa ga tafarki madaidaici.[iv]
Wannan shi ne abinda shugabannin mazhabobin Fikihu suka kira mutane zuwa gare shi. Ga maganganunsu nan an cirato kamar haka:
§  Imam Abu Hanifa (Ya rasu a 150H) ya ce: “Ba ya halalta ga kowane mutum ya dauki maganarmu sai ya san in da muka dauko ta”.[v]
§  Imam Malik (Ya rasu a 179H) ya ce: “Ni fa mutum ne mai yin daidai, ya yi kuskure. Don haka, ku rika duba fatawata. Abin da ya yi daidai da littafin Allah da Sunnar Manzonsa ku dauka. Wanda bai yi daidai ba ku bar shi.[vi]
§  Imam As-Shafi’i (Ya rasu 204H) ya ce: “Idan kuka samu abinda ya saba ma Sunnar Manzon Allah _sallallahu alaihi wasallam_ a cikin littafina, to ku rika Sunnar Manzon Allah _sallallahu alaihi wasallam_ ku bar maganata.[vii]
§  Imam Ahmad bn Hambal (Ya rasu a 241H): ya ce ma malaminsa Imam As-Shafi’i: “Ka fi ni sanin Hadisi. Abinda duk ya inganta a wurinka ka fada min don in yi aiki da shi”.[viii] Kuma ya ce: “Kada wanda ya dauki maganata ko ta Malik ko ta Shafi’i ko Auza’i ko Thauri. Kowa ya dauko daga inda muka dauka”.[ix]
Abu ne sananne a tsakanin malamai cewa, wadannan shugabannin gaba daya sun hadu a kan wata magana cewa, “Idan Hadisi ya inganta shi ne mazhabata”.[x] 
Don haka wanda ya bar Hadisi ingantacce ba mazhabarsu yake bi ba.
Sheikh Al-Fullani _rahimahullah_ yana cewa: Kada ka dauka maganar da suke cewa kada a bi su sai bisa ga hujja, wai da Mujtahidai suke magana. Sam. Suna magana ne da kowane musulmi.[xi]
Daga nan za mu fahimci cewa, lizimtar fatawoyin Malami daya ko mazhaba daya shi ne irin Takalidin jahilai wanda Malamai suka yi ta kai da komo a kan hukuncinsa. Wasu suka haramta shi, wasu kuma suka halalta shi saboda lalura. Amma babu shakka idan tare da haka, mutum ya zama yana kariya ga maganar wannan Malamin nasa ko Mazhabar tasa irin kariyar da ya kamata ayi ma maganar Manzon Allah _sallallahu alaihi wasallam,_ ta yadda zai rika lalubo hujjoji ko da suna da rauni, yana kariyar maganar malaminsa da su, yana ture hujjoji masu karfi da malamin nasa bai yi aiki da su ba, to wannan ya kauce ma tafarki madaidaici.
A takaice dai takalidanci uzuri ne wanda karancin sani da rashin kwarewa wajen nazari da bincike ke ba da damar yin sa. Amma idan mutum yana da kwarewa da ikon bincike kuma sannan ya bar littafin Allah da Sunnar Manzonsa ya kankame ma maganar wani malami, to ya zama kamar wanda ya ci mushe alhalin yana da halastaccen abinci.[xii]
Wannan shi zai kai mu ga ka’ida ta gaba:
 
*Manazarta*
[i]  Allah Ta’ala ne ya ce, Jahilai su tambayi Malamai. Kenan, Malamai su suke ijtihadi, su kuma jahilai sai su bi abinda Malamai suka fada masu.

[ii]  Suratun Nahli: 43 da Suratul Anbiya’: 7

[iii] Majmu’ Al-Fatawa na Ibnu Taimiyya (20/203).

[iv]  Jami’ Al-Ulum wa Al-Hikam, tahakikin Mahir Al-Fahl (3/979-980).

[v] Al-Intika’ na Ibn Abdil Barr (Shafi na 20).

[vi] Ikazh Himam Ulil Absar, na Fullani (Shafi na 72).

[vii] Al-Majmu’ na Imam Nawawi (1/63).

[viii] Al-Intika’ na Ibn Abdil Barr (Shafi na 75).

[ix] I’ilam Al-Muwakki’in an Rabbil Alamin,na Ibn Al-Kayyim (2/302).

[x]  Duba littafin: Ma’ana kaul Al-Muddalabi Idha Sahha Al-Hadith Fahuwa Madhhabi, na Subki, a cikin Majmu’at Ar-Rasa’il Al-Muniriyyah (2/98-114).

[xi]  Iqazh Himam Ulil Absar, na Fullani (Shafi na 50).

[xii]  I’ilam Al-Muwakki’in an Rabbil Alamin,na Ibn Al-Kayyim (2/344).

MATSALOLIN MA AURATAHikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin