page 2

1K 56 0
                                    

*Banyi zato ba.

*02*

Suna shiga part d'in ta fad'a samar kujera ta dafe goshinta cikin furta "Washhh!! Allah Brother nagaji."
Baii kalleta ba ya amsa "Baki gajiba yarinya sai na zaneki tukunna."

"laifin minayi?"

Ya yi mata banza ya matso ya sunkuya ya kama kunnenta ya murd'a tasaki ihun azaba tana yarfe hannu take hawaye yasoma bin fuskanta ganin haka yasa ya saketa yana gabga mat harara, ta tura baki furta "Wallahi Brother ka iya cin zalin."
  
Harara yaqara watsa mata sannan ya soma magana Mamiena Allah in baki watsi da sabbin d'abi'un nan dakika k'irk'iroba tsakanin jiya da yau, to zamusa k'afar wando d'aya dake."

  Tana liliya kunninta, ashagwabe ta dubesa "To ni kam Yaya minayi wai?"

"Rashin jin magata tare da rashin kunya da kikewa mama."

Sai da ta tabe baki sannan tace "Au wai akan mama ce kake murd'emin kunni? To wallahi sai dai ka kasheni amma na k'udiri aniyar wanke duk wanda yayi k'ok'arin tabamin Umma, ko da kuwa Dada ce bazan kyaleta ba balle kuma ace d'an k'wayarcan ne da uwarsa iyayen masifa."

  Shiru yayi yana kallon yadda ta dage tana ta zuba bako jan numfashi.

"Mamiena wai yaushe kika koma  haka? mara tsoro da tsiwa."

Ta sunkuyar da kai k'asa tana jan hanci sabida kukan da takeyi.

  "Uhm to yayi miki kyau tunda ban isa dakeba sai kiyi duk abinda kikaga dama amma kisani bazan tare mikiba in sunji miki ciwo nadai kai ki chemist."

Tura baki tayi tamik'e fuw! tashige d'akinta tana cewa "Allah yabaki lafiya ummata kidawo kizamemin garkuwa tunda wanda nake gani kamar ke yagaza kulawa da ni gashi nan har fatan mugun abu a sameni yakeyi."

Bayanta yabi da kallo ya wani had'e rai yana maijin kamar bai kyauta mata ba 'Amma ai yazama dole in nuna mata girmama babba musanman ma Dada datake matsayin mahaifiyar Abbansu.' Ya ambata cikin ransa.

Tana k'ok'rin shiga wanka ya turo k'ofar d'akin ya shigo taja ta tsaya tana wani bata rai. Shima rai ya had'e wanda sai da ta tsorata taja baya da sauri.
 
"Fito ki d'ora mana wani abu don kinsan ko breakfast bamuyiba har yanzu."

Cikin marairaiata tace "Dan Allah D'an uwa ka sayo mana takeaway."

"Ank'i siyowar, kifito ki yi mana abinci kuma mai dad'i kindaiji na fad'a miki."

"Wallahi bazan iya dafa komi ba Yaya hakeem, kaina ciwo yakemin tare da cinyata har da marata kuma ga shi zuciyata tak'i yimin dad'i sakamakon ganin ummanmu da nayi."
Saita saki kuka ta fad'a bathroom da sauri.

Juyawa yayi ya fice jikinsa duk yayi sanyi, "Dole ne innemowa umma mafita akan laluran nan, gashi tashiga watan haihuwa amma ba alamun zata warke, oh Allah kabawa baiwanka lafiya kafin lokacin haihuwarta yayi Amin."

D'akinsa ya shiga ya watsa ruwa ya fito yanufi masallaci yagabatar da sallah.

Tana zaune a parlour ta zuba magumi idanunta sunyi jajur har fatan
samarsu sun kun bura don kuka.
   Ahaka yasameta ya sa hannu ya cire mata tagumin da tayi ya janyota ta sauko k'asa ya bud'e abincin da shigo dashi yasom bata abaki saida ya tabbatar da k'oshi sannan yasoma ci.

"Mamiena banason ganinki cikin damuwa, don Allah kibari ki komo cikin walwalanki kamar da."

Idanu ta zuba mishi kamar baza tayi magana ba sai kuma ta bud'e baki da kyar tace "Sai naga ummanmu tasami lafiya sannan zan dawo normal sabida ni kad'ai nasan yarda nakeji araina game da laluranta, watanni hud'in nan data kwashe cikin lalura gani nake kamar ta she kara hud'u ne, musanman ganin cikin jikinta danayi  yau yak'aragirma wallahi abin ya firgitani sosai."
   Sai da yaja numfashi ya fesar da iska sannna yace "To Allah yabata lafiya cikin gaggawa."

"Amin Yaya."

Da dare duk iyalan gidan suna parlour n dada ana hira cike da nushad'i.
   
