JAGORAN AHLUSSUNNAH

28 0 0
                                    

*JAGORAN AHLUSSUNNAH*
📚 Mansur Sokoto

*Majalisi na 15*
*Ka’ida ta Goma Sha Biyu:*
Hadisi ba ya Bukatar Shaidar Alkur’ani
Idan Hadisi ya inganta daga Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam yana tabbatar da wani hukunci ko yana ba da wani labari, babu bukatar sai mun nemi wannan hukuncin ko mun samu wannan labarin a cikin Alkur’ani kafin mu gaskata shi. Domin Alkur’ani tuni ya tsarkake abin da Hadisi yake zuwa da shi tun da ya ce mu bi Manzon Allah sau da kafa. Kamar yadda ayoyin Alkur’ani a kan haka suka gabata.
Idan muka yi duba da kyau, aiko Manzo shi ne asali, saukar da littafi yana biye da shi. Wasu Annabawan ma ai ba a ba su littafi ba sam.[i]Wadanda aka ba su littafi kuma ba komai da komai ne littafansu suka kunsa ba. Misali, Annabi Musa Alaihis Salam da aka aiko shi zuwa ga Fir’auna da jama’arsa babu wani littafi a tare da shi tun da farko kuma ya tsayar masu da hujja har Allah ya hallaka su saboda kafircinsu, sannan daga baya Allah ya saukar masa da littafi, shi ne Attaura. Allah ta’ala ya ce:
وَلَقَدْ آتَيْنَا مُوسَى الْكِتَابَ مِنْ بَعْدِ مَا أَهْلَكْنَا الْقُرُونَ الْأُولَى بَصَائِرَ لِلنَّاسِ وَهُدًى وَرَحْمَةً لَعَلَّهُمْ يَتَذَكَّرُونَ
“Kuma hakika, mun ba Musa littafin (Attaura) bayan da muka hallaka karnukan farko don ya zama abin lura ga mutane, da shiriya da jinkayi ko da suna fadaka”. Suratul Kasas: 43.
Bisa ga bayanin da ya gabata muna iya cewa, duk Akidar da Annabi Musa Alaihis Salam ya karantar da Fir’auna da Hamana da jama’arsu, da Bani Isra’ila, da Hikimarsa[ii] ne ya karantar da su kafin saukar littafin Allah. Amma an karfafa shi da mu’ujizoji, masu gaskata shi suka gaskata, masu bijire wa imani kuma suka yi, aka hallaka su.
In muka dawo ga ibadoji za mu ga Manzon Allahsallallahu alaihi wasallamyana Sallah tare da Sahabbansa tun farkon Musulunci, tun suna yi a asirce har suka fara bayyanawa. Amma babu wata aya da ta sauka a lokacin tana wajabta masu yin ta, balai ta koya masu yadda ake yi. Sai a ranar Mi’iraji ne – shekaru takwas bayan bayyanar annabta - aka wajabta masu Salloli biyar, shi ma kuma ba aya ce ta faralta su a haka ba, Annabi ne dai ya yi bayanin (Sunnah kenan). Tare da haka Sahabbai suna alwala kamar yadda suka koya daga Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam tun kafin ayar alwala ta Suratul Ma’ida ta sauka shekaru ashirin da daya bayan aiko Annabi sallallahu alaihi wasallam.
Haka ita ma Sallar jum’ah an ba da tabbacin tsayar da ita a Madina karkashin limancin As’ad bn Zurara kafin hijirar Ma’aiki sallallahu alaihi wasallam zuwa can. Wannan kuwa ya gabaci saukar Suratul Jum’ah ita kanta.
A takaice dai, mumini da Manzo ne ya yi imani. Kuma ya yarda cewa, umurninsa duk gaskiya ne, babu son zuciya a ciki. Allah ya tsare shi daga wannan. Don haka, duk in da Nassi ya tabbata daga Annabi sallallahu alaihi wasallam to, babu wata shaida da mumini yake nema wadda ta wuce tabbatuwar sa din sai ya karbe shi ya yi aiki da shi.
 
*Manazarta:*
[i]  Kamar Annabi Nuhu, da Isma’il da Ishak da Yunus da Ludu da Hudu da Salihu da mafi yawan Annabawa duk ba a saukar masu da littafi ba, sai dai Hikima wadda ita ce Hadisi. Tare da haka Allah ya tabbatar ya yi masu wahayi kamar yadda ya ce: Hakika, mun yi wahayi zuwa gare ka kamar yadda muka yi zuwa ga Nuhu da annabawan da suke bayansa” Suratun Nisa’:163. Wannan karin hujja ne a kan cewa, Hikimar (Sunnah) ita ma wahayin ta ake yi musu.

[ii] Hikima a yaren Alkur’ani sau da yawa tana nufin Sunnah ne. Kamar yadda Allah subhanahu ya ce: “Kuma Allah ya saukar maka da Littafi da Hikima, kuma ya karantar da kai abin da ba ka taba sani ba, kuma falalar Allah ta kasance mai girma a gare ka” Suratun Nisa’i: 113. Kuma ya ce: “Kuma ku tuna – (Ya ku Matan Annabi!) da abinda ake karantawa a cikin dakunanku na ayoyin Allah da Hikima, hakika, Allah ya kasance mai ludufi ne, mai cikakken labari” Suratul Ahzab: 34. Duba kuma: Suratul Bakara: 129, 151, 231, 269 da Suratul Jum’ah: 2.

MATSALOLIN MA AURATADove le storie prendono vita. Scoprilo ora