page 21 to 25.

840 38 2
                                    

Banyi zato ba.
Mrsjmoon

*11 to 25*

"Ummun Hakeem Allah Hajiya shafa'atu tasoma yimana wasa da dukiya, abinda sam yin hakan ba halinta ba ne."

"Uhm mummyn twins ayimata uzuri kinsan lamarin garin sai ahankali, muta ne suna son abu kuma gashi babu kud'in siyansa, shi yasa in sun d'auka suke d'ad'ewa basu biya ba."

"Kumafa haka ne amiyata, to Allah ya warwarema kowa"

"Amin."

Sun d'auki lokaci mai tsawo suna lissafi akan business d'insu bayan su kammala suka d'ora da hira irinta aminai masu tarin rik'on amana da gaskiya.

Umma ta muskuta tana kallon mummy tace "Aminiyata Allah banyar da keba."

"Kamar ya mom twins?"

"A kan lamarinki da yaya Umar."

Had'e rai tayi tare da kauda fuska gefe.

Itama umma had'e rai tayi tace "Inajinki fad'amin abinda yayi miki da zafi wanda yasa kikak'i amincewa da buk'atarsa na son aurenki."

Cikin fushi tace "Mubar zance kawai Umman Hakeem."

"A'a Momyn Sady bazan bariba, inkuma mun soma 'yar haka dake ne sai inji."

Sunkuyar dakanta tayi tace "Tunda kindage sai kinji to kisani Umar shi ne mutumin da ya yaudareni ya lalatamin budurcina kuma da ciki ya baiyana jikina yayimin tijara tare da guduna yabarni cikin k'unci."

Idanu waje umma take kallonta sai kuma ta dafe kanta tasoma kwalla muryanta yayi rauni tace "K'awata dagaske kikeyi ko dai wasa ne?"

"Tunda muke da ke nataba yima wani k'azafi? da yanzu zakiyi wasi-wasi akan zancen da nafad'a miki."

"A'a Momyn Sady baki tab'a ba amma abin ne yazomin abazata."

"To ki amince da maganar dana fad'a miki gaskiya ne domin wannan shi ne dalilin dana k'i amincewa da zancen."

"Nayarda Aminiyata amma taya tsawan lokaci muna tare baki ganeshiba sai yanzu? Ko kin rufamishi asirine sai yanzu daya nemi zamowa abokin rayuwarki kikayi k'ok'arin hukuntashi ta wannan hanyar?"

"Ko d'aya bantaba sanin kuna tare da Umar ba sai ranar da Yunus yaso yin kidnapping d'in mamie na had'u dashi amma shi naga alama ya sanni tare da ku, wata k'ila b'oyewa yake da zaran yaganni daya gaji ne ya fitomin."

"Ina jin haka ne, don kunyarki bazai barshi yanuna kansa ba, amma wallahi *banyi zatoba* Allah banyi zaton jin mugun labari irin wannan akan yaya Umar ba sam, mutum ma'abocin karamci da natsuwa haka, a she shima kwallon d'an bariki ne."

"Uhmm k'awata aishi mutum baka shaidanshi domin halinsa birninsa wanda shi kad'ai yasan abinda ke cikinta."

"Hakane kam, Allah yabarmu da kyakykyawan zuciyoyi."

"Amin dai aminiyata."

Duk kansu shiru sukayi kowa yana sak'e-sak'e a cikin zuciyarsa.

Mummy taja numfashi tace "Shiyasa sanda naji Yunus d'ansa ne nace magaji mafiyi kuma alhakina ne yake bibiyarsa shiyasa Allah yajarabce shi da d'a irin Yunus dangin iblis."

"Tabbas Allah ya jarabci yaya Umar da tak'adarin d'a wanda da haihuwar irinsa gara barinsa a huta da dai irin jafa'in dayake jawo ma ubansa tare da mu makwaftansu, Allah natuba kagafarceni ba izgili nakeyima ba."

"Allah yashirya shine kawai abin fad'a, amma yaron nan yayi nisa bayajin kira."

"Allah yashirya shi inmai shiryuwa ne."

BANYI ZATO BATempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang