page 69 to 70

189 9 1
                                    

Banyi zato ba.
Mrsjmoon.

*69 to 70*

A gigice ya rik'e kafad'unta yana jijjigawa tare da cewa "Mamiena me yasameki? Me naja miki?  Bakin me Dadanmu tayimiki?"

Banza tayi masa tacigaba da kuka kamar yarinyar goye.

Rungumeta yayi hankalinasa atashe, yasoma shafar bayanta zuwa sumar kanta. K'okarin kwacewa takeyi amma takasa, sai ta hakura ta kwanta lamo ak'irjinsa tana sauke numfashi.

Tsawon lokaci suna a haka. Sai da yaga tasami nutsuwa sannan ya d'agota ya tsura mata idanu.

Lallai ta d'an rame kuma ta qara haske sai fuskanta data tasa kad'an cike da sha'awa.

Jan numfashi yayi yana murmushi jin dad'i na wani hasashe da ya d'arsu cikin zuciyarsa, cikin murna ya sauke mata kiss abisa goshinta, lumshe idanunta tayi ta bud'e ta doka mishi harara.

Cije lips yayi ya girgiza kai sakamakon jin son kasancewa da ita da taso masa cikin gaggawa.
  
Idanunsa yasoma shigarwa cikin nata yana latsa tafin hannunta tana  jin haka ta batarai tare da zamewa daga jikinsa tana shirin sauka daga saman gadon. A hanzarce ya maidata ya kwantar tare da d'ora mata nauyinshi.

Cikin miryan kuka tace "Yaya kasanfa bana da lafiya, kana gani yanzu nagama amai."

Bai tanka ba yamirgina yakoma da ita samarsa ya rungumeta yana aiki sauke numfashi.

"Princess baki amsamin tambayoyina ba."

Tura baki tayi ta had'e rai, ta kauda kanta gefe sannan ta amsa "Kaine kahani sukuni da jaraba wanda ya haifar da fad'awana cikin halin rashin lafiya abinda nayi imani ciki nake d'auke dashi domin watana biyu kenan banga period d'ina ba, kuma dama maganar Dada kenan kullum dazarar naje gida ita tak'osa taganni ina amai mayi ko su Haneef sa dawo wurinta, to gashinnan burinku kai da ita yacika ai."

Wani k'aran murna yasaki yasauko rungume ta ita ya sauke qasa ya zaunar shikuma ya durqusa bisa guiwoyinsa ya d'aga hannayensa sama yana mai cewa "Allah nagode maka. Allah yarayamin abinda ke cikin matana. Allah kasauketa lafiya. Allah yayi albarka ga zuri'ata tare da na dukkanin al'umman musulmi."

Ahankali ta amsa "Amin."

Ya janyota suka zauna bakin bed ya dubeta cike da murna yace "Kai amma nagodewa Dadanmu data tayi miki bakinan, gashi nasamu cikan burina na kuma samun k'ruwar arziki."

Duka ta kai mishi idanunta yataru da ruwa suna daf da zubowa.

Girgiza mata kai yayi yace "A'a mamie kibar kuka don Allah."

Cikin tsiwa ta tari numfashinsa "Dole inyi kuka Abbien twins,  domin har yanzu ban manta wuyan danasha wurin haihuwar su Haneefa ba, nasani ko wannan ma cs za'a sakeyi min ko kuma wata wakila bazan rayuba, ajalina ne yazo."

"Subbahanallahi Mamie meye yakawo maganar mutuwa kuma? Shin wake rayawa da kashewa?"

Ta amsa "Allah."

"To indai kinyi imani da hakan, don Allah kada kikara zancen nan."

"Uhmm Yaya nidai kasan yarda za'ayi da cikin nan kawai."

Tsareta yayi da idanun yace "Kamar yaba?"

Sunkuyar da kanta tayi kasa tace "Kaga su Haneef shekaransu d'aya da wata uku basu isa yayeba, sannan in su Sady sukaji inada ciki tsiya zansha wurinsu kamarme kuma gaskiya ni banshirya sake haihuwa yanzu ba."

  Fuskansa a had'e yace "Uhm ina saurarenki, me kikeso ayi yanzu?"

Cike da jin tsoro taja baya nesa dashi sannan tace "Azubar dashi, tunda bai zama halittaba."

BANYI ZATO BAWhere stories live. Discover now