page 5

627 37 1
                                    

*7 to 8*

Umma cikin rashin kuzari da bai gama isartaba ta d'agota tasoma share mata hawaye tana cewa "Godiya zakima Allah da yanufeni da samun lafiya ba kuka ba Mamie."

Tak'ara komawa jikin umman ta lafe tare k'ak'ameta tana fad'in "Allah mungode mata Allah kak'ara tsaremin mahaifiyata da duk kan al'umar musulmi daga fad'awa laluran hauka dama dikkan lalurar cuts."

"Amin ya rabbil Alamina." Umma ta amsa sannan saura mutanen dake saura ronsu suka amsa suma da Amin.

Duk sun kewaye Hajiya Jidda da Mummy suna kallon yadda akeyiwa jariirai wanka, inda Hajiya Jidda take wankesu Mummy kuma tana zubda ruwa takuma d'ebo wasu.

Angama wankesu tas an shiryasu cikin kayan sanyi farare sai k'amshinshi suke zubawa.
Mamie, Sadiya, Madeeha tare da Hameeda sai d'aukan su photo sukeyi za'a sanyasu astatus da dp.
  
Umma tana kwance a bisa doguwar kujera sai murmushi takeyi musu.
Itama tayi wanka tashirya tsaf abinta kamar ba itace laluran hauka yasame taba, sai dai ramar da tayi tare da duhu  wanda wannan kuma sai a hankali zai dawo.

Abdul Hakeem ne ya shigo yasanar dasu malamin ya iso.
  "Maza shigo dashi ciki." cewar mummy.

Abba tare da malamin suka shigo Abdul Hakeem yana biye dasu abaya.

Bayan gaishe gaishe malam ya dubi umma wacce ta lumshe idanunta tun shigowar malamin yayi murmushi tare da girgiza kai.

"Hajiya Na'ima, yakira sunarta."
Tabud'e idanu tayi wal dasu sai kuma ta kulle gam.
  Ya matso inda take yayi addu'a a wani ruwa da yazo dashi ya guntsa ya fesa mata a fuska tasaki k'ara ya k'ara fesa mata ta kuma sakin qara ya qara fesa mata akaro na uku sai ta soma atishawa ba k'ak'k'autawa sai da tayi kimanin mintoci biyar tanayi sannan ta dakata.
  Muryanta can k'asa ta furta "Alhamdulillah."
   Duka wurin tare da malamin suma suka d'auka da "Alhamdulillah."

Abba ya matsa jikinta yasa rigarsa yana share mata Hawaye tare da majinar da yafito mata yayin atishawar yana jera mata sannu cikin matuk'ar kulawa.

  Sai duk yabama yaran kunya, suka kauda fuska suna dariya k'asa-k'asa yayin da Hakeem abin yayi matuqar burgeshi mummy tare da Hajiya jidda sunkuyar da kai sukayi cike da jin dad'in irin kulawan da yanuna mata gaban jama'a.

Malam yayi gyaran murya sannan yasoma magana "Tabbas asiri akayi mata amma an tone abin yau d'innan shi yasa cikin hukuncin Allah surkullen ya warware amma sai junnun da aka had'ata dasu suka nemi su zauna a jikinta shi yasa sanda nazo suka nemi birkitata amma cikin ikon Allah sunyi gaba abinsu sunbarta, don dama ba wurin zamansu bane."

Yanzu zan bada magani wanda zatayi wanka d ashi tare da sha har tsawon kwanaki uku, sannan kuma zan bada wani wanda ita da yaranta jariran da manyan zasu riqa wanka dashi kullum, inya qare zan kawo wani.
  Domin abin sai da tsari sabida komi yake faruwa agidan ne kuma in sun sami labarin an karya asirinsu to zasu kuma bin wata hanyar don haka indai suna amfani da maganin kuma da yawan azkar tare da karatun AL-QUR'ANI mai girma to ba tantama sunfi qarfinsu, badai mutumba sai dai ikon Allah."

Yabada duk abinda yace  tare dayi masu bayanin yarda za ayi amfani dashi yayi musu sallama, su mummy da hajiya Jidda sai godiya sukeyi masa tare da samasa albarka, yayin da su Abba suka bi bayansa domin sallamarsa.

Abinda yafaru shine.

Da hantsi Dada ta shiga garden inda ta binne bak'ar layan da yayi sanadin haukacewar salihar surukanta.
Tayi taneman inda ta binne tarasa, duk ta had'a zufa sabida zafin rana amma taqi haqura da neman wurin.
Ta kwashe kimanin 1hr tana abu d'aya.
Ganin bazata gane wurinba yasa ta yanke shawaran fitowa tana addu'ar Allah ya dubi halin da Na'ima ke ciki ya yanke mata wahala ta sami kafiya.

  K'afar tane ya zame zata fad'i tayi saurin tafa qasa saiko hannunta ya zurma wani d'an rami, har ta wuce ta dawo da baya tasa wuk'a tasoma hak'a ramin abin mamaki sai gashi taci karo da dutsen da ta danne layar sannan akabi da qasa.
Jikinta na rawa ta d'aga dutsen sai ga layyar batayi komi ba tasa leda ta d'auka tayi gaggawan gonawa ta d'auki tokar ta watsa a masai wanda ma aika tan gidan ke amfani dashi.

