Banyi zato ba
Mrsjmoon*64*
Mamie rasa me ke mata dad'i tayi shine yahaifar mata da jin fad'a tare da kuka.
Har zuwa magrib tana kuka kuma tak'i fad'awa Hakeem abinda ke damunta sannan yace su tafi asibiti taqi yarda domin itama kanta bata san me ke damunta ba.
A haka ya lallab'ata tasha tea, tayo alwalla ta zauna don gabatar da sallar magrib, shi kuma yafi ce zuwa masallaci.
Ana idarwa ya wuto baiko jira an sallaci isha'i ba.
Tana zaune saman sallaya hannunta d'auke da k'aramar AL-QUR'ANI. Tana karantawa cikin zuciyarta.
Zama yayi gefenta tare da tsura mata idanu, sai da takai kan aya a cikin suratul Namli sannan tatsaya tare da yin addu'a mai tsayi suka shafa tare.
"Princess ya jikin, hope bakyajin ciwon komi?"
Harara ta doka masa ta kauda fuska gefe, kamar bataso ta bud'e baki da kyar tace "A wara nakeson ci kuma wanda baida kayan alatu sosai, atak'aice dai irin wanda ake soyawa nan akan layi ko cikin unguwa nake buk'ata kuma yanzu sannan mai zafi sosai wanda zai k'onamin harshe in inaci kuma kada asoyashi sosai, sama sama nake buk'atarsa."
Idanu ya zaro yana duban agogo yaga yanzu k'arfe 7:25pm yace "Mamiena awannan lokacin yaushe za'asami wani awara, don Allah kiyi hak'uri zuwa gobe in Allah yabamu aron rai sai innemo miki."
Baki ta b'are tana kuka kamar wacce aka tsinkawa mari. "Nidai yanzu nakeso sai dai inbaza kaje ba kawai kafad'amin sai inkira Ummana ta samomin a kusa dasu."
Hannunta ya kama cikin sigan rarrashi yace "Bari inje na samo miki, please ki bar kukan haka nan matata abin alfaharina."
Tura baki tayi tana jan hanci cike da shagwaba tace "Tam kayi maza ka kawomin don jinake kamar inci babu."
Miqewa yayi ya d'au mukullin motarsa yana cewa "Bani mintoci goma mmn twins."
Daf da fita layin ya hango mai soya awara mutane sun lullubeta, parking yayi agefe ya k'arasa wurin, ganin da layi sai yabata kud'in tare da yimata bayanin yarda yakeson asoya, yakoma cikin motarsa ya zauna.
ba'a jimaba mai awaran takawo mishi har inda yake tare da canjinsa, awaran ya karba yace ta rik' canjin ya gode.Koda ya dawo har tasoma barci, k'amshin awaran ya tada ita, jiki na rawa ta jawo ledar ko juyewa a plate bata tsayayiba ta hauci saida tayi k'oshi sannan ta dubeshi tace "Bissimillah."
Girgiza kansa yayi alamar bazai ciba, tab'e baki tayi tace "Kahuta kam."
Ture ragowar tayi gefe tace "Godiya dubu yayana, Allah yabarmu tare da juna cikin amincisa."
Ya amsa "Amin, sai me kikeso kuma?"
"Babu barci nakeji."
"Ok to muje kiyi wanka."
Kama hannunsa tayi suka shige bedroom.
Ciki dare ciwo ya hana Mamie barci tayi ta daurewa tana son yin jarumta, ganin abin yasoma fin k'arfinta tasoma kiran sunayen Allah, cikin ikon Allah lokaci kad'an barci ya kwasheta.
Hakeem kam yana can d'akinsa, nafila yakeyi kamar yarda yasaba yi dukkanin dare.
Sosai yayiwa mamie addu'a na Allah yasauketa lafiya ya kawo mata haihuwa cikin salama. Sai misalin qarfe uku na dare ya idar ya sanza kaya zuwa na barci ya nufo bedroom d'inta.Nishinta tare da salatin datake ja sukayi masa maraba cikin kunninsa.
A kid'ime ya kunna full light ya hangota durk'ushe saman guiwoyinta sai zufa takeyi kamar ba AC a d'akin.
Jikinsa ba inda baya rawa ya kamota ya rungume yace "Mamiena me ke miki ciwo?"
K'am k'ameshi tayi tana kiran "Ummanmu yaya kiramin ita mutuwa zanyi dan Allah kace tayafemin, ashe haka taji, washh! Allah bayana, cinyata, marata, ya ilahil alamina, ya Allahu akbar kabiran Ah!! Yaya katai makeni zan mutu wayyo Dada!"
Miqar da ita yayi tsaye takasa tsayuwa cak ya d'auketa ya nufi parking lot da ita, ya kwantar da ita a back seat yayi ya ja motar da gudu.
