page 11~12.

696 30 2
                                    

Banyi zato ba

Mrsjmoon

*11 to 12*

Horn yake zabgawa malam Lawwali mai gadi amma shiru baida alamar zuwa yabud'e masa gate d'in.
Cikin fusata ya bud'e motar ya fito ya tura k'ofar d'akin malam lawwalin yaga wayam bakowa ya ja wani uban tsaki ya fito ya bud'e gate da kansa yana ta zabgawa  mai gadin zagi kamar goyon maguzawa tare da aiyana rashin mutuncin dazaiyi masa gobe in sun had'u.

Ihunta da kururuwanta yaja hankalinsa ya dakata ya fito ya tsoge yana kallonta, cikin ransa yana tunanin 'Shin ko itama maman ta samu nasarar haukata ta ne?'

  Wani cutama da tayiwa gaban rigarsa shi ya dawo dashi daga tunanin da yafad'a.
 
Fad'itake "Tanbad'ad'de irin Allah wadai, wanda ya tsotsi rashin imani a nonon uwarsa, haihuwar gara ba ayiba, wanda aka haifeshi tsiya na zamanin fitsaranta, fitomin da jikata  d'iyar Albarka ko intujaraka yanzu."

Ak'ufule ya fizge riqon datayi masa yana auna mata kallon banza yace "Wani zancen iska kikemin haka Dada?"

"Uwarka ce ke zancen iska kaji ko, d'an Allah wadai.

  "Dada ya isheki tsinemin kada kisa na lalace."

"Lalacewa na nawa kuma tunda har ka iya satan mutane zaka sayar."

"A'uzu billahi!! Ya furta idanunsa waje.

"Akan ka zai fad'a a'uziyyan ba, mara tunani kawai."

Banza yayi mata ya bud'e matarsa zai shiga, ta fizgoshi yayo baya ba shiri ta sa hannu ta wankeshi ta mari ya zare idanu yana kallonta, tana haki tace "Koza karama ne?" Girgiza kai yayi tare da cije labbansa ya soma tattare hannun rigansa, ya d'aga hannu zai nausheta.

Kai!! Kul nace Yunus!!.

Ya sauke hannun a asanyaye yana mai sunkuyar da kai.

"Dakabarshi ai umaru ya dokeni kaga da nayi alfaharin cewa jikana yabani tukuicin haihuwar ubansa da nayi."

"Dada kiyi haquri don Allah kinsan ba hankali ya cikaba."

  "Eh na gamsu baya da cikakken hankali tunda gashinan ya fesawa 'yar uwarsa abin mutuwa zai fice da ita ya sayar ko ya aikata mugun... sai kuma tayi shiru ta k'ara cukume Yunus tana fesa masa bala'i.

"Wai ni Dada minayi miki ne kike son lak'amin sharri da yammacin nan?"

Tana rik'e dashi tace "Umaru ka umurcesa ya fiddomin da takwarata daga cikin motarsa tunkafin in kira masu babbak'un kaya."

Hak'uri Baffa yayi ta bata sannan ta saki ma Yunus riga tare da hankali d'ashi ya bugu da motar.

"Kai bud'emin bayan motarka dan najiyo k'amshin turare ciki."

  "Baffa wallahi bakomi ciki sharri kawai dada takemi... Tass!! Baffa ya wankeshi da mari cikin fushi ya tureshi gefe yana fad'in "Mahaifiyar ta wa ce zatayima sharri don tsaban fisara irinta ka."

Yabud'e sit d'in baya da kansa.

Arazane ya juyo yana kalkon Yunus wanda zufa da tuni yagama wanke masa fuska gawani firgici daya bayyana akwayan idanunsa.

Dada kam salati take ta rafkawa tana tafa hannaye cewa take "A she da gaskene abinda malam lawwali yazo yafad'amin? Allah kayi wadaran gantalallen yaron nan, ka wulak'anta shi."

Baffa number police yayi dialling bawanda ya lura da hakan cikin Dada da Yunus sundaiji yace "Eh a gidana inajiraka yanzu."

Ganin Yunus yana son gudu yasa yayi saurin kamoshi ya riqe tamau yasoma kaimishi duka da k'afa.

BANYI ZATO BATempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang