JAGORAN AHLUSSUNNAH*

42 1 0
                                    

*Majalisi na 26*

*Ka’ida Sha Ashirin da Biyu:*
*Maganar Gaskiya Babu Tufka da Warwara a Cikin ta.*

Maganar Allah ba ta Cin Karo da ta Manzo.
Daga cikin hanyoyin da masu fada da Sunnar Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam ke bi don kawo mata cikas akwai yawan cewa, Hadisai sun ci karo da juna, ko kuma sun saba ma Alkur’ani. Duk Musulmi ya yi imani Alkur’ani maganar Allah ce, Hadisi kuma – ingantacce - maganar Manzon Allah ce. Wadannan biyun kuwa babu shakka gaskiya ne. To, ya ya za ayi maganar gaskiya ta ture irin ta?!
Mu kara duba yadda Allah madaukakin Sarki ya yi umurni da da’ar sa hade da ta Manzonsa in da yake cewa:
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا أَطِيعُوا اللَّهَ وَأَطِيعُوا الرَّسُولَ وَأُولِي الْأَمْرِ مِنْكُمْ فَإِنْ تَنَازَعْتُمْ فِي شَيْءٍ فَرُدُّوهُ إِلَى اللَّهِ وَالرَّسُولِ إِنْ كُنْتُمْ تُؤْمِنُونَ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ ذَلِكَ خَيْرٌ وَأَحْسَنُ تَأْوِيلًا
Ma’ana:
*“Ya ku wadanda suka yi imani! Ku yi da’a ga Allah, kuma ku yi da’a ga Manzo, da kuma majibintan al’amarinku. To, idan kun yi jayayya a wani abu to, ku mayar da shi zuwa ga Allah da Manzo in har kun kasance kuna yin imani da Allah da ranar lahira. Wannan shi ne alheri, kuma ya fi karshe mai kyau”*. Suratun Nisa’: 59
A cikin wannan aya da’a iri uku Allah madaukakin Sarki ya fada, biyu na farko a hade saboda ba su cin karo da juna balle a samu sabani a cikin su. Sai ta uku wadda ta zo daban, don takan iya zuwa sabanin umurnin Allah da na Manzo. A cikin wannan hali kuwa ba za ta yi aiki ba. Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam ya ce: “Ba a yin da’a ga halittacce a cikin sabon Allah (mahalicci)”.[i]
Wannan ka’ida ce mai matukar amfani ga Ahlus Sunnah. Domin mutum zai rika samun irin wannan zato bisa kuskure – ko ganganci - a cikin Hadisan Akida masu maganar gaibi wadanda ya wajaba ayi imani da su. Kamar yadda wasu suka soke Hadisan bayyanar Annabi Isah alaihis salam da saukowar sa daga sama kafin tashin Alkiyama. Wadannan Hadisan kuwa duk fitattun littafan Hadisi sun fitar da su, cikin su har da mafi ingancin su; Bukhari da Muslim. Kuma an samo su daga Sahabbai kusan arba’in, mafi yawan su ta hanyoyi ingantattu. Amma duk da haka sai su ce, Hadisan sun saba ma Alkur’ani. Kai ka ce su wadannan Sahabbai da tabi’ai da duk maruwaitan hadisan har zuwa su Bukhari da Muslim da jigajigan hadisi sun jahilci Alkur’ani! To, wane Alkur'anin ne ma suka saba ma? Shi dai wannan Alkur'anin da ke a gabanmu karara ya tabbatar cewa, duk wani magoyi bayan Annabi Isa _alaihis salam_ zai yi imani da shi kafin mutuwarsa. Suratun Nisa': 159 abinda ke tabbatar da cewa, bai mutu ba, amma nan gaba zai zo ya mutu. Ga kuma ijma'in malamai kakaf da suka tafi a kan yarda da haka kamar yadda masana suka tabbatar.[ii]
A cikin mas’alolin Fikihu ma akan samu irin wannan. Kamar yadda wasu malaman mazhabar Hanafiyya suka ce Hadisin da ya ce: “Wanda bai karanta Fatiha ba ba ya da Sallah”, wai, ya ci karo da Alkur’ani in da Allah Tabaraka wa Ta’ala ya ce: “Ku karanta abinda ya sawwaka daga cikin sa (Alkur’ani)” Suratul Muzzammil: 20. Alhalin Imamul Bukhari da Muslim sun fitar da Hadisin. Bukhari ma ya tabbatar cewa _Mutawatiri_ ne.[iii] Idan muka yi duba ga hawa da gangarar ayar za mu samu tana magana ne a kan Sallolin nafilar dare. Idan kuma ma an dauke ta a kan sallar farilla ne, to hanyar Ahlus Sunnah a nan ita ce, a bar kowanne a wurinsa. Ayar Alkur’ani ta yi umurni mutum ya karanta abinda ya sawwaka, Hadisi kuma ya ce, cikin abinda ya sawwaka dole ne a hada har da Fatiha. To, ina cin karo a nan?
Daga cikin rassan wannan ka’ida: "Ka'ida ta 23".
Ku dakace mu.
 
*Manazarta:*
[i] Sahih Muslim: 7520

[ii]Duba kusan duk littafan Tafsir na Malaman Sunnah a tafsirin waccan aya. Sannan ka duba littafin Lawami' Al-Anwar Al-Bahiyya, na Safariniy da kuma At-Tasrih bi ma Tawatara fi Nuzul Al-Masih na Muhammad Anwar Kashmiri.

[iii] Duba misali: Sahih Al-Bukhari (756) da Sahih Muslim (394).

MATSALOLIN MA AURATAWhere stories live. Discover now