*JAGORAN AHLUSSUNNAH*
📚 Dr. Mansur Sokoto
💐🌺💐*Majlisi na 17*
*Ka’ida ta Sha Hudu:*
*Sahabban Manzon Allah sun fi kowa sani da fahimtar maganarsa*Martaba da matsayin Sahabbai ba abu ne da ya dace a samu jayayya a cikin sa ba. Duk mai karatun Alkur’ani ya ga tarin matsayi da girman falala da Allah ya ba su. Ba shi muke magana a nan ba. Kasancewar su almajiran Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam na kai tsaye wadanda suka shawo daga tafkinsa babu garwaye. Ga su kuma saboda sabon su da shi, ko motsi ya yi suna iya fassara shi. Tare da haka, sun samu cikakkiyar dama ta yi masa tambaya kan duk abinda ya shige masu duhu cikin abinda Allah ya saukar. Kuma babu shakka, sun sha tambayar sa a kan abinda ba su gane ba sai ya fahimtar da su. Wannan kuwa dalili ne a kan cewa, abinda ba su tambaya ba sun fahimce shi. Kari a kan haka, shi ma Annabi sallallahu alaihi wasallam da kansa idan ya san cewa ba su gane ba zai yi masu karin bayani bisa umurnin Allah. Kamar yadda Allah ta’ala ya ce:
وَأَنْزَلْنَا إِلَيْكَ الذِّكْرَ لِتُبَيِّنَ لِلنَّاسِ مَا نُزِّلَ إِلَيْهِمْ وَلَعَلَّهُمْ يَتَفَكَّرُونَ
“Kuma mun saukar maka da Ambato ne domin ka yi ma mutane bayanin abinda aka saukar masu, ko da za su fadaka”. Suratun Nahl: 44
Bisa ga haka, duk wata fassara ko fahimta wadda ta saba ma ta Sahabbai a Alkur’ani ko Hadisi abar nisanta ce, matukar ta ci karo da tasu fahimtar.
Misali a kan wannan shi ne, wata fassarar da ta bayyana game da fadar Allah subhanahu wa ta’ala: game da mata masu rashin ladabi da tawaye ga mazajensu:
وَاللَّاتِي تَخَافُونَ نُشُوزَهُنَّ فَعِظُوهُنَّ وَاهْجُرُوهُنَّ فِي الْمَضَاجِعِ وَاضْرِبُوهُنَّ فَإِنْ أَطَعْنَكُمْ فَلَا تَبْغُوا عَلَيْهِنَّ سَبِيلًا إِنَّ اللَّهَ كَانَ عَلِيًّا كَبِيرًا
Ma’ana:
Kuma wadanda kuke jin tsoron tawayensu (daga cikin matan aurenku), to ku yi masu wa’azi, kuma ku kaurace masu a shimfidu, kuma ku buge su. To, idan sun yi maku da’a to, kada ku nemi wata hanya a kan su (ta cutar da su). Hakika, Allah ya kasance madaukaki ne, babba.
Wannan aya tana shiryar da mazaje ne ga hanyoyin da suka halalta abi wajen ladabtar da matan aure idan suka yi kangara; suka bijire ma da’a. kuma cikin abubuwan da ayar ta lissafa har da dukan Macce idan lurarwa da kauracewa sun faskara. Duka kuwa suna ya tara kamar yadda duk mai hankali ya sani. Akwai duka na ladabtarwa da jan hankali, akwai na muzgunawa da cin zarafi. Akwai kuma na ukuba da tozartawa. To, wanne Shari’a take nufi a nan? Babu shakka, duk wanda yake karanta nassin Alkur’ani da hadisan Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam ya san irin tarainiyar da Musulunci ya yi umurni da ita ga Mata tare da matukar kula da kyautatawa da kuma kaurace ma cutarwa. Don haka, daga lura ta hankali ana iya gane abinda Alkur’ani yake nufi a nan. Tare da haka, Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam wanda aka saukar ma Alkur’ani bai bar maganar a rufe ba sai da ya fassara ta, kamar yadda ya zo a cikin Sahihu Muslim a cikin wasiyyar Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam ta karshe lokacin Hajjin bankwana, in da yake cewa: “Ku ji tsoron Allah game da Mata, saboda kun karbe su ne da amincin Allah, kun halasta farjojinsu da kalimar Allah. Kuna da hakki a kan su; kada su dora kowa a kan shimfidarku. Idan kuwa har suka aikata haka, to ku buge su bugu ba mai cutarwa ba. Su kuma suna da alhakin ciyarwa da sutura gwargwadon hali a kan ku”.[i] An tambayi Ibnu Abbas radhiyallahu anhugame da fadar Manzon Allah sallallahu alaihi wasallamcewa: “ku buge su bugu ba mai cutarwa ba” sai ya ce, bugu da aswaki ko makamancinsa.[ii]
Imam Al-Bukhari rahimahullah ya yi babi a cikin ingantaccen littafinsa a cikin Kitab An-Nikah: “Babin kyamar da ake yi ga dukan Mata, da fadar Allah “Kuma ku dake su” yana nufin dukan da ba ya cutarwa”. Sannan sai ya kawo hadisin Abdullah bn Zam’ah radhiyallahu anhu daga Annabi sallallahu alaihi wasallam cewa: “Kada dayanku ya daki matarsa irin dukan bawansa, sannan ya zo karshen wuni yana (son) saduwa da ita”.[iii]
Haka kuma Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam ya yi hani ga duka a fuska, kamar yadda ya zo a hadisin Jabir radhiyallahu anhu a cikin Sahihu Muslim.[iv]
