page 6

670 35 3
                                    

*9 to 10*

Sallamar Abdul Hakeem yasa Baffa yadakata da kai kawon da yake yi.

Amsawa yayi tare da nunamishi wuri yana mai cewa "Zauna." Bayan ya zauna ya dubi Baffan cikin girmamawa yace "Gani Baffana da fatan lafiya ko?"

Matsowa Baffan yayi sannan ya zauna a kujeran dake kallon wanda Hakeem din yake zaune.

"Tambayarka zanyi." yace da Abdul Hakeem.

"Inajinka Baffa." ya amsa a hankali.

"Wadanne mata ne d'azun suka dawo tare da ummanku?"

Kai tsaye Hakeem ya amsa "Hajiya Jidda ce tare da mummy."
  Ya d'ora da k'arin bayanin.
"Hajiya Jidda, hajiyar ummanmu ce shugaban gidan marayu, aika santa ko?"

Cike da gamsuwa Baffa ya amsa "Eh nasanta."

   To d'ayar kuma fa wacece ita?"

   "Mummy ce wato hajiya Fiddausi, ita kuma k'awar umma ce ko ince aminiyarta na k'ud da k'ud."

  "Ok dama tambayana akanta ne."

"Tam Baffa Allah yasa na sani."

"Insha Allah, shin 'yar wacce gari ce ko itama a gidan marayun take?"

"A'a 'yar garin zariya ce, bata da jibi da gidan marayu sam sai dalilin Umma. Domin a dalilin umma ta maida da gidan marayu tamkar gidanasu, domin umma ta fad'amin wata rana har kwana takeyi a gidan duk sabida shak'uwarsu da juna."

   Jinjina kai Baffa yayi sannan yace "To aina suka had'u?"

"A jami'a lokacin umma tana shekaran farko ita kuma ta na biyu."

"Yanzu aina take da zama?."

"Tana zaune a malali gidan mijinta wanda yarasu kimanin shekaru goma da doriya, yabarta da yara uku dukan su mata."

"Allah sarki, Allah yaji k'ansa da rahama."

"Amin."

Sai kuma Baffa yayi jim na d'an lokaci sannan yace "Yaran nata 'yan shekaru nawa ne?"

"Twins ne yaranta na farko 'yan shekaru ashirin da uku da watanni sai gambonsu ita kuma sa'ar mamie ce ita kuma sherunta ashrin da kusan d'aya.

Shiru Baffa yayi ya fad'a kogin tunani, cikin zancen zucci ke tambayar kansa 'Shine to ina cikin da nabarta da shi? Ko ta zubar ne kamar yadda tafad'amin sanda nak'i amsan batunta alhalin nasan nawa ne.'

Wani shashi na zuciyarsa ya amsa 'Kai bazata aikata sabon Allah ba ta hanyar kisan rai.'

Wani kuma ya amsa to inhaka ba ina labarin d'anka ko d'iyarka? dan cikin yaranta ba wanda ya kai shekarun da zaka ce naka ne.'

Wad'nnan sune tambayoyin da yakeyiwa kansa cikin zuciyarsa tare da amsa mara madogara.

Kallonsa yasauke bisa Hakeem wanda yazuba tagumi ya kafeshi da idanuwansa masu girma irin na Baffan sak, don Hakeem yafi kama Baffa sosai akan Abbansa shiyasa Baffan yake tsananin ji dashi ainun.

Samun kansa Baffa yayi cikin matsanancin jin kunyar yaron tamashi don gani yake kamar yasan abinda ya aikata na son rai a shekarun baya wanda yanzu kimanin shekaru talatin kenan da afkuwan k'addarar ko ya ce son zuciya.

"Baffa wani abu tayi maka ko?" Yatl tamayeshi cikin sanyin murya.

Girgiza mishi kai yayi.

"Baffa to don Allah inma wani abu tayi maka narashin kyautatawa  ina nema mata affuwa akai.
Sabida wallahi inajinta araina fiye da tunanainka, ita din mace ce mai nagarta tare da hakuri, ta kula da mu sosai musanman Ummanmu, gashi itama abin atausaya matane domin iyayenta duk sun rasu, dangin babanta kuma sunyi watsi da ita sakamakon matar babanta da tashiga tafita tarabasu da ita sannan kuma dangin mamanta sunyi mata nisa suna Sudan,  ba ko yaushe take ganinsu ba sai lokaci lokaci, jin dadinta d'aya dangin mijinta suna sonta da k'aunarta sosai, sund'auke mata kewan 'yan uwanta da tarasa gatansu."

BANYI ZATO BATempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang