Page 1

3.6K 124 9
                                    

*BANYI ZATO*.
Mrs j Moon.

*01*

Abakin windown wani daki mai cin mutum d'aya dake cikin asibitin mahaukata dake cikin gari kaduna, wata kyakykyawan matashiyar budurwa ce tsaye tana kuka mai sauti.
   Gefenta wani  matashi ne mai kama da ita sosai, magana yake mata cikin taushin murya kuma cikin sigan rarrashi.

"Mamiena kiyi haquri don Allah kibar kukannan haka, ummanmu addu'arki take nema bayawan kuka ba."
     ya fesar da iska yana maijin wani d'aci cikin ransa, yacigaba dacewa "Shi yasa banason zuwa dake dubata sabida irin halinnan da kike fad'awa na koke koke."

  Ita dai budurwan wacce yakira da mamie sai kukanta takeyi, cikin kukan tasoma cewa "Wllahi bazan taba yafewa wanda yayi sanadin jefamin uwa cikin wannan bala'inba sai na had'ashi da ubangijina yabi mata hakkinta."

   "Mamiena kizomo mai tawakkali da yarda da qaddara mana, ki cire zaton da kikeyi na wani ne yayi sanadin fad'awar ummanmu cikin wannan halin, ki yarda cewa Allah SWA shine mai wanzar ma da bawa duk abinda yaso a kuma lokacin da yaga dama, kizamo mai kyautata niyyarki ga kowa kiyi watsi da abinda shaid'an la'anan ne yake raya miki akan k'addararmu."

   Juyo da rinannun idanunta tayi ta zuba mishi tare da d'auke kukanta muryanta yana rawa tace "Brother H, kasan nid'in mai yarda da dukkan abinda katunar dani akai ne to amma wallahi yau dai zuciyata tagaza d'aukan tunatar wannan naka don haka kayi shiru don bajinka zanyiba balle na fahimta."

  "Ya salam!!! Yafurta tare da janyota jikinsa yasoma magana "Mamiena kada kiyi sabon Allah mana, ki amince da zancena donmin fadan Annabi S.A.W ne cewa duk wanda ya yarda da Allah da manzonsa da ranar qarshe  to yayarda da kaddara mai kyau ko kishiyarta, sabida haka yazama mana dole muyi biyayya ga Manzon Allah S.A.W indai munason ganin lamarinmu yatafi cikin salama tare da samun kyakykyawan sakamako ranar mahashar."

   Ahankali tasaki kuka tana jijjiga kai "Nayarda da qaddara Allah yabama Ummanmu lafiya cikin amincin Allah."

"Amin." ya amsa yana mai share mata hawayen dake zubowa saman cheek nata kamar anbud'e bakin tap.

Bakin windown ta koma tacigaba da kallon mahaifiyarta nasu wacce ke kwance bisa qasa duk da sanyin dake zubawa amma taqi hawa gado gata kuma d'auke da tsohon ciki yayi wani irin girma.

Ina gefe na qarewa matar kallo farace tas mai dan jiki kuma doguwace mai yalwar sumar kai saidai duk ya cukud'e yayi datti alamun yana buqatar gyara.

Wani qara matar ta saki alokaci d'aya kuma ta miqe tasoma buge buge tana ihu tana kaima cikin jikinta duka.

Agigice budurwan ta fad'a d'akin yayin da saurayin ya falla da gudu zuwa kiran doctors.

K'amqameta tayi ita kam sai duka take kaima yarinyar amma taqi sakinta duk kuwa da zafin dukan da ta keji, Ita dai burinta kada tayiwa kan rauni ko babyn cikinta.

    Cikin kuka take karanta mata ayar *Wattaba'u matatulul shayad'inu ala mulki sulaiman.*

Abin mamaki ko kafin doctors su iso tabar buge bugen ta kwanta lak'os jikin budurwan har ta koma barcinta.

Cike da al'ajabi doctors din tare da d'an uwanta suke dubanta, daya daga cikin doctors d'in yajefo mata tambaya inda yace "Me kika bata ta bar buge bugen har barci ya kwasheta?"

   "Ayar ALQUR'ANI mai qirma na karanta mata kuma cikin ikon Allah tabari takoma barcin data keyi."

  Jinjina kai sukayi sannan suka d'auketa suka maida bisa gado suka yi mata allura tare da barin wurin zuciyoyinsu cike da jimamin halin take ciki. Managarciyar mata mai tarin hankali da natsuwa amma tasami kanta cikin laluran tabin hankali.
Dan sun santa sosai sanda take zuwa duba marasa lafiya tare da bama masu jinyojinsu taimakon kud'i akula dasu.

Takowa yayi ya iso inda take kwance yakama hannunta yayi ta tofa mata addu'a sannan ya matso inda mamie take tsaye duk ta had'a zufa yaja hannunta suka fito.
  Cikin mota yasanyata ya zagaya ya zauna a driver seat ya ja motar suka bar harabar asibitin.

Sunyi tafiya mai isa sannun ya juyo ya dubeta yaga har lokacin hawaye take sharewa ya kauda kansa cike da jin zafin ganin zubar hawayen.

"Mamiena kibar kukan haka nan don Allah."
"Uhmm." Tace kawai tare da kauda fuskanta gefe ta tsirwa motoci dake wucewa idanu.

     "Dole insami Abba da mummy asan abinyi akan ummanmu sabida nima yanzu nagano wani abu atare da ita."

Juyowa tayi tabud'e baki da kyat tace "miye shi?"
"Bari sai naji naga bakin su Abba tukunna zan sanar miki."

  Tayi shiru tana cigaba da kallon titi ruhinfa cike da tunani.

A haka suka iso bakin wani katafaren gida mai kyau da tsari.
   Bayan bud'e musu gate d'in da mai gadi yayi suka shiga ciki ya gyara perkin a wurin ajiye motoci.

A jere suke tafiya suka doshi shiga cikin gidan.
   
" 'Ya'yan mahaukaciya, jikokin gidan marayu andawo daga yawon tazubar d'in da aka saba ko?  Ajuri zuwa rafi dai wata rana tulu zai fashe awayi gari muji ana kakarin amaimayi."

     Wata mata ce bak'a tana da kyau ba laifi take fad'an haka.

Ko juyowa ba wanda yayi balle tasaran zasu tankama mata. Sabida sun saba da jin irin haka tun Ummansu na da lafiyarta.

  Ta saki dariya har da shewa "Muzuba nida ku yara muga wazai ci riba."

Mamie ce ta juyo tace da ita "Allah yana tare da mai gaskiya mama, ummanmu zata warke kamar kowa mai hankali da yardan Allahu, sannan kuma fata nagari kamiri ne, bakinki ya sari bishiyar can da kike zaune.
 
Afusace matar tayo kansu.
Tana shirin fizgo mamie yasa hannu ya tare ta cikin kaushin murya yace "A'a mama muna ganin girmanki ama tsayinki na matar baffanmu."

  Daga haka yaja hannun k'anwar nasa suka shige part d'in Ummansu, suka bar matan da baki bud'e tana mamakin yarda yaron ya maida mata da martani alhalin tunda take cin masu fuska baitaba kulawa ba balle yatanka."

"Tabd'ijan lallai watan cin misu k'aniya la'ada waje ya tsaya." Ta furta tare da komawa inda take zaune qasar wata bishiya tana ta fesa bambamin fad'a kamar shafan almatsutsai.

BANYI ZATO BADonde viven las historias. Descúbrelo ahora