Wannan ita ce fassarar Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam ga wannan aya, kamar yadda ita ce fassarar magabata. Imam Ibnu Jarir rahimahullah yana cewa:
Masu fassara sun ce, sifar bugun da Allah ya halalta ayi ma macce mai yi wa miji tawaye ita ce, bugun da ba ya cutarwa.[v]
Halascin dukan Macce maras da’a kamar ya zo a waccan aya, ba yana nufin abinda ake so ne ba. Abu ne dai da aka ba da dama idan dalili ya kama, kuma bisa sharadin ya kasance na ladabtarwa mai sauki ba na yin ukuba da cutarwa da cin zarafi ba, ba kuma a fuska ba. Wannan halascin ijma’i ne na magabata. Amma mutanen kirki sukan kauce ma yin dukan duk da halscinsa. A hadisin Iyas bn Abdillah bn Abi Dhubab, Annabi sallallahu alaihi wasallam ya hana dukan mata a wani lokaci, sai mata suka rika fandare wa mazajensu, da aka fada masa sai ya yi izni, su kuma sai matan suka yi koke. Annabi sallallahu alaihi wasallam ya yi wata huduba wadda a cikin ta ya ambaci yawan koken mata kan wannan batu, kuma ya kara da cewa: “Masu dukan ba su ne mafifitanku ba”.[vi]
Imam As-Shafi’i rahimahullah ya yi sharhi a kan hadisin ya ce: “Sai Allah ya halasta wa maza duka, ya ba su damar yafewa, kuma ya nuna barin dukan shi ya fi.[vii]
Al-Hafiz Ibnu Hajar shi ma abinda ya ce: “Wannan ya nuna a jumlace dukan su halas ne a wajen ladabtarwa idan suka yi abinda bai dace ba in da ya kamata su yi biyayya. Amma idan miji ya wadatu da tsoratarwa da makamancin haka ya fi. Kuma duk lokacin da nuni ko furuci ke iya wadatarwa bai kamata a wuce su zuwa duka ba’.[viii]
Shi kam Annabi sallallahu alaihi wasallam bai taba dukan Macce ko bawa, ko ma dabba ba. In ji Nana A’isha radhiyallahu anha.[ix] Imam Nawawi ya ce: “wannan ya nuna cewa, dukan Macce da bawa da kuma dabba, duk da yake halas ne domin ladabtarwa amma barin sa ya fi.[x]
Tabbas, sanannen abu a wurin masu hankali cewa, hanyar ladabtarwa takan ba da kofa ga abinda ba shi aka saba yi ba. Haka dokokin kowace kasa da al’umma suke bayarwa. Iyaye sukan yi ma ‘ya’yansu duka don jan hankali da ladabtarwa. Maigida ma yakan daki bawansa da wannan manufa. Hukuma ita kanta, takan iya jefa barkonon tsohuwa a kan masu gangami haramtacce don gudun su afka wa jama’a ko su haifar da tarzoma mai lahani da keta doka.
Daga nan za mu fahimci cewa, wata fassarar zamani da ta bayyana ga ayar da muka kawo a sama, tana cewa, ba duka ake nufi da ayar ba, bayan Annabi sallallahu alaihi wasallam ya fassara ta a haka tare da sharhi da karin bayani, magabatan al’umma kuma sun hadu a kan haka, waccan fassara yasasshiya ce marar ma’ana saboda sabawar ta ga fassarar mutanen farko.
*Manazarta:*
[i] Sahihu Muslim (1218). Wannan riwayar Jabir kenan a Sahihu Muslim. A riwayar Amr bn Al-Ahwas radhiyallahu anhu cewa ya yi: “Ku ji tsoron Allah game da Mata, domin Allah ya hore maku su ne. Ba ku da wani abu a kan su wanda ya wuce haka. Sai fa idan sun zo da alfasha wacce take karara. To, idan suka yi haka, to ku kaurace masu a shimfidu, kuma ku buge su bugu ba mai cutarwa ba. Idan suka dawo yi maku biyayya kada ku sake taba su”. Al-Musannaf, na Ibn Abi Shaiba (2/56) da as-Sunan Al-Kubra, na Nasa’i (9169) da Sunan At-Tirmidhi (1163) da Sunan Ibn Majah (1851). Kuma Tirmidhi ya ce, hadisin mai kyau ne.[ii] Tafsir Ibn Jarir (5/68) da kuma Ad-Dur Al-Manthur fi At-Tafsir Al-Ma’thur,na Suyudi (2/523).
[iii] Sahih Al-Bukhari, hadisi na 4908.
[iv] Sahihu Muslim (2116).
[v] Jami’ Al-Bayan fi Ta’wil Alkur’an, na Ibnu Jarir Ad-Dabari (8/313).
[vi] Sunan Abi DAwud (1834) da Sunan Ibn Majah (1975) da Sunan Ad-Darimi(2122) kuma Ibn Hibban ya inganta shi a Sahihinsa (4189) da kuma Sheikh Albani a Sahihu Abi Dawud.
[vii] Al-Ummu, na Imam As-Shafi’i (5/112).
[viii] FathAl-Bari,na Ibnu Hajar (9/304). Duba kuma: Aun Al-Ma’bud, na Mubarakfuri (6/128).
[ix] Sahih Al-Bukhari (3560) da Sahih Muslim (4296).
[x] Sharhu Sahih Muslim na Nawawi (15/84).
YOU ARE READING
MATSALOLIN MA AURATA
SpiritualKi samu sassaken biyayya ki hada da saiwar shagwaba da ganyen gaskiya da bawan San dangin sa da jijiyar Kula da mahaifiyar sa ki hada su a turmin nan mai suna hakuri ki samu tabaryarnan Mai Suna Iya Magana ki daka su insha Allah Zaki mallaki mijin k...