Mahaukacin horn d'insa ya tada mai gadi daga barci agigice yafito ya bud'e masa get yafice kamar zai tashi sama.
Safa da marwa yake yi yana jan sunar Allah, duk ya had'a zufa kamar shi ke nak'udar.
Fitowan doctor Bahijja daga Labour room yagani ya nufeta da hanzari yace "Ya dai doctor? Ta haihu kuwa?"
Girgiza mishi kai tayi tare da mik'a mishi takarda tace "Sa hannu a nan zamuyi mata cs ne sabida bazata iya haihuwa da kanta ba sakamakon k'arfinta da ya k'are sannan tasoma zuban jini bama son rasa ta da yaran."
Hannunsa na rawa yayi signing.
Yana nan tsaye aka turota kamar matacciya zuwa theater room.
Bayansu yabi har suka shige da ita yaja baya ya buga kansa jikin ginin yana matsan kwalla "Allah yasa ayi asa'a kibfito lafiya Mamiena."K'arfe biyar da mintoci goma na asuba aka kuma turota zuwa d'akin hutu.
A tare suka isa cikin d'akin da nurses da suka turota.
Bayan sun shimfid'eta suka gyara mata drip d'in dasu sa mata suka fice.
Zama yayi baganta ya tsura mata idanu cike d tausayi, tak'ara haske fuskanta tayi 'yar fiyat, ya kai hannunshi ya dafa goshinta yana yi mata addu'ar samun sau'i.
Doctor Bahijja ce tashigo tare da wata nurse d'auke da babie cikin kayan sanyi farare sol an nad'esu a cikin showel pink.
"Congratulations Mr. Hakeem."
Dr. Bahijja ta fad'a fuskanta d'auke da murmushi.
Gyad'a kansa yayi tare da motsa bakinsa kad'an ya amsa "Thank you doctor."
Mik'a masa yaran sukayi, ya zare idanu yana duban doctorn cike da son jin k'arin bayani.
"Yaran kane yallabai, gasunan boy and girl masu d'auke da cikakken qoshin lafiya, Allah yarasu ya kuma bawa mamansu lafiya.
Bakinshi na rawa ya amsa "Amin ya rabbi."
Yaran ya rungume a jikinsa yanajin madarar son tare da k'aunarsu yana kwarara acikin jini da jijiyar jikinsa.
Kiran sallah yayi musu acikin kunnuwansa tare da ji musu hud'uba, sannan ya ja addu'a ya tofesu dashi ya kuma rungumesu yana kallon fuskan mamansu cikin matsanacin murna ya furta "Allah yayi miki Albarka Hauwa'u jidda, Allah yabaki lafiya mai nagarta ya kuma baki juriya wurin shayarwa tare da tarbiyyansu."
Shinfed'esu yayi a gefenta yashiga toilet ya d'auro arollah yasami wuri mai tsafta ya shimfida d'ankwalin ya gabatar da sallar subahi, koda ya idar sai yacigaba da azkar har gari yayi haske yadawo ya zauna ya sasu agaba yana aikin kallo yana murmushi kamar yasami tv.
7:00am doctor Bahijja ta shigo ta k'araso ta duba Mamie ta dubi Hakeem tace "Tana daf da farkawa k'ila zuwa nan da 8, ni zan wuce gida sai bayan azuhur zan dawo naga ya jikn nata yake."
"Tam doctor nagode Allah saka da Alkahiri."
"Amin, Doctor Bilyamin yanzu zai k'araso, Allah yabata lafiya."
"Amin."
Har tafita ta dawo tace "Kafad'ama mutanen gida kuwa?"
Girgiza kansa yayi "Na manta wayoyina a gida amma dazarar Dr. Bilyamin ya iso zan sanar dasu ta wayarshi."
Shigowa tayi ciki ta miqa mishi wayarta tace "Kirasu yanzu da tawa."
Amsa yayi yasa number Umma yasanar da ita bayan yagama ta amsa wayarta ta fice.
Bayanta yabi da kallo yana jinjina kirki irin na Doctor Bahijja, bayan kyautar sabbin kayan sanyi da ta sayawa yara har kuma da aron waya ta bashi. "Kai Allah yayi ta kwararowa rayuwarki Albarka Dr. Bahijja."
Yana nan zaune mummy tare da Baffa suka iso, kafin 8 d'akin yacika da dangi sai sambarka suketayi tare da yima Mamie da babies addu'u,o'i.
BINABASA MO ANG
BANYI ZATO BA
General FictionBayan gamayin dinner d'insu suka balle da hira, sosai suka tattauna da juna a inda Hakeem yayi ta bashi baki akan yazamo mai yarda da qaddara abisa laluran data sameshi. Yunus cike da annashuwa yayi ta godiya game da kulawansa akan laluranshi ganin...