Banyi zato ba
Mrs j moon.*45 to 48*
Cike dajin kasala mamie ta mik'e tasoma zagaye gidan har cikin garden sai da ta shiga wanda wurin yayi matuk'ar burgeta domin cike yake da shuke shuke masu kyau da tsari can daga gefe kuma ruwane mai kyau yake ta gangara kamar k'aramin kogi, k'ananun duwatsu ne gewaye da ruwan sunyi kyau.
a wurin ta zauna ta saka k'afafunta ciki tana wasa dasu, nushad'i mara misaltuwa takeji yana kwarara a birnin ruhinta.
Idanunta lumshe tana shak'an k'amshin furan nin da suka ke waye garden d'in, ta tsinkayi k'aaran wayarta.
Bud'e idonunta tayi tana duban screen d'in wayar.
Tabe baki tayi sannan ta d'auka tayi shiru.
Cike da jan magana Sady tace "Dallah malamansu baki iya sallama bane tare da mik'o gaisuwa zuwa ga addarki?"
D'an tsaki taja tace "Kinga banson iskanci, waye addar tawa?"
Dariya tasaki ta amsa "Gani bisa layi ina sauraren jin gaisuwar girmamawa daga gareni."
"Zako ki mutu ba agaisheki ba kam indai jiranta kikeyi."
"Jimin muguwa dai to bakinki ya sari bishiyar gidanki, bazan mutuba sai naji d'umin jikin my Honey Isma'il."
Murmushi Mamie ta mik'e ta nufo parlor tana cewa "Ai kekam kinboni da rashin munya inajin ke zaki nemesa."
"Naji dai komi zakice kiyi ta cewa nasan nan da anjuma kema zakiyi bulum buk'ui jikin brother Hakeem domin masu shiru-shuri d'in nan sunfi kowa zalama."
Kanbu amma Sady kekam ba k'aramar 'yar air bace, to kirubuta ki ajiye ni da da brother zaman yaya da k'anwa zamuyi, ko hannuna bazai taba."
Dariya cike da k'arajj ta sanya wanda saida mamie ta cire wayar a kunninta tare da kashewa tana fad'in
"Wallah Sady bak'aramar tantiriya bace, tayi ta sakin baki tana zuba zance kamar wata suda."
Kiran Imranat yashigo wayarta ta d'auke tare da sallama amsa mata imranat d'in tayi cikin sanyin murya.
"Sis har kinfara kewar gida ko?"
"Uhmm kedai bari kawai Mamie ganinan zaune nakasa motsawa ko nan da can, gidan duk yayimin girma gashi Dada ta caza mana tasa ankora mana k'awayen daza su d'ene mana kewa kafin dare yayi."
"Ai wallahi sis Dada batayi ba sam, gabaki d'aya ita burinta ta takurawa muta ne, ga uwar jaraban fad'a kamar mai aljannu."
Dariya Imranat takeyi "A'a sis aiko Dada bata fad'a saida dalili, inkinji tana tsiya to antaba tane."
"Aydama ke Dada bata laifi awurin sam, ko don kinga kinfi zubi da ita ne oho."
Nanma dariya Imranat takuma sawa tana fad'in "Banda sharri dai mamienmu matar big yayanmu mai abin mamaki."
Had'a rai tayi "Au tanan kika dawo to sai anjima da neman maganarki."
Ta datse kiran tana bin wayar da harara kamar Imranat d'in ce.
Imranat kam dariya tacigaba dayi ta furta "A lallai na yarda da zancen Sady data ce Mamie sifafuka ce domin tana matuk'ar son brother Hakeem amma tana likimo."
Mamie kam alwalla ta yo tagabatar da sallar magrib tazauna a wurin tanayin azkar har lokacin isha'i yayi ta gabatar ta d'ora da shafa'i tare da wutri tayi addu'a mai tsayi sannan ta fad'a bathroom ta had'a ruwan wanka ta zuba turarukan wanka masu k'amshi tasulle jikinta lungu da sak'o sannan tafito tabata lokaci gaban mirror tana kyalliya ta mulke kowanni sak'o na jikinta da had'in humra d'an barno, wannan kyautane daga k'awarsu Fatima kaka malam ta kawo musu.

YOU ARE READING
BANYI ZATO BA
General FictionBayan gamayin dinner d'insu suka balle da hira, sosai suka tattauna da juna a inda Hakeem yayi ta bashi baki akan yazamo mai yarda da qaddara abisa laluran data sameshi. Yunus cike da annashuwa yayi ta godiya game da kulawansa akan laluranshi ganin...