Mamie tana zaune gefe hannunta rik'e da cup tana kurban damammiyar fura wacce taji nono tare da madara, zuciyarta tayi nisa cikin tunanin ummanta, batama jin abinda suke cewa sam, shan furar takeyi kawai batare da sanin inda natsuwarta yake ba.

Motsin mutum taji agefenta ta zabura sabida taji tsoro.
Suna had'a idanu ya kashe maka ido d'aya tare da d'aga mata qira cikin salon tsinewa ya shafi fuskanta cikin furta "Affuwan na tsorata ki ko?"

Wani uban tsaki taja ta miqe tabar mishi wurin ta koma gefen Dada ta zauna sai cika take tana batsewa dan fushi.

Dada ta dubeta ta girgiza kai "Ke dawa kuma takwarata?"

"Ni da jikanki d'an kwayan can ne, yazo kusa dani zai zaisamin warin tabar shed'an."

Idanu waje dada tace "Ke! Mamie kifita udanuna in kulle, yanzu yunus d'in ne d'an kwaya?"

"Eh shifa Dada, koba kisan har  da ruwa yake korawa ba?"

"Uwarki mahaukaciyan nan ke kora ruwa, shegiyar, gantalalla kawai."

"kaine gantalalle wallahi kuma kaine shege mara mafad'i sannan ciwon umma mai warkewa ne da yardan Allah kuma kaima bakafi qarfin fad'awa cikin laluranba."

  Afusace yazo ya d'aga hannu zai maketa yaji an riqeshi ta baya ya juyo a zucuye yayi arba da Baffansa da sauri ya sunkuyar da kansa k'asa.

"Wawa, sha- sha-sha, mara tunani, wuce kabani wuri solobuyo kawai, karasa wanda zakayi fada da ita sai mace macenma k'anwarka wacce zaka zamowa garkuwa wurin kareta amma ka buge da fad'a da ita har da k'ok'arin ware k'wanjika kakeyi akanta dan sokanci."
 
Baffan ya dubi mamie yace "Zo nan yarinyata ta matso ya dafa kanta yace "Kibar biye masa kuna fad'a kinji? Yayarki ne."

"Tam baffa kayi haquri nabari."

"Bakimin ko ba d'iyar Baffa, Allah dai yabawa mahaifiyarki lafiya."

Amin." ta amsa ta kuma d'ora da cewa "Kaima Allah ta baka mata ta gari mai imani da natsuwa mai son farin cikinka da na zuri'arka."

"Amin yarinya ta." Ya amsa yana murmushi da gani kalaman sun faranta masa.

Yunus yana gefe sai harara yake aunawa mamie barinma da yaji k'arshen maganarta.
  'Wato mahaifiyarsa matar jaraba ce kenan take nufi komi?' Ya tambayi kansa cikin zuciyarsa.

Abba ne da Abdul hakeem suka shigo.
  Gaban dada suka durk'usa suka gaidata sannan suka gaida Baffa.

  Yunus, fatima, imranat tare da mamie suka gaida su.

Daganan aka bud'e wani babin hira wanda duk akan laluran hajiya na'ima ce ake magana wato umman su mamie.

Tsawon lokaci suka d'auka sannan kowa ya watse yanemi makwancinsa yayin da mamie ta mak'ale d'akin dada tak'i komawa part d'insu sabida haka kawai taji gabanta na fad'uwa tasami kanta dajin tsoron kwana ita d'aya a shashin, alhalin da bata tabajin hakanba.

Wuraren k'arfe d'ayan dare ta farka bataga dada ba ta miqe ta duba bayi bata ciki ta fito parlor cikin sand'a tayi arba da mama, Dada tare da yunus suna magana k'asa-k'asa, abinda taji suna magana akai ne yasa ta sake labewa jikinta narawa azuciyarta tana nanata 'Lallai biri yayi kama da mutum wallahi *banyi zato ba* Dada.

Tana xubar hawaye ta koma ta kwanta ganin barcin yak'i zuwa mata sai fad'a bayi ta d'auro alwalla ta zauna tasoma karatun qur'ani mai girma da kai sabi da bata cikin tsarki balle tayi nafila, haka tayi ta karatun tsawon lokaci sannan ta d'ora da addua memanma ummanta lafiya tare da kariya daga sharrin maqiya, domin  tasan Allah yana saurin amsar addu'a wacce take cikin haila da gaggawa.

Ko da dad ta dawo d'akin baqaramin gigita tayiba saka makon ganin mamie idanunta biyu.

Jiki a sanyaye ta hau gadonta ta kwanta ta ritse idanu gabanta na dukan 9~9.
 
Harara mamie ta bita dashi ta furta afili "tsohuwar kawai.
  "Ehye!!! Magana kikeyi takwarata? Cikin hargagi ta amsa "ni ba takwararki bace, takwarar hajiyanmu ce ta gidan marayu mai hangen nesa da nagarta ba mara imani ba irinki.

BANYI ZATO BAWhere stories live. Discover now