Banyi zato ba
*5 to 6*
Da k'arfi ya tura qofar parlorn ya shiga bako sallama turus yaja ya tsaya take kuma gabansa ya yake ya fad'i sakamakon arba da yayi da Abdul hakeem zaune yana duba wani kittafin addu'o,i.
'Daure fuska yayi tamau ya watsa mishi wani mugun kallo murya a shak'e mai cike da izza yace "Kai mahaukacin inane? dazaka shigo mana haka bako sallama don tsaban dak'ik'anci tare da jahilci."
Yunus ya rasa bakin magana hasalima baiji mai Abdul hakeem kefad'a ba sabida matsanancin rud'anin da yashiga donshi baitaba kawo tunanin zaik'ara ganin Abdul hakeem ba arayuwarsa sam, azatonsa tuni ya dad'e da barin gidan ya shiga uwa duniya su da had'uwa dashi sai kuma a darul salam insuna da rabon ganin juna amma sai ganinsa yayi zaune cikin k'oshin lafiya.
Yarda malaminsu ya fad'a masu indai sun binne layar a bayan d'akinsa to sai dai labarin waninsa amma ba dai shiba, amma abin mamaki sai gashi zaune daram.
Tsawar da yadaka masane ya dawo dashi hayyacinsa cikin kid'ima ya juya zaifice sai ya hango mamie zaune tana shan tea ya dawo da baya ya nufi wurinta tanaganin ya nufota ta miqe ta nunashi da yatsa "Wallahi ka kuma gigin tabani sai na illataka." Ta d'auki wata k'aramar wuqa ta riqe da kyau tana kallonsa.
Cije labbansa yayi tare da kad'a kai yace "Had'uwarmu akaro nabiyu bazai yi miki dad'iba yarinya don billahil azim sai kin gwammace mutuwarki da rayuwarki.
"Kai!! zo kawuce tunkafin in soma ball dakai." Abdul hakeem yace dashi cikin tsawa.
Wani uwar harara ya watsa masa sannan ya matso daf dashi yace "Kadaina dakamin tsawa kamar wani ubana, kuma inason kariqe aranka ni Yunus nine sanadin lalata wancan k'anwar take 'yar mahaukaciya jikan gidan mara....bai k'arasaba yaji saukan mari dama da hagu akid'ime ya ja baya yana shafa fuskansa cikin matuk'ar fushi yace "Wallahi sai nayi sanadin bacewarka a duniyar mutane." Ya kuma juya sashin da Mamie take zaune yace "Ke kuma ni ne sanadin budurcin ki da kike tink'aho dashi don sai na maidake mai yoyon fitsari."
Yana rufe baki ya kumajin naushi kan bakinsa ya saki k'ara yana shafa bakinsa yaga jini bai kai ga magana ba yakuma jin naushi da bugu ta ko ina yasoma kare kansa amma ina k'arfin ba d'ayaba ne ganin in ya tsaya Abdul hakeem zai iya yi masa illah yasa ya kwasa da gudu ya fice yana fad'in "Allah ya isa mugu kawai d'an masara kuma wallahi ni ne sanadin ku kai da ita."
Wata dariya Mamie tasa hartana rik'e ciki.
Harara Abdul hakeem ya watsa mata ta tsadai da dariyan tana tura baki sai kuma ta k'ara saka dariya yako yo kanta ta kwasa da gudu tana kiran "Abba! Abbana!!.""Na'am mamana me ki ka mishi?"
Abban yace yayin da yashigo parlorm dan gabatar da breakfast.
Boyewa tayi bayan Abba ta amsa "Shi ne zai dokeni don kawai inayin dariyan Yunus da yace masa mugu d'an masara."
Murmusawa yayi tare da rik'o hannunta suka nufi dining.
Zama sukayi dukkansu suka gaishe dashi ya amsa cikin kulawa sannan ya dubi Abdul Hakeem yace "Me yahad'aka da Yunus yarona?"
Shiru yayi har sai da Abban yakuma tambayarsa sannan ya fad'awa Abba abinda yahad'asu bai rage masa komiba.
Fad'a sosai Abban yayi masa sannan ya d'ora da cewa "Kada ku saka damu da wannan soki burutsin zancen nasa kudai kuzamo masu yawan aikin alkhairi da adduar neman tsari daga duk kan wani abin damuwa sannan da yardan Allah ba abinda zai sameku, kuma daga yau banson in k'arajin kahad'a k'ashi da Yunus gudun d'ebo tsiyar da ya tsotsa."
"Tam Abba insha Allah zan kiyaye."
"Good hakan shi yafi, Allah yayi muku albarka."
"Amin." suka amsa a tare.
ŞİMDİ OKUDUĞUN
BANYI ZATO BA
Genel KurguBayan gamayin dinner d'insu suka balle da hira, sosai suka tattauna da juna a inda Hakeem yayi ta bashi baki akan yazamo mai yarda da qaddara abisa laluran data sameshi. Yunus cike da annashuwa yayi ta godiya game da kulawansa akan laluranshi ganin...