page 26 to 30

1.2K 56 7
                                    

Banyi zato ba.

Mrsjmoon

*26 to 30*

Yana k'ok'arin bud'e motarsa ya tsinkayi muryan Baffa.
"Abdul hakeem inazuwa haka tun gari baigama wayewa ba?"

Cike da girmamawa ya juyo ya russuna "Baffa antashi lafiya?"

"Lafiya lau Hakeem, ina zaka naganka a gaggauce?"

"Mamie ce
Dr. Bilyamin yafad'amin sunbata gado wai bata da lafiya tun daren jiya."

"Ya salam!! Abu baiyi dad'iba kam, me ke damunta?"

"Bai fad'aminba tukunna sai in na'isa zanji ko me ye."

"Ok muje nima inganta, Allah yakawo sauk'i."

"Amin Baffa."

Shiga motar yayi suka wuce zuciyoyinsu cike da addu'ar neman mata sauk'i wurin  mai duka.

Yunus wanda ke tsaye kusa dasu basu lura da shiba saka makon hankalinsu baya wurin, yaji komi dasuke ce magana akai.

Cikin sanyin jiki ya bud'e motarsa yashiga ya zauna tare da dafe kansa yana fad'in "Allah natuba, Allah kayafemin gulmar dana k'ulla wanda nasan shi ne yayi sanadin kwanciyar yarinyar arziki jinya."

Abin mamaki sai ga Yunus yana matsan kalla cike da tarin nadamar abinda ya aikata, a haka yaja motarsa zuwa gidan da ummansa take zaune don dama yafito ne da shirin zuwa can yafad'a mata ya tuba itama yakamata ta gyara halaiyanta ko tasami kyakykyawan k'arshe. Shiriya ya zo masa inda cikin dare d'aya yaji tsoron gamuwarsa da Allah in har ya mutu cikin wannan rayuwar tabbas yasan babushiba samun rahama Allah.
Tuk'i yakeyi yana jan tsaki tare jama kansa kalmar Allah wadai sabida tunowa da irin shed'ancin da yayi na alfasha.

Hakeem yana gyara parking Dr. B. yana isowa tare da mummy.

Musabaha sukayi da juna yayin da Baffa da mummy sukayi kallon kallo basu tankama juna ba.

Hakeem ya dubesu cike da zargin amma sai yabasar ya isa wurin mummy tare da gaisheta, ta amsa suka shiga ciki.

Tsaye suke cirko-cirko kan Mamie wacce take ta sharan barci amma kallo d'aya zakayi mata kagano ta fad'a tayi zuru zuru da ita.

Baffa yaja numfashi yana duban Dr. Bilyamin yace "Doctor me ya kawo afkuwan ciwon?"

Ya amasa "Wallahi Baffa mudai jiya da dare ne... duk yasanar dasu abinda ya afku daren jiya sannan ya d'ora da cewa  to shine da subahi alluran danayi mata ya saketa har tasamu tayi wanka tana shafa mai sai ta sulale k'asa ba alamar numfashi, shine nayi gaggawan zuwa da ita hospital muka duk'ufa akanta da kyat mukayi nasaran daidaituwan bugun numfashin yadawo normal."

Mummy tace "Ya ilahil alamina, kabawa baiwarka Hauwa'u lafiya domin Alfarmar Annabin ramaha S.A.W"

   "Amin." suka amsa.

Baffa yakuma cewa "To kunsami ita yarinya dasukayi wayar da ita jiyan don jin me ta fad'a mata da zafi wanda har yayi sanadiyyar jefata cikin wannan halin?"

  "A'a Baffa ba musami sukunin nemanta ba."

"Ok bani number inji ko zansameta ni."

"Sai dai ajira Fatie su k'araso sai a amsa don ni bani da ita."

"Ga mai ita nan zaune har sai anjira zuwar wata, oya Hakeem kiramana ita muji."

Mummy ta  umurceshi.

Batare da yayi magana ba yasoma neman layin Zainab amma wayar akashe take har yanzu sai kawai yayanke shawaran bari ya kira na Ameen yaji.

Yunus ne zaune gaban mamansa yana koro mata bayin rashin lafiyan mamie.

BANYI ZATO BADonde viven las historias. Descúbrelo ahora