To adai dai lokacin kuma Umma ta farka daga barcin wahalar da ya d'au keta bayan tagama buge bugenta.
  
Da hamdalah ta farka tasoma bin d'akin datake da kallo, kafin ta tantance inda take maranta ta murd'a tare da wani azababben ciwon baya.
Cikin 'yan seconds nak'uda tazo mata gadan-gadan.
Tasoma salati da sallallami tana kiran sunayen Allah S.W.A.

A daidai kuma su Abba sun gama cike takardun sunyi komi sun iso inda take domin d'aukanta su tafi.
Doctors d'in dasu kayi musu jagora sune suka fara ganin halin da ta ke ciki aiko cikin gaggawan suka rufu akanta.
  
Bajimawa ta haifo yaranta biyu kyawawa dasu kuma masu k'oshin lafiya.

Abinda yabawa doctors tare da su mummy maki shine ganita cikin natsuwa ba alamar tabin hankali.
  A take sukayi ta sujjada suna masu mik'a godiyarsu ga Allah da yanunamisu ganin wannan rana mai tarin Albarka da farin ciki mara musaltuwa na samuwan lafiyar ta.

Saida ta huta sannan suka nufo gida.
A inda aminiyarta hajiya fiddausi tabata labarin abinda yasameta tayi ta hawaye tana kuma godewa Allah daya bata lafiya cikin tak'aitaccen lokaci.

Yau kwana hud'u da haihuwarta amma har yanzu bata koma gidantaba tana nan tare da sahibarta duk kuwa da Hajiya Jidda taso ta tafi da ita gidanta amma fir mummy tak'i dama Hajiyan ta matsa sai tasa mata kuka ganin haka ta hak'ura amma kullum tana gidan, anan take yini sai marece take komawa gidanta.

'Yan gidan marayu kuwa sahu sahu manyansu da yaransu sukayi ta zuwa ganin babies da yima mmnsu sambarka.
Sabida sunyi kewar alkhairinta garesu sosai kuma suma sun te maka wurin yi mata addu'ar samun lafiya.

Ana gobe suna Dada ta matsa sai ta dawo d'akinta anyi suna a can.
    Dada ma tana zuwa duk bayan kwana biyu.
 
Bawanda yafad'awa mama da Yunus samun kafiyarta alhalin kuwa mijinta Baffa yasani yaranta Imranat da Fatima har barka sunzo, baffan ne bai sami zuwaba, Dada ce ta kwab'esu da kada su fad'a masu.

Bayanda mummy ta iya sai haquri tunda Dada ta tubure sai ta koma d'akin ta.

Anyima d'akinnata saukan Alqur'ani tun haihuwarta da kwana biyu.

An gyara d'akin tsaf komi sabo akasaka cikinsa, yayi kyau sosai, akabishi da turaren wuta mai dan karen k'amshi.
 
Duk abinda akeyi shu'umar Hajiya Mama bata saniba don bata zama gida ana can bin bokaye.
Shiko Yunus yayi tafiya yawan ta zubar d'insa amma sai yacewa Baffansa aiki aka turashi Bauchi.

Mota biyu aka ciko zuwa gidanta.

Dada tana jin dirin motoci tayo waje da murna tana fad'in "Lale-lale marhabin da zuwa surukan arziki, irin Albarka, matar arziki, Allah ya cigaba da tsaremana ke cikin amincinsa."

"Amin Dada." Baffa dake bayanta ya amsa yayin da mama ta zuba idanu tagani ko Amarya Usman yayi, wata Abba.

Amma abisa mamaki sai taga Na'ima ce ta nufo Dada da sarsarfa ta rungumeta ga yara nan biyu d'auke a hannun mummy da Hajiya Jidda.
  Jikinta na rawa ta koma da baya zuwa part d'inta da gudu ta k'arasa cikin toilet tasoma zuba zawo a tsaye duk ta bata jikinta, ko lurabda hakan batayiba dan tsaba rud'ewan da tayi na ganin Umma  cikin k'oshin lafiya shine ya haifar mata da birki cewan ciki wanda sai da ta kaiwa ma'aikatan sarrafa kashi ziyara (M.S.K Company) lol.

Baffa shina yashiga rud'ani, jikinsa narawa muryansa yana sark'ewa kuma cikin dusasshewa yace "Fiddausi!.

Mummy kam bata jisaba balle sauran kuma, don sunyi masa nisa yadda bawanda zaijiyo  maganarsa.

'Dakinsa yakoma yayi ta safa da marwa hannayensa  goye abaya.
"Ina cikin da... sai kuma ya rufe bakinsa yana waige waige, cikin hanzari kuma ya d'auki wayarsa yasoma dialling number Abdul Hakeem.

  "Kazo d'akina yanzu ina jiranka."

Yace dashi tare da cigaba da zagaye d'akin cike da fargaba.

BANYI ZATO BAWhere stories live. Discover now