page 15 to 20

940 38 1
                                    

Banyi zato ba
Mrsjmoon

*15 ~20*

K'amshinta ya ankarar dashi isowarta.
Sallama tayi mishi cikin muryanta mai dad'i cikin sanyi.

Cike da wata yaudararriyan murmushi ya amsa mata. "Waalaikis salam 'yan mata adon gari in ba ku ba gari in kun yawa gari ya b'aci." Sai kuma ya yi saurin kama bakinsa  yana girgiza kai.

Sosai taji guy d'in yayimata, gashi da son hara. Murmusawa tayi  batare da tace komi ba.

Shima haka yaji ta burgeshi 'Ba dan ogansa yana tsakani ba tabbas da yasami matar aure duk da ba aure ne yanzu a agabanshi ba.'

"Ya kake zaune kai d'aya ko kunsami matsala da Qeen d'in taka ce? Maganarta yadawo dashi duniyar tunanin da yafad'a.

"Uhmm nibana da budurwa ai." Yace da ita yana wani kashe mata idanu.

"Kai haba?"

"Ai aka abin yake mai kyau."

"Lallai kam ka huta abinka."

"Haka kike gani?"

"Eh man kahuta da tunani mai hana mutum barcin dad'i musanman in kunsami matsala."

Dariya yasa sosai,
tabishi da kallo tana mamakin komi yabashi dariya cikin zancenta oho.

Gabansa ne yafad'i sanda takeyi mata kallon k'urullah, sabida yagano kamanninta da yayi da ogansa.

'Shiko oga me k'anwarsa tayi masa da yake k'ok'arin keta mata mutunci? Tabbas lallai wutan irin su oga daban/ne a jahannama.
Tabd'ijan, to kodai idanuna ne keyumin gizo? Wai shin me ma tayi masa da zafi? Wata k'ila cewa yayi yana sonta tace a'a.'

Sabida yasan kadan ne daga cikin  aikinsa ya sace duk yarinyar da yace yana ra'ayinta tace batayin shi, to inba ikon Allah sai ya sace ta yayi mata aika aika ya barta da dana sani.

Cikin zuciyarsa yake ta zance yana jinjinawa ogansa da halin dabbobi irintasa.

"Tunanin mika keyi kai da baka da budurwa?" Ta katse shi daga tunanin da yafad'a.

Ajiyar zuciya  yaja tare da cewa "Ke nake tunani domin a 'yan seconds har kin sacemin ruhina."

Bud'e idanunta tayi sosai sai kuma tasa 'yar k'aramar dariya tace "To ka amshe abinka tun wuri sabida baza tayimin amfanin komi ba."

"Sabida da mekika ce hakan?"

"Sabida bana da wurin ajiyeta ko dai dai da hudin kan allura ce."

Shiru yayi yakafeta da idanunsa masu d'aukan hankalin 'yanmata.

Cikin jin kunya kallon dakeyi mata ta rufe fuskanta da tafukan hannayenta.

  Zara zaran yatsunta yabi da kallo yana lasan labba.

"Tabbas oga zai kwashi gara anan kam, gata doguwar mace ni'imar maza, dama ace zai bani in d'an d'ana, aiko dana morewa rayuwata."

"Me kake cewa?" Duk sai ya daburce domin bai zaci afili yake zancenba.

"Cewa nayi ... ki.. na.. da..

"Dakata!! Malam."
Ta fad'a cikin tsawa.

"Kada karainamin wayau, waye oganka da ya aiko ka sace ni?" Sai ya kuma daburce yasoma kame kame yana inda-inda.

"Ba.. ba.. wanda.. ya.. aiko.. ni Allah ..kuwa nazo.. tayaku ..mur...na..ce.

Harara ta watsa mishi tace "Ina hankalce da kai tun d'azun duk inda nabi idanunka na kaina, don haka banyarda da kaiba kuma baza kabar wurin nan ba sai ka kira oganka yazo."

BANYI ZATO BAOù les histoires vivent. Découvrez maintenant